Ɗan Malam

Ɗan Malam Mun buɗe wannan shafi ne domin tallata Engr Abba Ganduje a DTR. Yadda nake kokari wajen rike masoyina. To haka nake kokari wajen kujewa duk wani makiyina.

Allah ka hadamu da masoyanmu. Karabamu da makiyanmu amin.

Press Release24/11/2021The Chairman of Tofa Local Government council, Alhaji Nafi'u Haruna Garba Yarimawa has inaugurate...
24/11/2021

Press Release
24/11/2021

The Chairman of Tofa Local Government council, Alhaji Nafi'u Haruna Garba Yarimawa has inaugurated Fourteen member Committee on Consumer Protection Committee to check fake goods in the area.

Alhaji Nafi'u Haruna Garba Yarimawa inaugurated the committee said the selection of members was base on merit and urged them to redouble efforts towards achieving the set objectives.

He charged them to work in accordance with terms of reference of the committee.

In his remark, the Director Personnel Management, Alhaji Rabi'u Abdullahi Daurawa expressed the local Government readiness to implement the present administration policies on fake and substandard products.

The members are Head of Water Sanitation and Hygienic Malam Bashir Mudi as Chairman, Head of Community Munzali Alhassan as Secretary, Representative of District Head Dr. Alhaji Isyaku Umar Tofa ( Mak**an Bichi) as member and Divisional Police Officer.

Others are Representative of Women organization Malama Binta Inuwa member, Primary Healthcare Coordinator Alhaji Baba Isa Representative as member and Information Officer also serve as member.

From Abdu Bako Abdullahi Information Officer Tofa Local Government council.

NAN BADA DADEWA BA ZA'A KAMMALA TITIN GARIN LAMBU- YARIMAWA ZUWA YALWA KARAMA DAKE KARAMAR HUKUMAR TOFA.A Kokarinsa na G...
24/11/2021

NAN BADA DADEWA BA ZA'A KAMMALA TITIN GARIN LAMBU- YARIMAWA ZUWA YALWA KARAMA DAKE KARAMAR HUKUMAR TOFA.

A Kokarinsa na Ganin ya Samar da Tituna Masu Inganci a Fadin karamar Hukumar Mai Girma Shugaban Karamar hukumar Tofa Hon. Nafiu H Garba Yarimawa, Zai cigaba da Gina titin garin Lambu, Yarimawa, Yalwa karama Dake Karamar hukumar, Domin Inganta Harkokin Sufiri Wajen Zirga zirga ga Mabiya Hanyar Musamman Wajen Fito da Kayayyakin amfanin Gona ga Manoman Yankin Baki Daya.

Shugaban karamar hukumar Yasha alwashin kammala T**in nan bada Dadewa ba, Yayin da Zaa Gudanar da aikin ta karkashin maaikatar kananan hukumomi Wanda Hon Murtala Sule Garo, Yake Jagoranta kuma ya Amince Da ayi Bisa Sahalewar Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Tuni dai Shugaban Karamar hukumar ya karbi Bakuncin Direktoci Daga maaikatar Kananan Hukumomi Domin duba yadda aikin T**in zai Kasance Domin Kammala shi akan Lokaci.

Idan Zamu Iya Tunawa Shugaban Karamar hukumar ya Fara aiwatar da wannan aiki a Shekarar data Gabata, Yayin da Za'a Cigaba da titin a Wannan Lokaci Domin Kammala shi.

Haka kuma, Nan bada Dadewa ba Za'a Fara T**in five Kilometers dake Cikin Garin Tofa Wanda Mai Girma Gwamna ya Amince a Kammala shi. Yau Laraba, 24 November 2021.

GINA MASALLACI A KASUWAR JANGUZA DAKE KARAMAR HUKUMAR TOFAMai girma Shugaban karamar hukumar Tofa Hon. Nafiu H Garba Yar...
08/11/2021

GINA MASALLACI A KASUWAR JANGUZA DAKE KARAMAR HUKUMAR TOFA

Mai girma Shugaban karamar hukumar Tofa Hon. Nafiu H Garba Yarimawa, ya Bada Umarnin Gina Masallacin Kamsal Salawati a Cikin Kasuwar Janguza Domin Taimakawa Yan Kasuwar Wajen Gudanar da Ibada akan Lokaci.

Shugaban Karamar hukumar Yana Gina masallacin ne a Bangaren da ake sayar da Dabbobi Dake cikin Kasuwar a Kokarinsa na ganin ya bada gudunmowarsa a Fannin Addinin Musulunci, Wanda Yanzu haka ana Dafda kammala shi baki daya.

Yau Lahadi 7 November 2021.

