25/08/2021
Dan zahara & yar fulani
🕌🕋🕌
🤲🏻🤲🏻🤲🏻
👉🏻Karamomin Sayyida Fa]ima:Idan mutum ya
bibiyi tarihin Sayyida Fa]ima zai ga cewa tana da
karamomi masu yawa wasu karamomin ma tun gabanin
a haife tane s**a kasance alal misali ta kasance tun tana
cikin mahaifiyarta take magana da mahaifiyarta a
ciki,akwai lokacin da Manzon Allah ya shigo cikin gida
sai ya ji Sayyida Khadija na magana alhali ba kowa a
cikin gidan shine Manzon Allah ke tambayar ta ke da
wa k**e magana? Sai ta ce da yaron da yake ciki na
ne,sai Manzon Allah ya ce mata mace ce kuma Allah
Ta’ala zai sanya zuriyyata daga gareta kuma a cikin
zuriyyar tane za a samu Imaman wannan
al’umma.Haka nan ya zo akan cewa lokacin da aka
haife ta sai ta kasamce a }asa tana mai sujuda,haka nan
lokacin da aka haife ta wani irin haske ya bayyana
wanda ya haskaka garin makka baki ]aya dama sauran
sassa na duniya.Haka nan kuma ya zo a kan cewa bayan
haihuwarta an ji tana cewa, “Na shaida babu abun
bautawa sai Allah kuma lalle baba na Manzon Allah ne
kuma shugaban Annabawa miji na kuma shine
shugaban wasiyyai.A ta}aice dai ayoyi da kuma
karamomi masu yawa sun bayyana a lokacin haihuwar
Sayyida Fa]ima.
Kuciga Al abbass & zainab yar fulani