10/05/2017
MURNAR MUTUWA MURNAR BANZA.
Shekaru uku baya, ma fi akasarinmu. hankalinmu a tashe yake, idanuwanmu ba su rufo da nufin yin barci, kullum mun yi fakare muna jiran ko ta kwana, da yawa daga cikinmu sun gamu da wani ibtila'i, ko dai na Boko Haram, ko na masu satar mutane, ko na barayin shanu, ko kuma rugujewar tattalin arziki. Wadannan matsaloli ne da in dai ba su shafe ka kai tsaye ba, to sun shafi wani wanda ka sani, haka muka yi ta zama da tashin hankali har Allah Mabuwayin Sarki Ya kawo mana irin abunnan da Bahaushe kance 'jirgin Annabi Nuhu'.
Zuwan shugabancin Muhammadu Buhari ya zame mana wani sanadi na fitonmu daga doguwar ninkayar da ta yi nufin karar da mu, wadda aka cusa mu da karfin tsiya, tsaro ya fara samuwa, nutsuwa da kwanciyar hankali s**a fara tabbatuwa, tattalin arziki ya fara murmurewa daga farmakin da kurayen kasa s**a kai masa, muka fara koyon yin da'a da yin daidai ko ba a tirsasa mu ba, akidar mutanen dauri ta fara dawowa jikinmu. Al'amura s**a fara saituwa a kasa, a kullum ana kara samun cin galabar danniya da wawurar baitilmani, almubazarancin da barayin dukiyar kasa suke yi ya fara bankwana. A yanzu ne za ka shiga masallaci ka yi sallah ba wata fargaba, mabiya addinin kirista su shiga coci ba wata damuwa, kai hatta wanda ba shi da addini ya amince kasar ga ta k**a hanyar gyara.
Abin mamaki, a sanina, idan amarya ba ta hau doki ba, ai kuwa ba za a dora mata kaya ba. Duk da dumbin alfanu da ake samu, wasu da ba su kishin kansu sun dauki kahon zuka sun caka wa BUHARI, sun mayar da shi ba ya da wani kokari, kuskure kadan za a samu su ci gaba da yadawa su kuzuzuta, amma kuma sai su yi biris da nasarar da BUHARI ya samu komin girmanta. ba za su yaba ba, k**ar malam ya ci shirwa za ka ji su, don munafinci.
Abun yana bani takaici idan na ga talakan da ke a karkara ya zauna yana zagin shugaba Buhari, wani abu wai bakin kaza, ya zauna ya yi ta kakaba masa MUTUWA, sai ka ce shi mai fadin ba zai mutu ba, mun dade da amincewa idan wa'adin mutum ya yi ba a jira, idan kuma bai yi ba, sai dai a yi kushe da hassada, amma BUHARI yana nan daram, a tunanina zuwa yanzu ya k**ata ma su irin wannan dabi'ar su gane abun a hannun Allah yake.
Za ka sha mamaki, idan ka ga ma fi yawan masu irin wannan mummunar fata ba su da wata riba ko da mutuwa shugaba ya yi, watakila sai ta zakin munafinci da jam'iyanci. Inda za ku gane karya suke munafukai ne, ba ranar da za su yi yabo, ko su ba da shawara, sai dai s**a da bambadanci. Wani abu kuma, ma fi yawan ma su surutun su ma ba mutanen kirki ba ne ko a gidajensu, abin nan ne na kyamar Karen da ke a gindin dinya. Ba sa kyautata wa kowa bare inganta rayuwar wani, amma a haka suke cin zarafin Buhari.
Wani abu da na lura da shi mafi yawan ma su yin mummunar fata ga Buhari, ba su ma san dalilin da ya sa suke zagin sa ba, kawai sun biye wa jam'iyanci da son zuciya.
A lokuta da dama, saniya ba ta sanin amfanin jelarta, sai bayan babu ita. Irin kokarin da dattijon nan yake yi, na gina sahihiyar kasa mai 'yanci da yalwa, ba lallai ba ne mu gane ta a yau, kila sai bayan ba shi, mu yi da na sani a lokacin da bai da amfani.
Fatanmu a kullum Allah Ya zaba mana abin da yake ma fi alheri ne a rayuwarmu, duk mai muguwar fata ga Shugaba Buhari da mu kanmu muna rokon ALLAH Ya mayarwa mashekiya da kaikayinta.
Ba za mu gajiya ba muna addu'a Allah duk wanda yake munafuntar Musulmi da Arewa Ya Allah Ka kakkarya shi.
ALLAH YA RABA MU DA RANAR YABO
Ahmad A Bawa
Faskari.
Katsina State Coordinator
BUHARI YOUTH CONGRESS FOR CHANGE (B.Y.C.C)