Mal. Aminu S.Gayan

Mal. Aminu S.Gayan Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mal. Aminu S.Gayan, Kano.

Tsohon gwamnan jihar Bauchi a mulkin soja Brig. Gen. Abu Ali, ya rasu a ranar 24 ga watan Nuwamnabn 2025 a fadarsa da ke...
24/11/2025

Tsohon gwamnan jihar Bauchi a mulkin soja Brig. Gen. Abu Ali, ya rasu a ranar 24 ga watan Nuwamnabn 2025 a fadarsa da ke Bassa-Nge da ke Lokoja a jihar Kogi.

Marigayin ya yi mulki daga Satumban shekarar 1990 zuwa Janairu 1992, a zamanin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Ya mika mulki a watan Janairun 1992 ga zababben gwamna Dahiru Mohammed bayan shirya zabe.

Kuma shi ne mahaifin Marigayi Lt. Col. Mohammed Abu Ali wanda mayakan Boko s**a kashe a shekarar 2016.

Sen. Abdul'aziz Yari ne a duke tareda Alh. Bello Mutawallen Maradun wanda Minister ne a Nigeria, sun kasane tsaffin Gwam...
24/11/2025

Sen. Abdul'aziz Yari ne a duke tareda Alh. Bello Mutawallen Maradun wanda Minister ne a Nigeria, sun kasane tsaffin Gwamnonin Jihar Zamfara

Hanya mai hadin zumuntar dole!
13/11/2025

Hanya mai hadin zumuntar dole!

Jami'an yan sanda basuda hurumin raka wike rigima ko ƙwacen filiDuk jami'in da yasamu wata matsala ko rauni, shi zai kul...
13/11/2025

Jami'an yan sanda basuda hurumin raka wike rigima ko ƙwacen fili

Duk jami'in da yasamu wata matsala ko rauni, shi zai kula da kansa.

Inspector General Of Police (Kayode Adeolu Egbetokun) ya gargaɗi jami'an yan sandan dake yawo tare da ministan Abuja (Nyesom Wike).

Ba za'a taɓa shawo kan matsalar tsaro ba a Nigeria, saboda ita ce hanyar samun arziƙin wasu manyan mutane a ƙasar nanBaz...
10/11/2025

Ba za'a taɓa shawo kan matsalar tsaro ba a Nigeria, saboda ita ce hanyar samun arziƙin wasu manyan mutane a ƙasar nan

Bazasu bari a daƙile musu hanyar cin abinci ba

Cewar General TY Ɗanjuma
--------------------

Matsalar tsaro a ƙasar nan, tana samun goyon bayan wasu azzalumai dagacikin jami'an tsaro, shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, malamman addini musulmi da kirista

Saboda haka ba zasu taɓa bari a zauna lafiya ba, saboda nan ne abincinsu yake.
--------------------

Nigeria munada gwarazan jami'an tsaro da makamai irin na zamani, da jiragen yaƙi da motocin yaƙi, da na'urorin bincike da jirage marar matuƙi wanda ba'asan adadinsu ba

Kowace shekara gwamnatin Nigeria na ware kuɗi tiriliyan (7) a ɓangaren tsaro

Kawai haryanzu ba'a sanya ranar kawo ƙarshen ta'addanci bane.

10/11/2025

Ga matakan da zakubi wajen rage tumbi 👇

SIYASA: Ɗan Sheikh Dahiru Bauchi ya ayyana shiga takarar gwamna a zaben 2027.Naziru Sheikh Dahiru Bauchi ya ce ya nemi i...
09/11/2025

SIYASA: Ɗan Sheikh Dahiru Bauchi ya ayyana shiga takarar gwamna a zaben 2027.

Naziru Sheikh Dahiru Bauchi ya ce ya nemi izinin Mánzòn Alláh SAW kafin yanke hukuncin fitowa takarar Gwamnan.

BA'A YIWA MACE MAI JUNA ALLURAR GENTAMICIN ⛔⛔⛔‎‎Wannan magani da kuke gani wato gentamicin dan Allah ayi hankali dashi s...
08/11/2025

BA'A YIWA MACE MAI JUNA ALLURAR GENTAMICIN ⛔⛔⛔

‎Wannan magani da kuke gani wato gentamicin dan Allah ayi hankali dashi sosai domin muna raina shi wata kila saboda rashin sanin amfanin sa da kuma irin illolin da yake haifar wa

‎Gentamicin tana daya daga cikin 'Antibiotics' a ajin ( Aminoglycoside), suna kashe kwayoyin bakteriya gaba daya wato ( bactericidal) neh, suna attacking na bacterial protein synthesis, sannan suna aiki kadai akan gram negative bacteria.

‎Wannan maganin ba'a yarda mace mai juna biyu tayi amfani dashi ba, saboda lokacin juna biyu idan akayi amfani dashi yakan yi crossing through placenta, sai ya shiga jinin yaron yaje ya taru a cikin cochlea da kuma vestibular na kunne wanda hakan ya kan jawo yaro ya zama baya ji ( hearing loss) . Yin amfani dashi ga mai juna biyu zai iya jawowa yaron ya zama kurma na dindindin.


