04/06/2026
BYFA Ta yi Na Musamman da Shugaban Fadar Gwamnati domin Gabatar da Wani Muhimmin Tsarin da zai Taimaka wa Nasarar Gwamna RaÉ—É—a a 2027
Darakta Janar na Building Your Future Ambassadors (BYFA), wadda a baya ake kira Dikko Vision Movement (DVM), Dr. Isah Rabe Kambarawa ya gudanar da wata muhimmiyar ganawa ta musamman da Shugaban Ma'aikata na Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdulƙadir Mamman Nasir, a Fadar Gwamnatin Jihar Katsina.
Ganawar ta mayar da hankali ne kan hanyoyin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin BYFA da gwamnatin jihar wajen tallata manufofi da nasarorin gwamnatin Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda, CON, tare da tabbatar da dorewar manufofin ci gaba da ke ƙarƙashin Tsarin "Gina Makomarka".
A yayin tattaunawar, Darakta Janar na BYFA ya gabatar da wani muhimmin tsari da ƙungiyar ta tanada wanda aka tsara domin ƙarfafa wayar da kan al'umma game da ayyukan gwamnati da kuma samar da ƙarin goyon bayan jama'a ga gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Ya bayyana cewa BYFA ta ƙudiri aniyar ci gaba da kasancewa a gaba wajen wayar da kan al'umma kan manufofi, shirye-shirye da nasarorin gwamnatin jihar, tare da ƙarfafa matasa, mata da sauran al'ummomi su ci gaba da mara wa gwamnati baya domin tabbatar da ɗorewar ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa a faɗin jihar.
Da yake jawabi a yayin ganawar, Shugaban Ma'aikata na Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdulƙadir Mamman Nasir, ya yaba da hangen nesa da jajircewar shugabannin BYFA wajen samar da sabbin hanyoyi na tallafawa manufofin gwamnati da kuma ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da jama'a.
Ya bayyana shirin da ƙungiyar ta gabatar a matsayin wani muhimmin mataki da zai taimaka wajen ƙara wayar da kan al'umma game da nasarorin gwamnatin jihar, yana mai cewa ya yi daidai da manufofi da shirye-shiryen gwamnati na bunƙasa walwala da ci gaban al'ummar Katsina.
Shugaban Ma'aikatan ya kuma tabbatar da shirye-shiryen Fadar Gwamnati na yin aiki kafaÉ—a-da-kafaÉ—a da BYFA domin tabbatar da nasarar duk wani tsari da zai amfani al'umma tare da taimakawa wajen ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatin Malam Dikko Umaru RaÉ—É—a, PhD, CON.
Darakta Janar na BYFA ya samu rakiyar Daraktan Mulki na ƙungiyar, Hon. Sadiq Abdullahi Gwarjo, yayin wannan muhimmiyar ziyara.
Har ila yau, zaman ya samu halartar wasu manyan jami'an gwamnati da s**a haɗa da Sakatarorin Dindindin na Fadar Gwamnati da kuma Ma'aikatar Lamuran Mata, lamarin da ya ƙara nuna muhimmancin tattaunawar da aka gudanar.
Ganawar ta gudana cikin yanayi na fahimtar juna, haɗin kai da kyakkyawan fata kan makomar jihar, inda ɓangarorin biyu s**a jaddada aniyarsu ta ci gaba da aiki tare domin tallafawa manufofin ci gaba da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.
Sanarwa:
Daraktan YaÉ—a Labarai da Sadarwa
Building Your Future Ambassadors (BYFA)
Alhamis, 4 ga Yuni, 2026
18 ga Zul-Hijjah, 1447AH
Hannatu Musa Musawa
Alh. Ibrahim Kabir Masari
Aminu Bello Masari
Katsina State Government
Katsina State Television KTTV
Katsina State Radio Service -KTRS
Renewed Hope Katsina State
City Boy Movement Katsina State
GMTD