ANA DAF DA KAMMALA GINA AJUJUWA A MAKARANTAR FIRAMARE TA UNGUWAR KAMFA DAKE MAZABAR YARIMAWA, A KARAMAR HUKUMAR TOFA.A K...
04/11/2021

ANA DAF DA KAMMALA GINA AJUJUWA A MAKARANTAR FIRAMARE TA UNGUWAR KAMFA DAKE MAZABAR YARIMAWA, A KARAMAR HUKUMAR TOFA.

A Kokarinsa na Ganin Ya Kawo Ayyukan Raya kasa a Mazabun Karamar hukumar Tofa Baki daya, Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Nafiu H Garba Yarimawa, Ya Bada Umarnin Gina Ajujuwa Wato Class Room Block a Makarantar Firamare ta Unguwar Kamfa Dake Mazabar Yarimawa Wanda Yanzu Haka an Kammala kaso Sittin Cikin Dari na Aikin Wanda ake Saran Nan da wani lokaci Kadan Zasu Kammala shi gaba daya.

Kafin Wannan Lokaci Shugaban Karamar hukumar Ya Gina Ajujuwa Guda Biyu mai Dauke da Offishin Shugaban Makaranta a wannan makaranta Wanda tuni an Kammala shi kuma Ana Amfani Dashi a Halin Yanzu.

Idan Zamu Iya Tunawa ita dai Wannnan Makaranta Tare da alummar Yankin Sun Dade suna Kira ga Mahukunta Dasu Gina Musu Karin Ajujuwa Domin Magance matsalar da suke fama da ita a wannan Makaranta.

Baya ga Haka Shugaban karamar Hukumar Ya Gina Kwalbati Domin Amfanin Mutanan Yankin Domin Magance Matsalar Zaizayar Kasa da Take Addabar Yankin, Haka kuma Ya Amince da Gina Gada Wato Bridge a Unguwar ta Kamfa Domin Saukakawa Mutanan Yankin wajen Wucewa Zuwa Babbar Hanya ta Yan Rake Wanda zaa fara aikin nan bada Dadewa ba.

Mazabar Yarimawa Tana Daya Daga Cikin mazabun Karamar hukumar Wanda S**a amfana da ayyukan raya kasa ta Karkashin Shugaban Karamar hukumar Wanda ya Hada da Gina Asibitin Shakatafi a Unguwar Santar Dankaka, Gina Babbar Gada a Garin Jataka Wanda Mahada ce zuwa Garuruwa Dabam Dabam, Gyaran Naura mai Bada hasken Wutar Lantarki a unguwar Kamfa, Sanya Naura mai Bada Hasken Rana a Babban masallacin Juma'a na Garin Yarimawa, Gina Masallacin Kamsal salawati a Garin Jataka, Fara Gina T**i Daga Garin Lambu, Jataka, Yalwa karama, Jobe zuwa Karamar hukumar Dawakin Tofa Wanda Nan bada Dadewa ba zaa Cigaba da aikin.

shugaban karamar hukumar ya Gina Rijiyoyin Burtsatse tare da Gyaransu a Dukkannin Unguwanni dake Mazabar Yarimawa, Bawa Matasa Takardar daukar aiki, tare da bawa Wasu Na Wucin Gadi, da dai Sauran Muhimman Ayyukan Raya kasa Wanda shugaban karamar Hukumar Ya Gabatar a wannan Mazaba.

Yau Alhamis 4 November 2021.

FLASH BACKAIYUKA DA NASORORIN SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR TOFA A KWANA 100 MASU ALBARKAKaramar Hukumar Tofa na 'daya daga c...
03/11/2021

FLASH BACK

AIYUKA DA NASORORIN SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR TOFA A KWANA 100 MASU ALBARKA

Karamar Hukumar Tofa na 'daya daga cikin kananan hukumomin jihar Kano wanda zasu fito a sahun farko ta fuskar samun aiyukan raya kasa da walwalar al'umma Dalilin zuwan jajirtaccen shugaba Alhaji Nafiu H. Garba Yarimawa

Hon Nafiu Yarimawa zuwan sa keda wuya ya dauki aniyar sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana ga 'daukacin masallatan juma'a dake sassa daban daban na mazabun karamar hukumar

Haka kuma nan bada jimawa ba kimanin mutane 130 zasu rabauta da aikin yi na din-din-din daga Shugaban karamar hukumar

Haka zalika Shugaban karamar hukumar da hadin gwaiwar gwamnatin jihar Kano da kuma Bankin duniya na shirin Samar da tafkeken Dam a garin 'Yan sabo dake mazabar Yanoko

