Lawan Hussaini Media Team

Lawan Hussaini Media Team Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Lawan Hussaini Media Team, Political organisation, Dala Kano State Nigeria, Kano.

MEGA EMPOWERMENT A cigaba da rabon babura da Hon. Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa yake yi, yau ma ya bai wa mutane 14...
18/05/2026

MEGA EMPOWERMENT
A cigaba da rabon babura da Hon. Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa yake yi, yau ma ya bai wa mutane 14 babura, muna taya su murna kwarai da gaske Allah ya sanya Alheri ya rika.


Lawan Hussaini Media Team
Monday 18/05/2026

A jiya lahadi 17/05/2026 Hon. Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa, ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar al'ummar...
18/05/2026

A jiya lahadi 17/05/2026 Hon. Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa, ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar al'ummar karamar hukumar Dala, ya samu lambar yabo daga kungiyar ABBA KA CIKA GWARZO, bisa irin gudunmawar da yake bayarwa a jihar Kano, muna godiya da wannan karamci naku, Member ya gode.


Lawan Hussaini Media Team

18/05/2026

LAWAN HUSSAINI MEGA EMPOWERMENT 2026🔥

Hon. Lawan Hussaini Chediyar Yan Gurasa, Ɗan Majalisar Jiha Na Dala.

Wasu daga cikin makarantun da Hon. Lawan Hussaini Cheɗiyar Ƴan Gurasa ya samar a Ƙaramar Hukumar Dala:Gina makaranta a u...
18/05/2026

Wasu daga cikin makarantun da Hon. Lawan Hussaini Cheɗiyar Ƴan Gurasa ya samar a Ƙaramar Hukumar Dala:

Gina makaranta a unguwar Yan Balangu, Mazabar Dala.

Gina makaranta a Baban Sama, Mazabar Yelwa.

Gina katafariyar makarantar sakandare a Kantudu.

Gina makaranta a Arzai, Mazabar Kofar Mazugal.

Gina makarantar Raudat a Layin Dorawar Tsohon Soja, Kurna (Mazabar Gobirawa).

Gina makarantar Islamiyya tare da masallaci a Mazabar Adakawa.

Rabon kayan makaranta (uniform) ga ɗaliban asalin Ƙaramar Hukumar Dala.

~Sufee
18/May/2026

Daga 2023 Zuwa 2026 Ya Samar Da Aiyukan Da S**a Laƙume N 1,300,000,000 a Faɗin Ƙaramar Hukumar Dala. Sannu Da Ƙoƙari Hon...
17/05/2026

Daga 2023 Zuwa 2026 Ya Samar Da Aiyukan Da S**a Laƙume N 1,300,000,000 a Faɗin Ƙaramar Hukumar Dala. Sannu Da Ƙoƙari Hon. Lawan Hussaini Cheɗiyar Ƴan Gurasa.

TARON TABBATAR DA ƳAN TAKARA A ƘARAMAR HUKUMAR DALA.Alhamdullillah yau Asabar 16/05/2026 jam'iyar APC reshan ƙaramar huk...
16/05/2026

TARON TABBATAR DA ƳAN TAKARA A ƘARAMAR HUKUMAR DALA.

Alhamdullillah yau Asabar 16/05/2026 jam'iyar APC reshan ƙaramar hukumar Dala ta gudanar da taron tabbatar da ƴan takara a matakin majalisar jiha da tarayya, inda jam'iya ta amince da Hon. Lawan Hussaini a matsayin ɗan majalisar jiha tare da taƙwaransa Hon. Aliyu Sani Madaki a majalisar tarayya a kakar zaɓen 2027. Taron ya gudana a hedkwatar jam'iyar APC dake ƙaramar hukumar Dala, bisa jagorancin shugabannin jam'iyya da jagororin Dala. Muna addu'ar Allah ya tabbatar wa da jam'iyyar APC Nasara cikin sauƙi tun daga sama har ƙasa. Allahummah Ameen.


Lawan Hussaini Media Team

HON. LAWAN HUSSAINI CHEDIYAR YAN GURASA, CONSTUENCY PROJECT 2023 ZUWA 2026.Alhamdullillah daga 2023 zuwa yau Hon. Lawan ...
15/05/2026

HON. LAWAN HUSSAINI CHEDIYAR YAN GURASA, CONSTUENCY PROJECT 2023 ZUWA 2026.

Alhamdullillah daga 2023 zuwa yau Hon. Lawan Hussaini Cheɗiyar Ƴan Gurasa, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Jihar Kano, ya samarda aiyukan da s**a haura Biliyan Dubu Da Ɗari Uku 1,300,000,000, a faɗin ƙaramar hukumar Dala.

Ga su kamar haka:-

1. Ya samarda Vocational Training Centre a Gwammaja Filin-Jet, wanda yakai kashi casa'in cikin darin na aikin yanzu haka ana gab da kammalawa.

2. Ya samarda Masallaci mai dauke da Makaranta a saman shi, a cikin Adakawa kusa da gidan kallon Sharu Garzali.

3. Ya samarda makarantar Islamiyya ta Baban-Sama cikin mazabar Yalwa.

4. Ya samarda Makarantar Islamiyya mai hawa biyu ajujuwa guda shida da ofisoshi da bandakuna a Kurna Dorawar Tsohon Soja dake mazabar Gobirawa.

