12/07/2026
🚨 Netanyahu Ya Gargadi Pakistan Kan Hulɗar Kasuwanci Da Iran 🇮🇱🇵🇰
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi gargadi kai tsaye ga Pakistan, yana mai cewa bai kamata ƙasar ta sayi mai daga Iran ko kuma ta shiga wata hulɗar kasuwanci da ita ba.
Netanyahu ya yi barazanar cewa idan Pakistan ta ci gaba da yin kasuwanci da Iran, za ta iya fuskantar irin abin da ya ce Isra’ila ta yi wa Iran na lalatawa.
Wannan magana ta zo ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin rikici da takun-saka tsakanin Isra’ila, Iran da ƙawayensu a yankin Gabas ta Tsakiya.
Me kuke tunani kan wannan gargadin da Netanyahu ya yi wa Pakistan?