Bugu da kari Shugaban karamar hukumar ya bayar da umarnin daukar matakin gaggawa ga wata makwarar ruwa dake Cikin garin Yarimawa

Dadin-dadawa Shugaban ya bayar da tallafin buhunan shinka dana gero ga daukacin al'ummar mazabu 15 da sauran kungiyoyin al'umma dake fadin karamar hukumar duka a kokarinsa na ganin anyi azumi cikin walwala da jindadi

Kimanin matasa 200 ne 'Yan Social Media s**a rabauta da kayan abinci da kudin cefane, domin ganin anyi bukukuwan sallah cikin nutsuwa

Wadannan sune kadan daga cikin nasarori da aiyukan alkhairi da Shugaban ya aiwatar a cikin kwana dari (100) kacal da yayi a Offis a matsayin shugaban karamar hukumar Tofa karo na 2

Allah Ubangiji ya saka masa da mafificin Alkhairi ya kuma kara masa kwarin gwiwar cigaba da kwararo aiyukan alkhairi ga al'ummar karamar hukumar. Ameen 🙏🙏🙏

TAKARAR ABBA TANA NAN DARAM DAM DAM DON HAKA KU CIGABA DA YADA MANUFOFIN ENGR UMAR ABDULLAHI GANDUJE KAWAI.Sakon Kwamnad...
13/10/2021

TAKARAR ABBA TANA NAN DARAM DAM DAM DON HAKA KU CIGABA DA YADA MANUFOFIN ENGR UMAR ABDULLAHI GANDUJE KAWAI.

Sakon Kwamnada Murtala Sule Garo zuwa ga Alummar Kananan hukumomin Dawakin Tofa Rimingado da Tofa.

Mai Girma kwamishinan Maaikatar Kananan hukumomi Dr Murtala Sule Garo, yayi Kira ga Matasan Kananan Hukumomin DTofa Rgado da Tofa Cewa Duk Abinda Matasan Wannan yanki suke so a kakar Zabe ta 2023 Shi Mai girma gwamna yake so Don Haka ku Cigaba da wayar da kan Matasa akan wannan Tafiya ta Engr Umar Abdullahi Ganduje, Domin Mai Girma Gwamna Dan siyasa ne zai Bawa kowa Damarsa.

Hon. Garo, ya fadi hakan ne Yau a Hedikwatar Karamar hukumar Dake cikin Garin Tofa wajen Bawa Matasa mutum 1000 Tallafin Dogaro da kai Wanda Shugaban Karamar hukumar Yayi, Yayin da yake amsa Tambayoyi ga Matasan Karamar hukumar wanda S**a yi masa akan Lallai Engr Umar Ganduje, ya Tsaya Takarar Dan Majalissar Tarayya a 2023, Yayin da Kwamishinan Nan take ya Amsa da cewa a Cigaba da yada manufofinsa kawai Insha Allahu Yana Nan Tafe Domin Duk Abinda Alummar Suke so Babu Shakka Mai Girma Gwamna na Tare Dashi.

Hon. Murtala Sule Garo, ya Yaba Kwarai da Gaske kan yadda Yaga Matasa Suna Nuna Shauki tare da Soyayya ta Zahiri ga Engr Abba Abdullahi Ganduje, Domin Lallai yazo ya Wakilce su a kakar zabe ta 2023.

Daga Bisani Engr Ganduje, Ya Tashi Bisa Rakiyar Wasu Shugabannin Kananan Hukumomi zuwa Tsakiyar Filin Taro Domin Jinjinawa Matasan Tare da Godiya bisa Yadda s**a Nuna Masa Soyayya tare da kauna akan Bukatar su.

Engr Umar Ganduje, na Tare da Amininsa Shugaban Karamar hukumar Nasarawa Hon. Auwal Lawan Aranposu. Yau Talata October 2021.

Rahoto
Rufai Muhd Tofa

MUTUM DUBU DAYA MAI DAKIN GWAMNA PROF HAFSAT GANDUJE, TA BAWA TALLAFIN DOGARO DA KAI A KARAMAR HUKUMAR TOFA.Mai Dakin Gw...
13/10/2021

MUTUM DUBU DAYA MAI DAKIN GWAMNA PROF HAFSAT GANDUJE, TA BAWA TALLAFIN DOGARO DA KAI A KARAMAR HUKUMAR TOFA.

