13/05/2022
GANAWAR JAGORA (H) DA DALIBAN HAUZA
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
A yayin ganawar Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) da wasu daga daliban Hauzar Ilimi wadanda s**a zo hutu tare da Tablig daga kasashen Iran, Iraq da Lebanon, a ranar Talata 11 ga watan Shawwal, 1443 (11/5/2022) a gidansa da ke Abuja, ya yi kira kan matakan da ya dace a bi wajen isar da sako da yada ilimi ga al’ummar wannan nahiya.
Jagoran ya kirayi daliban da cewa: “In mutum ya je muhallin da zai yi Da’awa (Tabligi) zai yi la’akari ne da bukatun mutanen wajen ne ya ga inda shi zai taimaka musu ya d**o su zuwa wani mataki da za su iya kaiwa fiye da wanda suke a kai. Ba zai zo da duk abin da ya karanto ne ya rika zuba musu ba, (in ya yi hakan) za su iya kasa fahimta su yi masa garau (suna kallonsa), kila ma su ce kansa da motsi, saboda ba za su gane abin da yake cewa ba, b***e su fahimci me yake koyar da su.”
Ya ba da misali da yadda wani Malaminsa na Usul da Mandiq a Jamhuriyar Musulunci ta Iran yake karfafa shi a kan muhimmancin koyar da karatun da yake yi a lokacin. Amma sai ya zama ba a samu wanda suke da ahaliyar da zai karantar da su wannan ilimin a nan ba (a lokacin). Har da ya fadawa Malamin haka, sai yake cewa: “Gaskiya ne, in ka je ka ga mutane ya zama su matsalarsu yanzu Alwala ne suke so su iya, kaga ba batun ka musu Usul ne ba, su abin da ya dame su kawai z aka koya musu.”
Ya bayyana yadda ya kamata a rika magana da mutane daidai da hankalinsu. Inda ya ba da misali da yadda bayan zuwansa Iran a 1980 ya ga taron mutane masu goyon bayan juyin Musulunci, da ya dawo ya yi kokarin sanar da mutane komai da komai, amma s**a kasa fahimta. Har wani ya shaida masa cewa wannan abin ba zai yiwu ka fadawa mutane su gane ba, sai dai in ka aikata su gani a tare da kai (ta haka za su iya fahimta su yi).
Yace “Na’am ba zai yiwu kowa da kowa ya gane ba, domin an ga Annabawa ai, amma sai aka ce musu basu da hankali. Me aka cewa shugaban Manzonni (S)? Aka ce masa boka, aka ce masa mawaki, har ‘Majnuni’ ma an ce masa. Ba abin da ba su fada ba. Don haka ba yana nufin kowa zai (gane har ya) karba bane.”
Shaikh Zakzaky yace: “Su mutane su fahimci tsari ya koma na addini shine (ya gagaresu), kowa ya rikice, ba wanda yake ganewa. Saboda ba yadda za a yi ka nunawa mutum nizami. Wasu sai su ce wai ana nema a hambare musu gwamnati. Nake cewa ai ba Gwamnati ake nufi ba. Gwamnatoci nawa aka yi? Ni daga wayau na zuwa yanzu na ga Gwamnati ya kai 13.”
Nan ya lissafa gwamnatocin da ya shaida tun daga na mulkin Bature, har zuwa na Soja da ta fararen hula har 13, Yace: “Ka ga in canjin gwamnati ne, to na ga wajen 13 ne. To ba canjin Gwamnati muke nufi ba, canjin nizami (muke nufi).”
Ya cigaba da cewa: “Shi kuma juyi yana da wahalar ganewa. Su mutane da an fara magana sai su ce wai za a kwace musu gwamnatinsu. Nace wa ke maganar gwamnati? Ana maganar mutane su koma nizamin addini, ku kuna ce za a kwace gwamnati. Gwamnatocinku duk da kuke yi gaba daya tun daga na mulkin mallaka har izuwa yanzu duk a kan nizami daya ne -Tun da turawan mulkin mallaka s**a zo s**a kafa nizaminsu har izuwa yau (iri daya ne).”
A nan ne ya kara haske kana bin da yake kiran al’umma a kansa ta hanyar ba da misali da yadda Shehu Usman ya samu al’ummar kasar nan bisa nizamin Gargajiya ya canza su zuwa addini, daga baya Bature ya zo ya canza su zuwa ga nizamin da ke iko yanzu, inda ya jaddada cewa mu kuma a yanzu muna kira ga komawa wannan addini din ne.
Yace: “Shehu Usman ya zo ya samu al’ummar nan ne tana nizamin Gwargajiya, akwai Sarakuna, amma al’ada suke bi. Ko da yake da yawansu Musulmi ne, amma dai nizamin da ke iko al’ada ne. To shi (Shehu) sai ya dora al’umma a kan nizamin addini.”
Ya cigaba da cewa: “Shi kuma da Bature ya zo shi kuma nizamin addinin ya kawar. Har na sha yin magana nace shi Bature fa bai boye mana ba, sosai maganar da Lugard ya yi a Sokoto, yace da can Fulani sun ci kasar nan da yaki, suna da ‘yancin su mallaki kasar nan, to mu kuma yanzu Ingilishi mun ci ku da yaki mu ke da ikon mu mulke ku, saboda haka muma akwai dokokinmu za mu so ku bi kamar yadda mu ma za mu dan yi bitan naku, amma ku bi namu, yanzu kuna bisa nizamin Ingila ne.”
