Arewa Nexus

Call Contact the organization

Arewa Nexus Kasance da mu domin samun sahihan rahotanni na dumi-duminsu a kan lokaci. 📰 We know your need

AREWA NEXUS: Matattarar ingantattun labarai, bincike mai zurfi, da al'amuran yau da kullum daga Arewacin Nijeriya da sassan duniya baki daya cikin harshen Hausa zalla.

YANZU-YANZU: Wasu 'yan jam’iyyar APC daga ƙaramar hukumar Illela ta jihar Sakkwato sun yi hatsarin mota a kan hanyarsu t...
23/10/2026

YANZU-YANZU: Wasu 'yan jam’iyyar APC daga ƙaramar hukumar Illela ta jihar Sakkwato sun yi hatsarin mota a kan hanyarsu ta zuwa Kaduna domin halartar taron Tinubu.

Shugaba Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 10 domin shirin tunkara da kuma maida martani kan cutar Ebola a Najeriya,...
23/10/2026

Shugaba Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 10 domin shirin tunkara da kuma maida martani kan cutar Ebola a Najeriya, sannan ya nada Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ya jagoranci kwamitin musamman na shugaban kasa kan cutar Ebola da sauran sabbin cututtuka masu hadari.

Kashim ya iso Maiduguri domin bude asbitin koyarwa ta Kashim Ibrahim University mallakin jahar Borno
23/10/2026

Kashim ya iso Maiduguri domin bude asbitin koyarwa ta Kashim Ibrahim University mallakin jahar Borno

Sarki Sunusi Ya Caccaki Atiku Abubakar Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Yace Cire Tallafin Ya Zama Wajibi Don Dawo da Tatt...
23/10/2026

Sarki Sunusi Ya Caccaki Atiku Abubakar Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Yace Cire Tallafin Ya Zama Wajibi Don Dawo da Tattalin Arzikin Nijeriya

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya caccaki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kan kalaman da ya yi game da cire tallafin man fetur a Najeriya.

A cewar rahoton jaridar The Nation na ranar Litinin, 28 ga Afrilu, 2025, Sanusi ya bayyana cewa, ko dai Atiku ba ya faÉ—in gaskiya ne, ko kuma bai fahimci irin aikin da yake son zuwa ya yi ba.

Sanusi ya ce kalaman Atiku kan yadda aka cire tallafin man fetur sun nuna rashin fahimtar yadda aka gudanar da matakin da kuma dalilan da s**a sa aka É—auke shi.

Ya jaddada cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da aka aiwatar sun zama wajibi domin taimakawa wajen tabbatar da daidaiton tattalin arzikin Najeriya.

Tsohon gwamnan CBN ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ya kasance wani mataki mai muhimmanci wajen hana tattalin arzikin Najeriya faÉ—awa cikin mummunan hali.

Ya kuma yi kira ga shugabannin ƙasar da su mayar da hankali wajen samar da hanyoyin magance matsalolin tattalin arziki masu ɗorewa, maimakon dogaro da tallafi kawai.

Sanusi ya ƙara da cewa ya kamata a gudanar da gyare-gyaren tattalin arziki da za su taimaka wajen gina Najeriya mai ƙarfi da kwanciyar hankali.

Wani lauya mai zaman kansa mai suna Barr. Hamza Nuhu Dantani sun baiwa hamata iska a shafin Facebook tare da mai taimaka...
12/10/2026

Wani lauya mai zaman kansa mai suna Barr. Hamza Nuhu Dantani sun baiwa hamata iska a shafin Facebook tare da mai taimakawa gomnan Borno kan harkokin Media Abdulrahman Ahmad Bundi.

Me zakuce?

Za’a fuskanci matsalar rashin wuta a fadin jahar Borno sakamakon Power Gas Plan na Maiduguri ya lalace inji hukumar yada...
09/10/2026

Za’a fuskanci matsalar rashin wuta a fadin jahar Borno sakamakon Power Gas Plan na Maiduguri ya lalace inji hukumar yada labaru da tsaron cikin gida ta jahar Borno.

Meke faruwa tsakanin kungiyoyin tallata APC na City Boys Movement da Village Boys Movement a Borno?
08/10/2026

Meke faruwa tsakanin kungiyoyin tallata APC na City Boys Movement da Village Boys Movement a Borno?

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya shiga tsakani tare da sasanta Mataimakin Shugaban Majalisa...
07/10/2026

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya shiga tsakani tare da sasanta Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Hon. Abubakar Kabir Bichi, bayan saɓanin siyasa da ya kunno kai tsakaninsu.

An gudanar da zaman sulhun ne a Abuja da safiyar Laraba, inda shugabannin s**a tattauna tare da amincewa da ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu domin ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar APC a Kano.

Gwamna Abba Yusuf ya buƙaci magoya bayan ɓangarorin biyu su daina cin zarafi, kalaman tunzura jama’a da duk wani abu da zai iya kawo rarrabuwar kai, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

Sanata Barau da Hon. Bichi sun amince da sulhun tare da jaddada goyon baya da biyayyarsu ga jam’iyyar APC, kana s**a gode wa Gwamna Abba Yusuf bisa shiga tsakani da kawo ƙarshen saɓanin.

Jami’an tsaro sun ceto yan bautan kasa da aka sace a jahar Imo
07/10/2026

Jami’an tsaro sun ceto yan bautan kasa da aka sace a jahar Imo

Da ÆŠumi-ÆŠumi Gwamnatin Nijeriya ta saki kuÉ—aÉ—en Albashi na Ma'aikatan Jami'o'i Gwamnatin Nijeriya ta saki kudaden Albash...
07/10/2026

Da ÆŠumi-ÆŠumi

Gwamnatin Nijeriya ta saki kuÉ—aÉ—en Albashi na Ma'aikatan Jami'o'i

Gwamnatin Nijeriya ta saki kudaden Albashi da aka riƙe ta mambobin ƙungiyar Ma'aikatan Jami'o'i ta SSANU wanda s**a yi gargaɗin kawo tsaiko ga ayyukan karatu na jami'o'in ƙasar

Address

Maiduguri
Maiduguri

Telephone

+2348061552823

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Nexus posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Arewa Nexus:

Shortcuts

Share