Mai Dakin Gwamnan kano Prof Hafsat Abdullahi Ganduje, Tare da Kwamishinan Maaiktar Kananan Hukumomi Dr Murtala Sule Garo, Sun Jagoranci Bawa Mutum 1000 Tallafin Dogaro da kai a karamar hukumar Tofa, Yayin da aka Bawa Mata mutum 600 Tare da Maza Mutum 400 Wanda shugaban karamar Hukumar Hon Nafiu H Garba Yarimawa, ya Bawa Alummar Karamar hukumar a Kokarinsa na Inganta Rayuwar Matasan Yankin baki daya.

Yayin da kowanne ya Rabauta da kudi Naira Dubu goma goma Wanda Jimillarsu ya k**a Naira Naira Miliyan Goma dai dai.

Prof Ganduje ta Yaba da Kokarin Shugaban Karamar Hukumar Bisa Tallafawa Al'ummarsa Tare da koyi da Mai Girma Dr Abdullahi Umar Ganduje, wajen Taimakawa Matasa da Jarin Dogaro da kai Domin Ciyar da karamar hukumar Gaba.

Taron ya Samu Halattar Mak**an Bichi Hakimin Tofa Dr Isyaku Umar Tofa, Kwamishinan Maaikatar Ayyuka Hon. idirs Garba URimi, wasu daga cikin Shugabannin Kananan Hukumomi da dai Sauran Matasa Dabam dabam. Yau Talata 12 October 2021.

Rufai Muhd Tofa

HON.NAFI'U YARIMAWA YA GOGE TARAHIN SIYASAR JOBE A KARAMAR HAKUMAR TOFA.Ya zama wajibi a garemu mu Kara bayyana godiyarm...
29/09/2021

HON.NAFI'U YARIMAWA YA GOGE TARAHIN SIYASAR JOBE A KARAMAR HAKUMAR TOFA.

Ya zama wajibi a garemu mu Kara bayyana godiyarmu ga ALLAAH bisa nasarar samun haziki kuma fasihin shugaba Mai son cigaban al-ummarsa wato HON.NAFI'U H. GARBA YARIMAWA.

Al-ummar wannan karamar hakuma shaidane a cikin shekara daya (1 year) Mai girma zababben shugaban karamar hukumar Tofa ya samawa Matasa Dari uku da takwas (308) aikinyi domin dogaro dakai a wannan karamar hukuma.

Misali.

1.Matasa Dari da daya (101) suke amfana da tsarin TEMPORY a matsayin FIRST BATCH.

2.Matasa Dari da bakwai (107) ne zasu amfana da tsarin TEMPORARY a matsayin SECOND BATCH ciki hadda ma'aikatan lafiya da Malaman makaranta.

3. Matasa Dari (100) ne s**a Fara amfana da allawonces na naira Dubu ashirin ( #20,000) dan bunkasa harkokin tsaro a wannan karamar hukuma.

Tabbass bambanci a bayyana yake kuma gaskiyar al-amarin a fili take, yau kimanin shekara goma sha shida (16) HON.TIJJANI ABDULJADIR JOBE yana wakiltar DTR a zauren majalissar kasa amma har izuwa wannan lokaci bazaku iya lissafa Matasa Goma sha shida (16) da s**a sami aikinyi domin dogaro da Kansu ta hannunsa ba, gashi kuma babu kudiri a majalissa, ballantana ayyukan raya kasa.

Dan haka muke cigaba da yin godiya ga al-ummar karamar hukumar Tofa bisa cigaba da gamsuwa da shugabancin Mai girma zababben shugaban karamar hukumar tare da addu'ar ALLAAH ya Kara masa kwarin gwiwa dan cigaba da zazzago mana ayyukan cigaba a lungu da sako na wannan karamar hakuma.

Daga Baseer Mbt

AN HARAMTA SAYAN MAN FETIR  A JARKOKI A GIDAJEN MAI NA KARAMAR HUKUMAR TOFA.Bisa Dalilan Tsaro Mai Girma Shugaban karama...
22/09/2021

AN HARAMTA SAYAN MAN FETIR A JARKOKI A GIDAJEN MAI NA KARAMAR HUKUMAR TOFA.

Bisa Dalilan Tsaro Mai Girma Shugaban karamar hukumar Tofa Hon. Nafiu H Garba Yarimawa, ya Bada Umarnin Gaggawa ga Masu Gidajen Mai Wato Filling station Dasu Daina Sayarwa da Masu Jarkoki Mai a Fadin karamar hukumar Baki Daya, Shugaban karamar hukumar Yace Duk Mutumin da yazo SayA A JARKOKI kada a sayar Masa Idan Kuma Muka K**a mutum ya sayar Tare da Wanda aka Sayarwa Zamu Dauki Matakin Rufe Gidan man Gaba Daya Tare da Daukar Mataki akansu.

