31/07/2025
SANARWA DAGA HUKUMAR KULA DA AIKIN 'YAN SANDA NA KASA
Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (Police Service Commission) karkashin jagorancin Dattijon kirki DIG Hashimu Salihu Argungun (rtd) tana shirin daukar 'yan Nigeria da suke da DEGREE, HND da ND aikin 'yan sanda a matakin Cadet ASPs da INSPECTORs
An jima da dakatar da tsarin direct entrance service na Police wanda suke fitowa da mukamin ASP da INSPECTOR shekaru 12 da s**a wuce tun bayan da aka kirkiri P***C, amma yanzu DIG Hashimu (rtd) ya dawo da tsarin, suna karban horo ne a Police Staff College dake Jos jihar Pilato
Don haka masu sha'awa sai su kasance cikin shiri, domin kwanannan za'a fitar da tsarin daukar aikin, na tattauna da Maigidana kuma Malami Dr Muhammad Amin Garba akan tsarin, yace min ba karamin cigaba za'a samu ba
Sannan DIG Hashimu Argungun yayi rantsuwa yace zai tabbatar da anyi adalci wajen diban sabbin 'yan sandan masu Degree da Diploma, yayi gargadi yace duk wani mutum da aka samu ta bayan fage da yunkurin cin amanar tsarin diban za'a kamashi ya fuskanci hukunci, zai tabbatar anyi adalci ba tare da wani ya bada cin hanci ko ya nemi kamun kafa a gurin wani ba
A sanina hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa bata taba samun Chairman din da yake aiki da gaskiya sannan ya rike amana kamar DIG Hashimu Argungun ba, mutumin kirki ne mai halin Dattako
Idan an fitar da tsarin zamu sanar anan, sannan kar a karaya da cewa wannan aikin dan talaka ba zai samu ba, a jarraba, ina da yakini dari bisa dari akan DIG Hashimu zai yi iya bakin kokarinsa domin talakawa su samu
Allah Ya masa jagoranci, sannan muna fatan Allah Ya bawa masu rabo sa'a