15/04/2026
Godiya ta tabbata ga Allah SWT da ya nuna mana rana irin ta jiya a inda jam'iyar mu ta ADC ta gabatar da gangamin convention din ta a birnin taraiya Abuja, wanda kuma Ya samu halartar jigajigen jamiyar k**ar masu Girma Atiku Abubakar, da Jagora Dr Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi da kuma Rotimi Amaechi. Tare da shugabannin jam'iyar ADC na kasa karkashin jagorancin halataccen shugaban mu wato David Mark.
Munga kalubale kala kala daga azzalumar Gwamnatin Tinubu da mukarraban sa domin ganin sun hana taron nan wiyuwa.
Kadan daga cikin abubuwan da s**a mana shine garzawa kotu domin neman rusa shugabancin ADC, wannan bai tasiri ba s**a yi amfani da INEC wajen cire sunan David Mark a matsayin shugaban jam'iya, wannan ma bai hana mu ba s**a koma wajen maganar Venue inda shi ma aka hana mu filin taro na Eagle Square, da National Stadium kai har ma da manyan hotels irin su Hilton, sai wajen event center muka k**a muka biya, shi ma karfe dayan dare s**a matsawa mai wajen lamba cewa zasu rusa wajen ta idan ta bar mu mu kai taro. Sai da manyan mu s**a dira wajen cikin dare har asubah, sannan aka kyale mu. Duk da haka sai da aka turo wasu bata gari s**a yanke wutar lantarkin wurin taron, sai da muka hayo manyan janareto sannan taro ya yiwu.
Banda delegates kusan dubu uku da s**a halarcin taron, da sauran shugabannin jam'iya suma kusan dubu uku, Allah kadai ya san mutum dubu nawa ne akan t**i a wajen taron. Kuma duk ba wanda aka bawa ko kwanan shinkafa duk raayine ya kawo su.
Tabbas na san jiya Tinubu bai bacci ba, ganin yadda muka tsallake wadannan kalubale, kuma akai taro mai armashi lafiya aka gama lafiya. Allah mungode ma!
Daga karshe, sako na ga gwamnatin Tinubu shine, wamakaru wamakarallah, wallahu khairun makirin! Na san ba lallai ace Tinubu ya san ayar nan ba, dan haka na kusa da shi ku masa Tilawa!
Falle daya ce!
Salihu Tanko Yakasai
Sabuwar Tafiya
Kwankwasiya Amana!
15th April, 2026