Siyasar Kano Update

Siyasar Kano Update Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Siyasar Kano Update, Political organisation, Yalwa Unguwar Kulkul, Kano.
(6)

Asphalt overlay from Dakata Bus-Stop to Kwanar Dakata.  .
02/06/2026

Asphalt overlay from Dakata Bus-Stop to Kwanar Dakata.

.

01/06/2026

Kwamishinan da ke rikon ma'aikatar ruwan na Kano kuma kwamishinan ma'aikatar muhalli Dakta Dahir Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan, yayin wata ziyarar duba aiki da ya kai, a matattarar ruwa da le Goron dutse.

Ya ce sakamakon korafe-korafen da al'ummar Kano ke Yi na rashin ruea ya sa gwamnan Kanon injiniya Abba Kabir Yusuf ya Tashi tsaye wajan ganin an magance matsalar.

Dr Dahir ya Kuma ce akwai matattarar ruwan da an kai shekara talatin ba a zuba mata ruwa ko Lita daya ba a Goron Dutsen. A don haka ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajan ganin an magance matsalar ruwan a Yan watannin nan.

Idan ba za a manta ba dai tun a kwanakin baya ne gwamnatin Kano ta kaddamar da shirin ta na gyare-gyare a bangaren ruwan wanda zai ci Sama da biliyan sha daya.

Gwamna Yusuf ya amince da kashe Naira biliyan 21.89 don gyaran matatun ruwa na Kano Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf...
31/05/2026

Gwamna Yusuf ya amince da kashe Naira biliyan 21.89 don gyaran matatun ruwa na Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kashe Naira biliyan 21.89 domin gyarawa da inganta matatun ruwa na Challawa da Tamburawa, a wani yunkuri na magance matsalar karancin ruwa da ake fuskanta a fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin gudanar da Hawan Nasarawa a Kano, inda ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar warware matsalar samar da ruwa mai tsafta da ake fama da ita.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an ce kudin da aka amince da su sun hada da Naira biliyan 9.9 domin gyaran Matatar Ruwan Challawa da kuma Naira biliyan 11.99 domin inganta Matatar Ruwan Tamburawa.

Yusuf ya ce ayyukan za su tabbatar da samar da ruwan famfo cikin sauki da dorewa ga mazauna birnin Kano da yankunan da ke kewaye da shi.

Ya bayyana samar da ruwa mai tsafta a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba, yana mai tabbatar da cewa za a dawo da ingantaccen tsarin samar da ruwa kafin karshen shekarar 2027.

A cewarsa, gyarawa da inganta wadannan manyan cibiyoyin ruwa za su kara yawan samar da ruwa tare da inganta rabonsa a sassan jihar.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a muhimman ayyukan more rayuwa domin inganta rayuwar al’umma.

Haka kuma, ya sanar da shirin gwamnatin jihar na samar wa manoma taki a farashi mai rahusa a wannan daminar, domin bunkasa noma da kuma karfafa samar da abinci.

Yusuf ya ce matakin zai taimaka wajen rage nauyin da ke kan manoma, kara yawan amfanin gona da kuma karfafa bangaren noma a jihar.

Kafin 12 na rana Hon. Muhammad MD Hassan yayi nasara a Karamar hukumar Nasarawa Insha Allah.Idan Allah yabawa MD nasara ...
26/05/2026

Kafin 12 na rana Hon. Muhammad MD Hassan yayi nasara a Karamar hukumar Nasarawa Insha Allah.

Idan Allah yabawa MD nasara za,a taimaki al’uma kwarai da gaske, za kuma a kawo cigaba a fanni daban daban, Fatan mu Allah ya bashi nasara.

Khatimu Kulkul
26 May 2026.

26/05/2026

Allah mai zamani 😂

PDP kuma Malam?