‎Sannan wannan maganin yana da illa sosai ga hanta domin yakan iya lalata tah wato ( Nephrotoxocity), sannan yakan haifar hajijiya ( vertigo/diziness)

‎Abinda ya kamata ka sani game da Gentamicin 👇👇👇

‎1 baya aiki akan kwayar virus, fungal infection, parasite

‎2 ba'a son mace mai ciki tayi amfani dashi saboda ototoxicity

‎3 ba'a son amfani da shi tare da NSAID kamar diclofenac, ibuprofen, piroxicam da sauran su, da furusomide

‎4 ba'a son hada tah da wani maganin/ zuba tah a cikin ruwa ( drips)

‎5 ba'a son tsofaffi suna yawan amfani da ita

‎7 tana jawo kurmancewa ( hearing loss) musamman ga yaran da suke mahaifa, tana lalata koda ( Nephrotoxocity ), da kuma rashin daidaito ( balance)

‎8 maganin nan ka iya haifar da hajijiya ( vertigo), tashin zuciya, amai

‎Manya manyan side effects din sa sune
‎👉 ototoxicity
‎👉 Nephrotoxocity


‎Ayi kokari a kiyaye bawa mace mai juna biyu gentamicin injection saboda gudun matsala.

‎GENTAMICIN INJECTION ARE CONTRAINDICATED IN PREGNANCY ⛔⛔


Marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero daga dama, daga hagu marigayi sarkin Hadejia Alhaji Abubakar Maje Haruna. A lokac...
03/11/2025

Marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero daga dama, daga hagu marigayi sarkin Hadejia Alhaji Abubakar Maje Haruna. A lokacin da su ke jiran zuwan marigayi firaministan Burtaniya, Margaret Thatcher a ranar 8 ga watan Janairun 1988, in da ta ziyarci Legas da Kano.

Tsohuwar Firayim Ministan Burtaniya Margaret Thatcher ta ziyarci Kano, Najeriya, a watan Janairun 1988, a wani bangare na rangadin da ta yi a kasashen Afirka.

A ziyarar da ta kai Kano, ta kasance bakuwar Sarki, kuma an tarbe ta da dimbin jama’a sabanin zanga-zangar da ta fuskanta a Legas, babban birnin Najeriya a lokacin. An gudanar da hawan daba wanda ya kunshi dubban mahaya domin karrama ta.

Zuwan ta Kano wani lamari ne da ya yi fice, domin ita da mijinta, Denis Thatcher, jirgin su ya sami matsala wajen sauka, saboda tsananin hazo a lokacin.

Mutane dayawa suna mutuwa sanadiyyar nutsewar mota acikin ruwaIdan motarka ta nutse acikin ruwa, ga hanya mafi sauƙi da ...
03/11/2025

Mutane dayawa suna mutuwa sanadiyyar nutsewar mota acikin ruwa

Idan motarka ta nutse acikin ruwa, ga hanya mafi sauƙi da zaka cece rayuwarka

1. Kar kayi yunƙurin buɗe ƙofa, nauyin ruwa bazai bari ƙofar ya buɗe ba

2. Kar ka sauke gilashi, bazai sauke ba acikin ruwa

3. Idan kayi amfani da hannu ko ƙafa domin fasa gilashi, bazaka iya ba.

Hanya mafi sauƙi shine:

Ka cire kan kujera “Headrest” kayi amfani da wannan ƙarfen ka fasa gilashin baya domin anan zaka samu babbar ƙofar fita kaitsaye.

⚠️ Gilashin gaba yanada wahalar fashewa, bayan haka idan mutum ya fasa gilan gaba motar zatayi saurin nutsewa acikin ruwa saboda nauyin inji.

Alhassan Mai Lafia

ZAA DENA AMFANI DA DOLLAR A SIYEN TICKETS A NIGERIA....Gwamnatin Nigeria tana duba yiyuwar dakatar da siyen tikitin jira...
03/11/2025

ZAA DENA AMFANI DA DOLLAR A SIYEN TICKETS A NIGERIA....

Gwamnatin Nigeria tana duba yiyuwar dakatar da siyen tikitin jiragen saman kasashen waje da akeyi da Dollar...

A yanzu kusan duk Tickets da ake siya na kamfanonin jiragen sama da suke jigilar fasinjojin Nigeria suna siyar da Tickets dinsu ne da Dollar maimakon Naira wanda hakan ke karawa Dollar daraja a Nigeria kuma yake rage darajar Naira, sai dai a iya cewa hakan na gaf da zama tarihi domin gwamnatin Nigeria tace hakan ba zai cigaba da faruwa a kasarta ba..

Kamfanonin jiragen sama irinsu British Airway, Lufthansa da Emirates suna siyar da Tickets dinsu da Dollar maimakon Naira duk da cewa fasinjojin Nigeria suke dauka a cikin Nigeria, akwai sauran kamfanoni masu yawa da suma suke siyar da Tickets da Dollar maimakon Naira ..

Gwamnati tace dole ne ta kawo tsare tsaren da zasu durkusar da Dollar tare da hanata cigaba da hauhawa....

Yadda Dolar take a matsayin kudi haka ita ma Naira take don haka dole ne a mutumta Naira a cikin Nigeria, ba zai yiyu aki amfami da Naira a Amurka sannan ace zaa dinga amfani da Dollar a Nigeria....

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mal. Aminu S.Gayan posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share