05/01/2026
Na samu damar halartar bikin yaye daliban shirin horaswa da koyon sana’o’i ga matasa, wanda ƙungiyar matasan Danladi Nasidi multi link da ke Mazabar Mariri, Ƙaramar Hukumar Kumbotso, s**a shirya. Wannan biki ya kasance abin alfahari da farin ciki, domin ya nuna yadda al’umma ke ba da muhimmanci ga cigaban matasa ta hanyar koya musu sana’o’in dogaro da kai.
A yayin jawabi na, na miƙa godiya ta musamman ga dattijan wannan unguwa bisa irin cikakken goyon baya da kulawa da s**a bai wa wadannan matasa. Hakika rawar da dattijai s**a taka wajen ƙarfafa gwiwar matasa su rungumi sana’o’i abin a yaba ne, domin hakan zai taimaka matuƙa wajen rage zaman banza da dogaro da wasu, tare da gina matasa masu anfani ga kansu da al’umma baki ɗaya.
Haka kuma, na yaba ƙwarai da gaske ga malamai da masu koyar da wadannan sana’o’i bisa jajircewarsu, haƙuri da kishin da suke nuna wa matasa. Irin wannan sadaukarwa daga gare su shaida ce cewa har yanzu akwai mutanen da ke ɗaukar ilimi da koyar da sana’a a matsayin hidima ga al’umma. Gudummawar su ba kawai ilimi ba ce, har ma gina makomar matasa mai inganci domin su dogara da kansu
Bugu da ƙari, na yi kira ga sauran mazabu da ƙungiyoyin matasa a faɗin Ƙaramar Hukumar Kumbotso da su yi koyi da wannan kyakkyawan tsari. Samar wa matasa hanyoyin koyon sana’o’i da dogaro da kai shi ne ginshiƙin cigaban al’umma, domin matashin da ya samu sana’a ya samu makoma, ya samu mutunci, kuma ya zama ginshikin zaman lafiya da ci gaba.
Na kuma taya Hon Kamaludden Abubakar Baba wakilin shugaban karamar hukumar kumbotso comrd Abdullahi ghali basaf karbar lambar girmamawa ( graphic award) da daliban wannan makaranta wanda s**a koyi graphic s**a yiwa shugaban bisa irin gudummawar da yake bawa matasan karamar hukumar kumbotso
A ƙarshe, ina tabbatar wa wannan ƙungiya da dukkan mahalarta cewa a ƙarƙashin Majalisar Matasan Ƙaramar Hukumar Kumbotso, za mu ba da duk wata gudummawa da goyon baya gwargwadon iko domin ƙarfafa wannan gagarumin ƙoƙari da suke yi na tallafa wa matasa. Domin kuwa wannan shi ne burinmu tun farko na ganin matasanmu sun samu ilimi, sana’a, da kyakkyawar rayuwa mai ɗorewa.
Allah Ya saka wa kowa da alheri, Ya kuma albarkaci wannan shiri na tallafawa matasa
~ Comr. Ahmad Tijjani Muhd
Shugaban Majalisar Matasan
Ƙaramar Hukumar Kumbotso