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo Ya Tallafa wa Marayun Garo da Buhunan Shinkafa 50 da Bajimi Domin Bikin SallahShugaban ƙar...
25/05/2026

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo Ya Tallafa wa Marayun Garo da Buhunan Shinkafa 50 da Bajimi Domin Bikin Sallah

Shugaban ƙaramar hukumar Kabo, Hon. Lawan Najume Kabo , ya bai wa marayun garin Garo da kewaye tallafin buhunan shinkafa hamsin tare da bajimin sa domin gudanar da bikin sallah cikin farin ciki da walwala.

Tallafin wanda aka bayyana a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin shugaban wajen tallafawa marasa galihu da marayu, ya samu karɓuwa da yabo daga al’ummar yankin da kuma kwamitin tallafawa marayun.

Shugaban kwamitin tallafawa marayun tare da sauran mambobin kwamitin sun bayyana jin daɗinsu bisa wannan karamci, inda s**a ce tallafin zai taimaka matuƙa wajen sanya marayun su ma gudanar da shagulgulan sallah cikin annashuwa kamar sauran al’umma.

Sun ƙara da cewa irin wannan taimako na nuna kulawa, tausayi da ƙaunar da Hon. Lawan Najume Kabo ke yi wa marayu da masu ƙaramin ƙarfi a cikin al’umma.

Al’ummar yankin sun bayyana aikin a matsayin abin yabawa kuma abin koyi ga sauran shugabanni da masu hannu da shuni, musamman duba da irin muhimmancin kula da marayu da addinin Musulunci ya tanada.

An kuma yi addu’ar ALLAH Maɗaukakin Sarki Ya saka wa shugaban ƙaramar hukumar da mafificin alkhairi, Ya ƙara masa lafiya, arziki da nasara tare da ci gaba da ba shi ikon yi wa al’umma hidima yadda ya kamata.

Karamar Hukumar Kano Municipal, Kujerar Majalisar tarayya Engr Koki Sagir ko Dr Yusuf Kofarmata ?Ku bayyana mana a Comme...
25/05/2026

Karamar Hukumar Kano Municipal, Kujerar Majalisar tarayya Engr Koki Sagir ko Dr Yusuf Kofarmata ?

Ku bayyana mana a Comment section.

Mun yi watsi da bukatar Pantami ta neman shiga PDP - Masu neman tikitin Gwamnan jihar Gombe a PDP‘Yan takarar gwamna hud...
24/05/2026

Mun yi watsi da bukatar Pantami ta neman shiga PDP - Masu neman tikitin Gwamnan jihar Gombe a PDP

‘Yan takarar gwamna hudu na jam’iyyar PDP a jihar Gombe sun yi zargin cewa ana kokarin shigar da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami cikin jam’iyyar domin ya shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar.

A cikin wata sanarwar bayan taron gaggawa da s**a gudanar ranar Lahadi a Gombe, ‘yan takarar da sun hada da Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki, Hon. Usman Aliyu Garry da kuma Mrs Monica Kaltho.

Sun bayyana cewa doka ba ta amince mutum ya sauya jam’iyya sannan ya sake shiga irin wannan tsarin zabe bayan an riga an kada kuri’u tare da kirga masa a wata jam’iyya ba kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

‘Yan takarar sun ce suna maraba da duk wani mai kyakkyawar manufa da zai shiga PDP, amma sun nuna adawarsu ga duk wani yunkuri na shigar da mutumin da ya riga ya fafata a zaben fidda gwani na wata jam’iyya daban.

The All Progressives Congress (APC) has announced Monday, 25th May, 2026, as the deadline for the submission of Governor...
24/05/2026

The All Progressives Congress (APC) has announced Monday, 25th May, 2026, as the deadline for the submission of Governorship, Senatorial, House of Representatives, and State Assembly Primary Election Reports and Result Sheets.

Submission of Legislative Bye-Election Results/Reports will commence on Saturday, 30th May, 2026.

All Committees are directed to ensure timely and proper submission of all required documents.

APC..Progress.

An kwarfe Kabiru Gaya 😂
24/05/2026

An kwarfe Kabiru Gaya 😂

Address

Yalwa Unguwar Kulkul
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Siyasar Kano Update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Siyasar Kano Update:

Share