03/05/2026
YAN UWANA MATASA AMMA YAYAN TALAKA GA WATA SHAWARA........
✍️Yana da kyau ka kalli cikin Duniyar ka, ka zurfafa tunaninka sosai, ka kalli me ya dace kayi a Rayuwa? tunda na farko dai ba'a ajiye maka ba b***e ka Ɗauka, wataqila ma ka taso Gidanku kaine Babba, wataqila ka ta so Gidanku babu mahaifi (Ya rasu) to ka nutsu kaga me ya dace kayi a Rayuwa??
✍️Idan Rayuwa ta baka damar yin karatu da Aiki ko kasuwanci duk ka haɗa ka jajirce kayi, ka manta da batun ƴan mata ko Abokai ƴan qarya, duk sai idan ka zama wani abu a Rayuwa za su zo gareka, amma idan baka da komai gudun ka za su dinga yi sai Qalilan👌 ka tsaya kayi abin da ya dace👏
✍️Idan kuma Rayuwa kasuwa kawai ta baka ikon yi ka jajirce kanta kaɗai, kuma kar ka damu kan dole sai ka yi karatu a lokacin da babu yanda za kayi karatun, domin wataqila idan ka tafi makarantar ƴan uwanka da iyayenka mata wataqila su jigata ko su tozarta🥺 abin da Rayuwa ta baka dama shi kake yi, kuma wataqila idan ka dawo gida ba Abinci, ana karatu da Yunwa ne?? sannan waye zai ɗauki wahalhalun karatun?? Ko zaka iya ɗauka da sana'ar ka To Gida fa?? To kaga kenan karatu sai Allah yasa kana da Iko, ba ruwanka da waɗanda s**a yi gaba a Rayuwa fiye da kai, ba ruwanka don wani ya wuce ka, Rayuwa ba tseren mota bane, kowa Rabonsa yake riska, dalilin da yasa nace ka daina kallon su shine gaskiya irin wannan tunanin ya jefa matasa da yawa kamuwa da ciwon Damuwa da faɗawa harkar a mutu har Liman, ka tsaya kayi aiki da Hankali a komAI
AIKI DA HANKALI YAFI AIKI DA KARFI