11/05/2025
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Jagoranmu Jagoran Talakawa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ……….
Da Fari Ina Mika Sakon Gaisuwa Ga Mai Girma Jagora Muna Rokon Allah Ya Kara Daga Darajarka Ya Kara Baka Lafiya Da Kaifin Basira Ya Kareka Daga Sharrin Masu Sharri Sannan Yayi Riko Da Hannayenka Ya Doraka Akan Dai Dai.
Abu Na Gaba Shine Mai Girma Jagora Munji Ra’ayoyin Mutane Da Yawa Akan Sauya Jam’iyya Wanda Da Yawa Daga Cikin Mutanen Da Muka Tuntuba Da Kuma Sauran Wayanda Bamu Tuntuba Bama Sun Bayyana Mana Ra’ayinsu Da Sha’awarsu Akan Ka Jamu Ka Kaimu Duk Inda Kakeso Mu Masu Biyayya Ne a Gareka Kamar Yadda Mai Girma Gwamna Ya Fada a Satin Nan Da Bakinsa.
Da Wannan Damar Muke Rokon Mai Girma Jagora Da Kayi Duba Na Tsanaki Ka Daukemu Ka Kaimu Jam’iyyar APC Dan Allah Saboda Wasu Dalili Masu Karfi Da Muke Dasu Wayanda Bazasu Fadu Anan Ba.
Sanin Kowa Ne Yadda Wayannan Mutane Suke Mana Bita Da Kulli Sun Hana Gwamnatin Rawar Gaban Hantsi Bisa Jagorancin Wasu Mutane Daga Fadar Shugaban Kasa Wanda Da Muna Jam’iyyar APC Babu Wanda Ya Isa Yayi Mana Haka Akwai Abubuwa Da Dama Da Wayannan Mutanen Suke Kokarin Toshewa Wannan Gwamnatin Kawai Saboda Ba Jam’iyyarsu Mukeyi Ba.
Ina Da Yakinin Shugaban Kasa Wanda Shine Jagoran Jam’iyyar APC Na Kasa Yafi Ganin Girmanka Akan Kowanne Irin Mutum a APC Arewa Baki Daya Bama Kano Ba
Al’ummar Jihar Kano Masu Saka Jar Hula Da Wayanda Basa Sakawa Yan Siyasa Da Wayanda Ba Yan Siyasa Ba Sun Gamsu Ka Jamu Ka Kaimu APC Saboda a Samu Saukin Wayannan Abubuwan Da Ake Mana Na Rashin Albarka.
Don Allah Madugu Mu Afka Kawai.🤲🏼
Jikan Oga ✍️✍️