13/05/2026
1) Bazai iya zuwa Villa ya gana da shugaban kasa ba—— Sai gashi yaje.
2) Bazai Iya barin NNPP ba—— Sai Gashi ya barta.
3) APC bazasu karbeshi ba sunce sai yazo da kwankwaso ———— Sai gashi sun karbeshi Hannu bibiyu
4) Bazasu Bashi Jamiyya ba———- Sai gashi Ya karbi 60%
5) Ganduje bazai yarda su Bashi Jagoranci ba———- sai Gashi Sunce shine Jagoransu yadda ya dama haka za’a sha.
6) Bazasu bashi takara ba ————- Sai gashi duk Yan takarar sun Janye sunyi masa Mubaya’a.
7) Saidai ya shiga primary election ————- sai Gashi duk yan takarar sun Janye sunce basu yarda wani yayi takara dashi ba.
8.) Tunda ya shiga APC yanzu zai Daina Ayyukan da yakeyi a gari ya koma Rabon Kudi————- Sai gashi Kullum sabbin Ayyuka ake sake fitowa dasu.
9) Bazai Iya Fitowa ya shiga Mutane ba saboda baa sonsa——— sai gashi duk inda yaje sai son Barka.
10)Bazai Iya zaben Deputy Gwamna ba saboda rikici, duk wanda ya dauka matsala ne, Jamiyyar zata lalace————- Sai gashi anyi lami lafiya, Harda Sanata Barau a Gurin Rantsuwar Murtala sule Garo
11)Ai bazai iya yin sulhun Yan takara ba———— Sai gashi anyi Lafiya
12) Ai duk wanda bai samu takara ba zai fice, Jamiyyar ta tarwatse ———- Sai gashi anyi sulhun Takara lafiya an gama Lafiya.
13) Bazai Iya sulhunta Rikicin ATM Gwarzo da Barau ba———— Sai Gashi Jiya anyi sulhu kowa na Murna.
Yanzu H.E Engr. Abba Kabir Yusuf Shine Maradonan Siyasar Jihar kano, Kowa da lokacinsa, Yanzu Allah shi ya Arawa dama kuyi Hakuri ku sallama.
Iya wannan Yakamata yan NDC su gane duk tunaninsu akan Mai girma Gwamna Alhaji Abba kabir Yusuf ba daidai bane.
Allah ne yace ya karrama Dan Adam, Saboda haka ku daina tunanin Kukadai ne ko kuma Jagora ne kawai ya iya, Allah yana bawa kowa Basira da Hikima da Nasara.
14) Zakuce Bazai Iya cin zabe ba———
Allah zai bashi Nasara duba da Irin Ayyukan Alkairi da yakewa Kanawa, Inada Tabbacin Zasu sake zabarsa.
Abba Kafin Allah Ne
AYRC