17/05/2026
Ya ku al’ummar Kano Central, lokaci ya yi da za mu zabi shugabanci na gaskiya, shugabanci mai tausayi da kishin jama’a. Salmanu Muhammad (Ya Malam) ya nuna cewa yana tare da talaka a kowanne lokaci. Yana sauraron koke-koken jama’a, yana shiga cikin harkokin cigaban matasa, kuma yana da manufofi masu anfani wadanda za su kawo sauyi mai ma’ana a rayuwar al’umma. Wannan takara tasa ba ta son kai ba ce, takara ce ta hadin kai, cigaba da kuma makomar Kano Central.