21/09/2025
Muna farin cikin sanar da al’umma cewa mun samu nasarar rabawa ɗaliban Dan Agundi Special Primary School littattafai sama da 2000 ta hannun Comr. Abdulhakim Kumbotso, karkashin jagorancin Kungiyar Daliban Dan Agundi. Wannan wani ƙoƙari ne na kawo ci gaba ga al’umma, musamman ma a bangaren ilimi, wanda ke daga cikin abubuwan da muke baiwa muhimmanci a cikin yankinmu.
Malamai da ɗalibai na makarantar sun nuna matuƙar farin ciki da godiya ga wannan tallafi. A matsayina na ɗaya daga cikin wakilan al’umma, wannan na daga cikin ƙoƙarinmu na kawo wa al'ummar yankinmu ci gaba mai dorewa.-SIK