5. Ya sabunta Asibitin Burji dake unguwar Bakin-Ruwa tareda da dawo dashi bakin aiki bayan shafe shekaru a rufe.

6. Ya samarda dakunan kwanci da ofisoshi da bandakuna a cikin Asibitin Gidan-Dagaci a mazabar Gobirawa.

9. Ya samarda dakin duba marasa lafiya da ofis da bandaki da rumfa a Asibitin Umma-Zariya a Filin-Durumi cikin mazabar Gobirawa.

10. Ya samarda katafaren gini mai dauke da dakunan kwanciya da ofisoshi da bandakuna a Asibitin Tudun-Bojuwa (Dan-Asibiti) mazabar Gobirawa.

11. Ya samrda da bandakuna a cikin makarantar Beraye a mazabar Kofar-Ruwa.

12. Yanzu anci kaso hamsin na aikin dakunan kwanciya da ofisoshi da bandakuna a cikin Asibitin Lunkwi dake mazabar Kofar-Ruwa.

13. Ya samarda karamar sakandare mai rukunin ajujuwa da ofisoshi da bandakuna har guda hudu a mazabar Kantudu, wanda yanzu haka anci kashi arba'in na aikin ta.

14. Ya gina katafariyar kwata mai tsahon gaske tareda rufeta a lungun Sharu-Dalami dake mazabar Dala.

15. Ya gina Kwata tareda rufeta, mai tsasyin mita dari uku da doriya a cikin unguwar Kul-kul dake mazabar Yalwa.

16. Ya samar da aikin lungu kal-kal ta hanyar gina Kwata da rufeta da shimfida Inter-Locks a cikin unguwar Aikawa dake mazabar Bakin-Ruwa.

17. Ya shimfida Inter-Locks da gina Kwata tareda rufeta a cikin unguwar Chediyar Yan Gurasa zuwa gidan Sheikh Mudi Salga.

18. Ya gina katafariyar kwata a unguwar Juma dake mazabar Kantudu.

19. Ya gina Kwata tareda rufeta a unguwar Limanci zuwa Yantandu dake mazabar Adakawa.

20. Ya gina doguwar Kwata a lungun Goda Makafin-Dala dake mazabar Kabuwaya.

21. Ya gina Kwata a Bunawa dake mazabar Bakin-Ruwa.

22. Ya gina kwata a lungun Fura cikin mazabar Madigawa.

23. Ya sanya Fitulun Solar a Asibitoci guda goma dake karamar hukumar Dala.

24. Ya yi Empowerment na Naira miliyan arba'in da takwas, kowace mazaba mutum dari biyu ne kowanne su ya rabauta da Naira dubu ashirin jimila Naira miliyan hudu.

25. Ya samarwa mutum ɗari da ƴan kai aikin yi na dindindin a mabambantan ma'aikatun gwamnatin jihar Kano, ƴan asalin ƙaramar hukumar Dala.

26. Ya bai wa mata ɗari da ashirin kekunan ɗinki don su dogara da kan su.

27. Ya raba wa matasan ƙaramar hukumar Dala Babura guda ɗari da biyar don bunƙasa walwalar su.

28. Gwamna Alh. Abba Kabir Yusuf ya sahale mai aikin gina katafariyar kwata a unguwar Ayagi wadda ta lakume kudi har Naira miliyan dari uku da saba'in.

29. Ya kai koke kan sanya Fitulun Solar akan titin Jakara zuwa Goron Dutse Alhamdullillah yanzu haka an kammala aikin su.

30. Ya gabatar da kudire-kudire wanɗanda zasu kawowa Dala cigaba dama jihar Kano.

31. Ga taimakon daidai kun al'umma da yan jam'iyya wanda kullin cikinsa yake, ta hanyoyi mabambanta.

Bayan waɗannan akwai wasu. duba da irin wannan hoɓɓasa da Member ya yi muna ganin ya dace mu sake zaɓar sa don ɗorawa akan waɗannan Aiyukan alherin nasa.

Signed
Nasa'i Abdullahi
SSA Media & Publicity to Majority Leader Kano State House of Assembly, Dala Constituency.
Friday 15/05/2026.

🌹🕋SAKON BARKA DA JUMA.A DAGA FADAR HON LAWAN HUSSAINI MAJORITY LEADER KANO STATE DAN MAJALISAR JAHA MAI WAKILTAR DALA🌹🕋*...
15/05/2026

🌹🕋SAKON BARKA DA JUMA.A DAGA FADAR HON LAWAN HUSSAINI MAJORITY LEADER KANO STATE DAN MAJALISAR JAHA MAI WAKILTAR DALA🌹🕋

*🟤FALALAR KAWAR DA CUTA DAGA KAN HANYA🟤*

_🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Wata rana wani mutum yana tafiya akan hanya, sai ya sami reshen qaya a kan hanyar, sai ya daukeshi, sai Allah ya yimasa godiya kuma ya gafarta masa.🌹🌹_

Mai Girma Leader Hon Lawan Hussaini yana yiwa kowa fatan Alkairi da fatan Munshiga sabuwar shekarar 2026 Lafiya Allah yasa Ameen dafatan kowa zaiyi juma.a Lafiya Allah yasa Haka Ameen🌹🕋


LAWAN HUSSAINI MEDIA TEAM
15/5/2026

14/05/2026

Address

Dala Kano State Nigeria
Kano
700101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Lawan Hussaini Media Team posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share