02/06/2026
REMASAB ta karyata zargin rashin biyan Æ´an shara albashin su
Hukumar Kula da tsaftar muhalli da kwashe shara ta Jihar Kano (REMASAB) ta karyata rahotannin da ke ikirarin cewa ba ta biyan ma’aikatanta albashi, tare da zargin cewa wasu ma’aikatan na karɓar Naira 10,000 kacal a kowane wata.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abubakar Ahmad, ya fitar ranar 2 ga Yuni, 2026, REMASAB ta ce zarge-zargen da aka wallafa a wani flyer na shafin Facebook na gidan rediyon Dala FM ƙarya ne kuma ba su da alaƙa da ainihin halin da ake ciki a hukumar.
Hukumar ta bayyana cewa babu wani ma’aikacinta da ke karɓar albashin Naira 10,000, tare da ƙalubalantar duk wanda ke da irin wannan da’awa da ya gabatar da shaidar biyan albashinsa ga hukumar ko ga kafar yaɗa labaran da ta wallafa zargin.
REMASAB ta nuna damuwa kan yadda aka yaɗa rahoton ba tare da neman ƙarin bayani ko tabbatar da gaskiyar lamarin daga hukumarta ba, tana mai cewa hakan ya saɓa wa ƙa’idojin aikin jarida na gaskiya, adalci da ƙwarewa.
Hukumar ta kuma bukaci Dala FM da sauran masu yaÉ—a rahoton su gabatar da hujjojin da s**a dogara da su wajen wallafa zarge-zargen, tare da neman a janye rahoton da kuma gyara bayanan da aka wallafa.
A cewar sanarwar, REMASAB na ci gaba da biyan albashin ma’aikatanta a kai a kai ba tare da jinkiri ba, sannan ta ce ta biya duk wasu basuss**an albashi da ta gada, inda ta jaddada cewa a halin yanzu babu wani ma’aikacin hukumar da ake bin sa albashi.
Hukumar ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa domin kauce wa yaɗa labaran da ba su da tushe.
Daily Nigerian Hausa