10/09/2025
🚨Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce irin jarabawa, hawaye, da tashin hankali da ya sha bayan zaben 2023 ya kara zurfafa kudirinsa na kawo sauyi a jihar nan domin amfanin al’ummarta.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin kaddamar da majalisar shura a gidan gwamnati dake Kano.
Da yake tunawa da gwagwarmayar da ta biyo bayan nasarar da ya samu a zaben, Gwamna Yusuf ya ce tafiyar sa zuwa karagar mulki ba abu ne mai sauki ba.
"Na fuskanci kalubale mafi tsanani a rayuwata bayan zaben 2023," in ji shi. “Amma ta wannan kalubale da hawaye, na ci gaba da jajircewa wajen yi wa Kano hidima, har yanzu ina nan saboda karfin Allah, ba don wani mutum ba.”
Ya kara da cewa, yayin da da yawa s**a tadeshi shi, Allah ya sa ya zama gwamna a 2023, kuma Allah ne kadai zai iya tantance makomarsa a 2027.
"Shugabanci baya hannun mutum," in ji shi. "Allah ne ke sanyawa kuma yana cire shugabanni yadda ya so."
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa dole ne shugaba na gaskiya ya mai da hankali kan ayyukan da za su daukaka jama'a, ba wai don cimma wata manufa ta siyasa ba.
"Ko na sake neman takara ko ban sake tsayawa takara ba, aikina shi ne in ci gaba da gabatar da shirye-shirye masu ma'ana wadanda za su amfanar da masu zabe," in ji shi.