Coalition Of Youths Organizations For Tinubu/Dikko

Coalition Of Youths Organizations For Tinubu/Dikko Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Coalition Of Youths Organizations For Tinubu/Dikko, Political organisation, Katsina.

The Coalition of Youth Organizations for Tinubu 2027 (CYOT 2027) is an umbrella coalition bringing together progressive youth organizations, youth-led organizations, volunteer groups, student bodies, community-based youth associations

Gamayyar ƙungiyoyin matasa masu goyon bayan shugaba Tinubu tare da haɗin gwiwa da gidauniyar Katsina Healthcare sun guda...
28/07/2026

Gamayyar ƙungiyoyin matasa masu goyon bayan shugaba Tinubu tare da haɗin gwiwa da gidauniyar Katsina Healthcare sun gudanar da gangami bada magani da duba lafiya kyauta

A wani yunƙurin haɗin gwiwa da s**ayi domin taimakawa al'umma marassa ƙarfi sun duba marassa lafiya tare da basu magani, da kuma yin awo ga marassa lafiya

An gudanar da gangamin a asibiti Maryam health Care Clinic dake dake Modoji Katsina a ranar 27 ga watan Yuli 2026

A yayin da yake jawabi yayin bada tallafin lafiyar Sakataren tsatsare na ƙungiyar Muhammad Dikko Musa yake cewa wannan haɗin gwiwa ne, tsakanin ƙungyarmu da da wanan asibiti Maryam Clinic domin taimawa marassalafiya wanda basuda halin zuwa asibiti

Ya ƙara da cewa ita kungiyar gamayyar ƙungiyoyin matasa masu goyon bayan Tinubu Coalition Of Youths Organizations For Tinubu/Dikko ba kwai wayar ta kan al'umma kan Shugaba Tunubu ta tsaya kaɗai ba, harda taimako ga al'umma ta fannoni daban-daban

Shima anasa Jawabin shugaban Asibitin ta Maryam Nurse home Katsina Malam Nuhu Idris yace a wanan hadin gwiwa muyi yarjejeniya da ƙungiyar inda muka yafe kaso 15% su kuma s**a bada koso 75% tunda ganin likita, bada magani da kuma aune-aune

Haka zalika muna son yin amfani da wannan dama domin muyi kira ga sauran kungiyoyi da ɗaiɗaikun al'umma da Gwamnati da suyi koyi da wanan ƙungiya sanan kuma a matakin asibitin mu a shirye muke domin tallafawa al'umma musamman ta bangaren lafiya sanan kuma muna rage kaso mai tsoka.

Daga Karshe dai Shugaban kungiyan a yayin jawabin sa yace ita wannan kungiyan a shirye take domin hadin gwiwa da cigaban alumman kasa baki daya

15/07/2026

Minene Sabunta Muradi ko Fata?

Saurara kuji domin samun sani akan Sabunta Muradi Renewed Hope Katsina State

Gamayyar ƙungiyoyin matasa masu goyon bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu sun yi Allah wadai tare da yin tir ga al'umm...
13/07/2026

Gamayyar ƙungiyoyin matasa masu goyon bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu sun yi Allah wadai tare da yin tir ga al'ummar da s**a yi wa Dr. Abu Ammar kalaman ɓatanci.

A wata sanarwa da Sakataren Tsare-tsare na Gamayyar Ƙungiyoyin Matasa Masu Goyon Bayan Tinubu, Aminu Tanimu Turaki, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2026, ƙungiyar ta yi tir tare da yin Allah wadai da kalaman ɓatanci da wasu mutane s**a yi wa Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dr. Abu Ammar, sakamakon wani suna da yakira Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu dashi.

Sanarwar ta bayyana cewa tun da farko akwai wasu mutane da ke jiran samun wata dama domin su riƙa yin ɓatanci ko kuma su ɓata wa Shugaban Hukumar Hisbah suna, saboda ayyukan gyaran tarbiyya da hukumar ke gudanarwa. A cewar sanarwar, sun yi amfani da wannan batu ne a matsayin hujjar kai masa hari.

Sanarwar ta ƙara da cewa a Najeriya kowane ɗan ƙasa yana da 'yancin faɗin ra'ayinsa kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ya tanada. Saboda haka, kamar yadda kowane ɗan Najeriya ke da wannan hakki, haka ma Dr. Abu Ammar yana da cikakken 'yancin bayyana ra'ayinsa.

Ta kuma ce, kasancewar Jam'iyyar APC ce ta naɗa Dr. Abu Ammar a matsayin Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, babu laifi idan ya yi magana kan harkokin jam'iyyar ko ya bayyana ra'ayinsa mai kyau game da wani shugabanta.

A ƙarshe, ƙungiyar ta ja hankalin tare da gargaɗin masu ci gaba da yin kalaman ɓatanci ga Dr. Abu Ammar da su ji tsoron Allah su daina. Ta kuma bayyana cewa kasancewar su masu laifi agare shi, ya dace su nemi afuwa daga gare shi.

Signed
Amb. Muhammad Musa Dikko
Secretary, CYOT.

11/07/2026

Renewed Hope Agenda ba kalmar yaƙin neman zaɓe kaɗai ba ce. Cikakkiyar manufa ce ta gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wadda aka ƙirƙira domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, samar da damarmaki ga al’umma, da gina Najeriya mai ɗorewa.

Lokaci ya yi da za mu fahimci manufofin da ake aiwatarwa domin mu kasance masu cikakken sani, mu kuma ba da gudunmawarmu wajen gina Najeriya mai ci gaba.

Wannan shiri haɗin gwiwa ne tsakanin Coalition of Youths Organization da Renewed Hope Ambassador, Katsina State, domin wayar da kan al’umma game da Renewed Hope Agenda da muhimmancinta ga ci gaban Najeriya.

Ƙungiyar Coalition of Youth Organizations for Tinubu (COYOT) ta kai ziyarar girmamawa ga fitaccen malami, Sheikh Dr. Ami...
10/07/2026

Ƙungiyar Coalition of Youth Organizations for Tinubu (COYOT) ta kai ziyarar girmamawa ga fitaccen malami, Sheikh Dr. Amin Abu Ammar, inda ta miƙa masa takardar naɗi a matsayin Patron na ƙungiyar.

A yayin ziyarar, shugabannin COYOT sun gabatar da manufofi da hangen nesan ƙungiyar, waɗanda s**a mayar da hankali kan haɗa kan matasa da tallafa wa manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Da yake karɓar naɗin, Sheikh Dr. Amin Abu Ammar ya bayyana cikakken goyon bayansa ga ƙungiyar, tare da alƙawarin ba da shawarwari, addu’o’i, da jagoranci domin tabbatar da nasarar ayyukanta.

Address

Katsina

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Coalition Of Youths Organizations For Tinubu/Dikko posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share