Ya kara da cewa: “Shi kuma (Bature) ba Babarodo ya yi ba ma, sai da ya tara Sarakuna a Lokoja, ya dauko Alkur’ani ya nuna musu yace kun ga wannan da shi ke iko da ku, amma yanzu ba shi bane, bari ku ga makomarsa. Aka samu wani Bature ya yi wa Alkur’ani fitsari suna kallo. Yace kun ga makomarsa kenan. Aka dauko tutar Danfodiye mai rubutun ‘La’ilaha illahu Muhammadur Rasulullah’ aka ce da kuna karkashin wannan tutar, to bari ku gani, aka kona. Aka dauko tutar nan mai ‘Cross’ aka daga aka ce to yanzu kuna karkashin wannan. To me ya rage?”
Shaikh Zakzaky yace: “To yanzu mu abin da muke cewa shine za mu komawa addini ne. Amma sai mutane su rika cewa o’o’o’o! In dan boko ne yace maka ‘impossible’! In kuma bai yi boko ba sai yace ai ba zai yiwu ba, an yi nisa, ba zai yiwu ba. Me zai hana shi yiwuwa? Sai su ce ai kasar ba Musulmi ne duk ba. Sai mu ce ai Allah bai lizimta mana yin kasa ba, abin da ya lizimta mana yi shine yin addini.”
Ya kara da tambaya: “Ko Allah Ta’ala ya lizimta mana yin kasa ne? Ko akwai wata Aya da tace ya ku mutane in kuka samu kanku a wata kasa kuka ga akwai wasu mutane da ba Musulmi ba a cikinku ku ku ajiye addinin Musuluncinku?” Yace: “Da can ma da ake Musuluncin an ce dole kowa Musulmi ne? Ko da Bature ya zo kasar nan ya samu kowa Musulmi ne? Ya samu mutane da yawa suna addinai daban-daban, amma Musulunci ke iko ba Al’ada ba. Abin da ya zo ya samu kenan, shi kuma ya zo ya kawar.”
Jagora (H) yace: “Har yanzu sun kasa gane cewa juyin juya hali da ake yi ba juyin mulki bane, sauyin tunanin mutane ne. Su mutane ne suke canzawa, in sun canza dole ita gwamnatin da za a yi za ta zama irinsu ce. Amma in aka canza Gwamnati kuma nizamin (da ke iko) yana nan, to duk abu daya ne ai. Yanzu duk canje-canjen da ake na gwamnatocin nan kun ga bambanci ne?”
Yace: “Duk mutane yanzu sun zaku cewa badi a zo a yi zabe su samu sauyi… Tunanin da s**a rika yi kenan a da can ko? Sai kuma abin da s**a zaba ya zama musu abin da ya zama musu. To kuma mai yiwuwa in sun yi zaben kuma a sake ganin abu ya sake zama yadda zai zama. Amma abin da ake ce musu shine, shi nizamin yana nan (don haka ba wani canji don an canza mai tafi da shi).”
Ya kawo misali da motar da injinta ya buga, a maimakon a yi kokarin duba injin a canza, sai ya zama kullum ana kokarin canja matukinta ne da tunanin kowa bai iya tukin bane. “Na san duk wadannan misalan tun 1970s nake badawa, nake cewa kun ga abin da mutane suke ce mana mu gyara abin da ba zai gyaru bane, mun ki gane shi nizamin za mu canza ba kamar yadda kullum kuke tunanin wai sai a zabo shugabane wanda zai ja abin ba.” Yace.
Ya jaddada cewa: “Shi nizamin za a canza, domin in aka ce shugaba ne, sai aka canza shi, in shi shugaban mutumin kirki ne to ba sai kuma nizamin ya zama na gari ba. Ba sai komai ya zama daidai ba, saboda shima zai yi amfani ne da ma’aikatansa wadanda suke cikin nizamin, su kuma ga abin da suke a kai, shine za a cigaba a kai din, yana ji yana gani ba zai iya sauya abin ba, komai gyaruwansa, komai walittakansa wadannan mutane za su lalata masa komai. Za ma su yi abin da mutane shi za su zarga.”
Jagora yace: “Yanzu abin da yake kanmu shine a yi ta ilmantar da mutane, don wadansu kalaman nake ganin kila mutum in ya yi ilimi ne zai iya ganewa.” Ya kara da cewa: “To kuma ka san ilmantar da mutane daga mustawan da suke ka daga su shima ba karamin aiki bane, saboda haka in an je karatu misali a kauye, ya kamata a yi ajin manya, wadanda bukatunsu za a yi la’akari da shi. Sai an fara musu da tsarki da wanka, don ta yiwu wasu basu sani ba, haka nan suke rayuwa.”
Ya kawo misalsalan yadda jahilcin wasu ke bayyana bayan sun girma alhali ana dauka su sun san abubuwa in ba don hakan ya bayyana daga gare su ba. Yace: “Kar ku sha mamaki da yawan mutane sunansu Musulmi ne, amma in aka koma ana maganar (hatta) wankan janaba da yawa basu iya ba.”
Ya kawo misali da yadda wani limamin kauye ya ba da fatawar cewa in mutum ya sadu da mace in dai matarsa ce to ba sai ya yi wanka ba. Yace: “Liman ne a kauye yake ba da wannan fatawar. To ka ga irin wadannan jidali maka-Malam ka je irin wannan kauyen kana musu maganar Wulaya ma ai kana bata lokaci ne, ba shine ‘asasi’ ba. hawa-hawa za ka bi su, mataki-mataki.”
A karshe ya jaddada muhimmancin samar da ajin manya maza da mata, sannan ya ba da shawarar shirya Daurori ga musamman yara baya ga karantar da su na dindindin da ake yi, wanda hakan zai taimake su sosai wajen tasowa cikin turbar nagarta.
12/05/2022