11/06/2026
Gwamna Dikko Radda ya Kaddamar da Gidaje 152 na Yan Gudun Hijira a Jibia
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, ya kaddamar da gidaje 152 da wasu muhimman ayyukan inganta rayuwar alumma a Karamar Hukumar Jibiya, a wani kokarin gwamnatinsa na sake farfado da yankunan da matsalar tsaro ta shafa da kuma samar da hanyoyin samun abinci da kudin shiga, tare da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
An aiwatar da wadannan ayyuka ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina, Sashen Cigaba na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP), Gwamnatin Tarayyar Jamus ta hannun GIZ, Gwamnatin Kasar Norway da sauran abokan cigaba daga fadin duniya. Ayyukan sun hada da Cibiyar Zaman Lafiya (Climate Peace Hub) da Koyar da Sana’o’i, samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana ga al’ummar Daddara, gina asibitin dabbobi, gine-ginen a cikin kasuwa, tallafin noma, tallafin kasuwanci, horas da ma’aikata, samar da ruwan sha da fitilun tituna duk a cikin karamar hukumar Jibia.
A jawabinsa na maraba, Shugaban Karamar Hukumar Jibiya, Alhaji Surajo Ado Jibiya, ya yaba wa Gwamna Radda da abokan cigaban bisa kawo wadannan ayyuka da zai inganta rayuwar al’umma tare da bunkasa tattalin arzikin yankin.
A nasa jawabin bude taro, Kwamishinan Harkokin Karkara da Raya Al’umma, Farfesa Abdulhamid Ahmed Mani, ya bayyana ayyukan a matsayin wani babban ci gaba a kokarin samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma a jihar. Ya ce shirin ya yi duba ne ga muhimman kalubalen da s**a shafi rashin matsuguni, rashin aikin yi, hanyoyin samun abin dogaro da kuma gina al’umma.
Da take jawabi, Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Sashen Cigaba (UNDP) a Najeriya, Misis Elsie G. Attafuah, ta yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina bisa jajircewarta wajen samar da zaman lafiya da ci gaba mai anfani ga kowa. Ta jaddada cewa dorewar zaman lafiya na bukatar saka hannun jari a rayuwar jama’a, cibiyoyi don habaka tattalin arziki.
A sakonnin fatan alheri da s**a gabatar, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa, Jakadiyar Tarayyar Jamus a Najeriya, Mai Girma Annette Günther, da Jakadan Masarautar Norway a Najeriya, Mai Girma Svein Baera, sun yaba da tsarin hadin gwiwar da ake amfani da shi wajen magance matsalolin tsaro da karfafa juriyar al’umma. Sun kuma sake tabbatar da goyon bayansu ga shirye-shiryen da ke inganta zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba mai dorewa a Katsina da yankin Arewa Maso Yamman Nigeria.
A babban jawabinsa, Gwamna Radda ya bayyana gidajen da aka kaddamar a matsayin wata alama ta kokarin dawo da mutunci da martaba ga iyalan da matsalar tsaro ta shafa. Ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta samar da filin ginin, katanga, hanyoyin shiga, magudanan ruwa, wajen ibada, makaranta, kayan daki, gudumuwar Naira dubu dari biyu (N200,000) ga kowane magidanci don jan jari da sauran muhimman abubuwan more rayuwa domin cika wannan aiki.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta bayar da tallafin Naira miliyan 500 ga mutane 500 daga Karamar Hukumar Jibiya ta hannun Hukumar Kula da Ci gaban Sana’o’i da Kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA), domin taimaka musu wajen farfado da kasuwancinsu da hanyoyin samun kudin shiga.
Yayin da ya sake jaddada cewa tsaro shi ne ginshikin manufar gwamnatinsa ta “Gina Makomarku” (Building Your Future Agenda) , Gwamna Radda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta zuba sama da Naira biliyan 7 wajen samar da kayan aiki da tallafawa ayyukan tsaro. Ya ce ingantuwar tsaro ta bai wa manoma damar komawa gonakinsu, ta sa kasuwanci ya farfado, tare da dawo da kwarin gwiwa ga al’umma.
Har ila yau, ya yi kira ga hukumomi, abokan cigaba, sarakunan gargajiya da al’umma da su kara hada kai wajen magance tushen matsalolin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar.
A jawabinsa na godiya, Hakimin Daddara, Alhaji Usman Usman Nagogo, ya gode wa Gwamna Radda, abokan cigaba da dukkan masu ruwa da tsaki bisa wannan gagarumin aiki, tare da tabbatar da cewa al’ummar yankin za su kula da wadannan kayayyakin more rayuwa domin amfanin al’umma da al’ummomin da za su zo nan gaba.
An kammala taron ne da kaddamarwa tare da zagayen duba ayyukan da Gwamna Radda, jakadun kasashen waje, abokan cigaba, sarakunan gargajiya da sauran manyan baki s**a gudanar.
Taron ya samu halartar manyan baki ciki hadda mataimakin gwamnan jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, Rt. Hon Nasir Yahya Daura, jakadu daga majalisar dinkin duniya, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.
MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government
June 11, 2026.