Npower Kano

Npower Kano This Page is desicated for Empowerment and Educatonal Purpose for Nigerian Youths, all activities are free

Muna Tuni, a Tanadi statement of Account na Kudaden NPower
28/10/2025

Muna Tuni, a Tanadi statement of Account na Kudaden NPower

Assalam wa Rahmatulaah.

Muna Kiran duk Dan NPower da ba'a Biya shi kudin sa Cikakku ba, ya ciro Statement of Account dinsa na watannin da ya yi aiki, ya hada da Posting later din shi ya ajiye su waje daya ya killace su.

Akwai Sanarwa ta Musamman nan ba da dadewa ba.

Mun gode

Assalam wa Rahmatulaah.Muna Kiran duk Dan NPower da ba'a Biya shi kudin sa Cikakku ba, ya ciro Statement of Account dins...
18/10/2025

Assalam wa Rahmatulaah.

Muna Kiran duk Dan NPower da ba'a Biya shi kudin sa Cikakku ba, ya ciro Statement of Account dinsa na watannin da ya yi aiki, ya hada da Posting later din shi ya ajiye su waje daya ya killace su.

Akwai Sanarwa ta Musamman nan ba da dadewa ba.

Mun gode

Muna yiwa Dan Bello, Abba Hikima da Sauran wadanda suke taimakawa Fatan Alkhairi da samun Nassara.Allah ka fito da Hakki...
17/10/2025

Muna yiwa Dan Bello, Abba Hikima da Sauran wadanda suke taimakawa Fatan Alkhairi da samun Nassara.

Allah ka fito da Hakkin Yan NPower Ameen

15/10/2025

Allah Ya Jikan Dr Allah ya saka Wa Dr da Alkhairi

Ina ma a ce Malaman Izala suna da Tawari'u irin na wannan Dattijon

 Mu yiwa Annabi Salati, Da Harrufan Gwaninta, ya kai cikin zuciyarmu ya cike farin cikin ruhin mu, Adadin da zai cika du...
03/10/2025



Mu yiwa Annabi Salati, Da Harrufan Gwaninta, ya kai cikin zuciyarmu ya cike farin cikin ruhin mu, Adadin da zai cika dukkan bigire da Kididdiga, Annabi Mai Karamci Dan Aminatu Masoyin Allah.

Kyautar Data N500 ga Mutum 10.
Kayi Following Ka yi sharing, kayi comment Da Salatin Annabi wanda ka ke jin dadin yi, ka tura mana Number Opay

Allah Mun gode maka Bisa Falalarka

Kyautar Data 1GB. Zuwa Mutum 100Ka/Ki yi wa Nigeria Fatan Alkhairi, ka/ki yi following Page din mu, ka/Ki yi sharing Pag...
01/10/2025

Kyautar Data 1GB. Zuwa Mutum 100

Ka/Ki yi wa Nigeria Fatan Alkhairi,
ka/ki yi following Page din mu,
ka/Ki yi sharing Page din mu,
ka/Ki tura mana Numberka

Allah Ka Bamu Lafiya da zama Lafiya....... Mu je Maha

Aboki mai irin waɗannan halayen, ka riƙe shi don baka da k**arsa 👇1. Tunda yana da aminci (ba ya cin amana).Aboki na ƙwa...
01/10/2025

Aboki mai irin waɗannan halayen, ka riƙe shi don baka da k**arsa 👇

1. Tunda yana da aminci (ba ya cin amana).
Aboki na ƙwarai zai tsaya da kai a duk wani irin hali, ba zai bar ka ba lokacin da kake cikin wahala ko jarabawa.

2. Domin yana da gaskiya (ba ya yi maka ƙarya ko yaudarar).
Yana faɗa maka gaskiya ko da ba za ta yi maka daɗi ba, saboda yana son alkhairi a gare ka.

3. Don yana da tausayi (yana damuwa da halin da kake ciki).
Idan kana cikin damuwa, zai ji tausayinka da gaske, ya yi ƙoƙarin rage maka zafin raɗaɗin da kake ji, ta hanyar shawarwari ko taimako.

4. Kuma yana da amana (yana iya ɓoye sirrinka).
Duk abin da ka gaya masa a matsayin sirri, ba zai fallasa shi ga wani ba ko bayan kun samu rashin jituwa.

5. Kuma yana ba ka shawara ta gari (yana ba ka shawara mai amfani).
Idan kana neman shawara, ba zai ruɗe ka ba, zai gaya maka abin da zai taimaka maka a rayuwa.

6. Kuma mai girmamawa ne (yana girmama ka da ma iyalanka).
Ba ya wulaƙanta ka, ko ya yi maka magana da raini; yana ganin darajarka da mutuncinka.

7. Yana yi maka taimako (yana tare da kai a farin ciki da baƙin ciki).
A lokacin farin ciki, yana taya ka murna; a lokacin baƙin ciki, yana tallafa maka da duk abin da yake iyawa.

8. Sannan yana da haƙuri (ba ya saurin fushi da kai).
Idan ka yi kuskure, ba ya yin hanzari ya tsane ka, sai dai ya yi haƙuri ya fahimce ka.