Shugaban karamar hukumar ya Baza Jami'an Tsaro Domin Tabbatar da wannann Doka, Sannnan ya Umarce su da Su cafke duk Wanda aka k**a Da JARKOKI Dauke da Man Fetir ko Gas Walau a Mota ko akasin Haka Matukar Yana Dauke da Man Fetir, Shugaban karamar hukumar ya Fadi hakanne a wani Taro da ya Kira a Offishin sa dake Sakatarial mulkin karamar hukumar tare da Kungiyoyin Al'umma Wanda ya Hada da Kungiyar Direbobi ta NURTW, Kungiyar Dillalai, Kungiyar Yan Kasuwa, Kungiyar Masu Gidajen Mai, kungiyar Employees tare da Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah.

Hon Yarimawa, yace Sun Dauki Wannan Mataki ne Bisa Inganta Harkar Tsaro a Fadin karamar hukumar, Bugu da Kari Yace ya Dauki Maaikatan Sa kai na Vigilant Mutum 100 Domin Shiga Lungu da Sako na karamar hukumar.

Haka Kuma yace ya Samar da Baburan Hawa Tare da Mota DOMIN Bawa Jami'an Tsaron Wajen Yin Sintiri Tare da Sanya Ido Wajen shige da fice na Mutane.

Shugaban karamar hukumar yayi Kira ga al'umma Dasu Sanya Ido Sosai ga Duk Mutumin da S**a Gani Basu Yadda Dashi ba Da suyi Gaggawar Sanarwa da Jami'an Tsaro Mafi kusa Domin Daukar Mataki na Gaba.

Shugaban karamar hukumar ya Kara bada Umarni Ga Dillalai da Masu Unguwanni su guji Bada Haya tare da sayar da Gonakai, Gidaje, Filaye ga Bakin Fuska ba Tare da Bincike ba, Don Haka Shugaban karamar Ya bada Umarni ga Dukkannin al'ummar karamar hukumar Wanda Zasu yi sayayya su Tabbatar sun Mallaki Shedar Takarda ta karamar hukuma Domin Kara Samun Cikakken Zaman lfy a karamar hukumar Baki Daya.

Taron Ya Samu Halattar Masu ruwa da Tsaki na karamar hukumar Wanda ya Hada da Shugaban JAM'IYAr APC Hon. Murtala Inyako Lambu, Shugaban Rundunar Yansanda ta karamar hukumar ASP Isyaku MD, Mabanbantan Kungiyoyin Al'umma da dai Sauran su a Kokarinsa na Tabbatar da Zaman Lafiya Mai Dorewa a Fadin karamar hukumar Baki Daya.

Yau Laraba, 22 September 2021.

Commander 🔥 🔥🔥🔥
21/09/2021

Commander 🔥 🔥🔥🔥

Mai Girma Shugaban karamar hukumar Tofa Hon Nafiu H Garba Yarimawa,ya Jagoranci Zama na Musamman akan Harkokin Tsaro da ...
21/09/2021

Mai Girma Shugaban karamar hukumar Tofa Hon Nafiu H Garba Yarimawa,ya Jagoranci Zama na Musamman akan Harkokin Tsaro da Dagatai da Masu Unguwanni Wanda aka gudanar a Fadar Mak**an Bichi Hakimin karamar hukumar Dr Isyaku Umar Tofa.

Shugaban karamar hukumar yaja Hankalin su Dasu Dage dantse Tare da Sanya Ido wajen Shige da Ficin Mutane Musamman bakin Fuska DOMIN Samar da Cikakken Tsaro a Gundumominsu.

Haka Kuma Shugaban karamar hukumar ya Amince da Daukar Maaikatan Sa kai na Vigilant mutum 100 a kokarinsa na Inganta Harkar Tsaro a Fadin karamar hukumar Baki Daya. Taron ya Samu Halattar Mak**an BICHI Hakimin Tofa Dr Isyaku Umar Tofa.

Mai girma shugaban karamar hukumar Tofa Hon Nafiu H Garba Yarimawa, ya karbi bakuncin kungiyar Gwaggo Youths Development...
20/09/2021

Mai girma shugaban karamar hukumar Tofa Hon Nafiu H Garba Yarimawa, ya karbi bakuncin kungiyar Gwaggo Youths Development Forum karkashin jagorancin Najib Idris Rano.

Wanda s**a kawowa shugaban karamar hukumar ziyarar girmamawa tare da gabatar masa da kungiyar a Offishin sa dake Sakatarial mulkin karamar hukumar.

Yau Litinin 20 September 2021.

Address

Tofa
Kano
1234

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ɗan Malam posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Ɗan Malam:

Share