9. Sannan yana yi maka nasiha (yana tunasar da kai lokacin da kake aikata kuskure).
Yana gyara ka ta hanyar ladabi da hikima, ba wai yana kallon ka har ka je ka lalace ba.

10. Ga nuna ƙauna (yana nuna maka ƙauna da kulawa ba tare da son kai ba).
Aboki na gaskiya yana nuna ƙaunarsa gare ka ba saboda abin da yake samu daga wurinka ba, sai domin soyayya ta gaskiya.

11. Yana kare mutuncinka a bayanka.
Idan aka zage ka ko aka ɓata maka suna, shi zai tsaya ya kare ka ko da kai ba ka nan, ya nuna darajarka ga mutane.

Shi yasa na ce, ba ka da k**arsa.

Barde Usman
30 September, 2025

GAME DA KARATUN SHEIKH NAZIFI ALKARMAWY (H).Wato wani abu ne da ake cewa, basira ta ƙarewa kare ya koma tunkuyi, sun ɗau...
01/10/2025

GAME DA KARATUN SHEIKH NAZIFI ALKARMAWY (H).

Wato wani abu ne da ake cewa, basira ta ƙarewa kare ya koma tunkuyi, sun ɗauko jerin gwanon ababe har guda takwas na yaƙar tunani da kawar da hankula, amma sun ga har yanzu al'umma bata gafalaba ga barin turbar kira dan tabbatar da ɗaukar mataki a kan Lawandi, shi ne s**a dire domin su ɓadda sawu su Shubhantar da abinda s**a jahilta domin fito da wata ma'ana da suke son sana'antawa a tunanin wawaye duk dan tseratar da lawandi.

Sheikh Karmawi (H) yace: ANNABI (S.A.W) na tajalli ga (Rakumi, Jagora k**ar wani Shehi) sunce hakan ɓatancine, sai kuma gashi ALLAH da kansa yana faɗin yayi tajalli har ga halittarsa dutse: فلما تجلى ربه للجبل جعله دكا وخر موسى صعقا , Mala'iku suna Tajalli ga Sahabbai da wata siffa ta Matafiya, ko Siffar wasu Sahabban (Bukhari Hadisi na 50, Bukhari Hadisi na 3768, Muslim Hadisi na 177 ).

To idan ALLAH zai Tajalli ga Dutse hakan bai zamo Ɓatanci ba, Mala'aiku na Tajalli da Siffar wasu daga Sahabbai ko Matafiya hakan bai zamo Ɓatanci ba, to Yaushe dan ANNABI (S.A.W) yayi tajalli da Siffar wata Halitta ko wani Bawan ALLAH hakan zai zamo Ɓatanci, Tajalli baya nufin zamowar abin tajalli zuwa matsayin abinda ya bayyana tattare dashi.

ALLAH YA GANAR DA WAƊANNAN BEBAYEN, KUMA LALLAI BABU ABINDA ZAI KAWAR DA HANKULAN AL'UMMA A KAN WANNAN ABU DA AKE KAI NA KIRA A ƊAUKI MATAKI BISA ƁATANCIN DA MALAMINKU YAYI.

ALHAMDULILLAH.

Muhammad Usman Gashua ✍️

Tsire da Balangu labarin wuta sukeji.Munafuki shine zai gaya musu bala'in wuta Idan bai dena Munafunci ba. Allah ka raba...
30/09/2025

Tsire da Balangu labarin wuta sukeji.
Munafuki shine zai gaya musu bala'in wuta Idan bai dena Munafunci ba. Allah ka rabamu da Munafunci..

Yanzu Yanzu: Gwamna Abba ya kaddamar da shirin tallafawa matasa, an dauki sama da mutum 5,000 a tashin farko.Kowane mata...
30/09/2025

Yanzu Yanzu: Gwamna Abba ya kaddamar da shirin tallafawa matasa, an dauki sama da mutum 5,000 a tashin farko.

Kowane matashi daga ciki zai samu tallafin N150,000 domin ya k**a sana'a ko ya kara jari a Kano.z

DA DUMI-DUMI: Kun dai ji ko!An bayyana cewa daga watan Janairu, shekarar 2026, mata da maza masu yin karuwanci ko 'runs'...
30/09/2025

DA DUMI-DUMI: Kun dai ji ko!

An bayyana cewa daga watan Janairu, shekarar 2026, mata da maza masu yin karuwanci ko 'runs' a Najeriya za a fara karɓar haraji daga gare su.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnati na shirin sanya wannan doka ne domin samun karin kudaden shiga, duk da cewa wannan aiki bai dace da al’ada da addininmu ba.

Wannan mataki ya jawo cece-kuce a tsakanin ‘yan Najeriya, inda wasu ke ganin ba daidai bane gwamnati ta amince ta rika karɓar haraji daga ayyukan da al’umma ke ganin haramun.

👉 Wannan batu yana da nauyi sosai, me kuke gani? Ya dace gwamnati ta daina karɓar irin wannan haraji ko kuwa ta ci gaba da aiwatar da shi?

Address

Sokoto Road
Kano
0000

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 10:00 - 16:00
18:00 - 19:00

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Npower Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share