Tinubu/Abba Youth Support Organizations Kano State

Tinubu/Abba Youth Support Organizations Kano State Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Tinubu/Abba Youth Support Organizations Kano State, Political organisation, Kano.

31/03/2026

Abba kafin ALLAH.
ALLAH dayaka jiya shi zaibaka gobe🤲

ABIN LURA A SIYASAR WANNAN LOKACI.....✍️Daga Munzali shehu Gwamnati APC, ADC, NNPP, PDP Kusan duk abu dayane, mutanen ci...
31/03/2026

ABIN LURA A SIYASAR WANNAN LOKACI.....

✍️Daga Munzali shehu Gwamnati

APC, ADC, NNPP, PDP Kusan duk abu dayane, mutanen cikin wadancen Haruffan sune bukatarsu bata biya ba s**a dawo cikin wadannan Haruffan, amma duk dayane.

Saboda haka musani Shugabanni nagari bawai acikin jam'iyya guda suke gaba daya ba.
Akowacce jam'iyya ana iya samun nagari, hakama ana iya samun akasin haka.
Kawai kazabi wanda kake ganin yayi dai dai da ra'ayinka,ko bukatarka,domin idanma kazagi wadancen ko kagama hakilo kana kalubantar waccen jam'iyyar tofa watarana sai awayi gari kaga ansake(Vise versa ) ko haduwa a karkashin inuwa daya kamar yadda yake faruwa a yanzu

Addu'armu kawai ALLAH yabamu shugabanni masu kishin al'umma🤲.
Yakamata yanzu adaina rudar mutane da jam'iyyar suwane sune nagari, wadancen kuma tunda basa tare da suwane bamutanen kirki bane.

Menene Ra'ayinku danganeda wannan sauye saiyen dake faruwa🤔

30/03/2026

Wassulhu Khair....

Malam Nasir El-Rufai, muna mika Ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarka.
Allah yajikanta yasa aljannace makomarta😭🤲.

Wannan abinda yayi haka akeson Mumuni yazama Mai yafiya,kuma mai hakuri

"Ya zama dole mu taya Madugu da addu'a saboda yau ya ci amanar kan sa da kan sa, domin shi ma ya fita daga jam'iyyar NNP...
29/03/2026

"Ya zama dole mu taya Madugu da addu'a saboda yau ya ci amanar kan sa da kan sa, domin shi ma ya fita daga jam'iyyar NNPP."

Kaɗan kenan daga cikin jerin saƙonnin da D.G. Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

YANZU YANZU: gomnan Jahar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya Bawa yan midiyarsa Umarnin akan maida Raddi ga Abokan Adawarsu Y...
29/03/2026

YANZU YANZU: gomnan Jahar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya Bawa yan midiyarsa Umarnin akan maida Raddi ga Abokan Adawarsu Yan Kwankwasiyya

yanzu yanzu Governor Abba kabir Yusuf ya gana da Tsofaffin yanmajalisar Tarayya na Jam'iyyar Apc
29/03/2026

yanzu yanzu Governor Abba kabir Yusuf ya gana da Tsofaffin yanmajalisar Tarayya na Jam'iyyar Apc

Yadda jagororin Jam’iyyar APC na ƙasa s**a halarci babban taron jam’iyyar a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
28/03/2026

Yadda jagororin Jam’iyyar APC na ƙasa s**a halarci babban taron jam’iyyar a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Alhaji Shehu Wada Sagagi daga mukaminsa na Kwamishinan Kasuwanci da Masan...
25/03/2026

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Alhaji Shehu Wada Sagagi daga mukaminsa na Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu na jihar.

Siyasarmu TV ta rawaito a sanarwar da daraktan yada labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis 26 ga Maris 2026, ya ce an umarci tsohon kwamishinan da ya mika ragamar ma’aikatar ga daraktan kasuwanci nan take.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya gode wa Sagagi bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake kan mukamin, musamman a fannoni na siyasa da addini da kuma kananan da matsakaitan sana’o’i.

Ta kara da cewa matakin na daga cikin gyare-gyaren da gwamnatin ke yi domin inganta tafiyar da ayyuka da tabbatar da ci gaba mai dorewa a Jihar Kano.

Me za ku ce?.

Gwamna Abba na Shirin Rushe Shugabannin Kananan Hukumomi 44 a Kano.Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba K...
25/03/2026

Gwamna Abba na Shirin Rushe Shugabannin Kananan Hukumomi 44 a Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na duba yiwuwar rushe dukkan shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar.

Majiyoyi sun ce tuni gwamnan ya kammala shirin, inda ake zargin cewa an mikawa Majalisar Dokokin Jihar Kano kudirin da ya shafi wannan mataki domin duba yiwuwar amincewa da shi.

Rahoton ya kara da cewa matakin na cikin wasu tsare-tsaren da gwamnatin ke yi na sake fasalin harkokin gudanarwa a matakin kananan hukumomi.

A halin yanzu, jama’a na jiran ganin ko yaushe wannan batu zai tabbata, tare da yadda majalisar dokokin jihar za ta dauki wannan kudiri.

Ra'ayinku al'ummar kano, Idan wannan mataki ya tabbata, mene ne ra’ayinku kan wannan yunkuri na gwamnatin jihar Kano?

Mai Girma Gwamnan Kano H.E Abba Kabir Yusuf, tare da takwarorin sa gwamnoni najeriya sun halarci bikin karbar gwamnan ji...
25/03/2026

Mai Girma Gwamnan Kano H.E Abba Kabir Yusuf, tare da takwarorin sa gwamnoni najeriya sun halarci bikin karbar gwamnan jihar Zamfara H.E Dauda Lawal, inda Mataimakin shugaban kasar Najeriya H.E Kashim Shettima CON, ya wakilici shugaban kasa a taron.

24 03 2026.

Gwani Haruna Makoɗa na riƙe da ragamar ma'aikatu uku a gwamnatin Jihar Kano bayan wasu sauye-sauye da Gwamna Abba Kabir ...
15/03/2026

Gwani Haruna Makoɗa na riƙe da ragamar ma'aikatu uku a gwamnatin Jihar Kano bayan wasu sauye-sauye da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a cikin majalisar zartarwa.

Tun a baya, a sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa a bayyana Makoɗa, wanda shi ne Kwamishinan Ilimi, zai ci gaba da kula da Ma’aikatar Albarkatun Ruwa bayan murabus din Hon. Umar Haruna Doguwa da aka zaɓa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na Kano.

Haka kuma a yau Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rushe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi tare da haɗa ta da Ma’aikatar Ilimi, wanda hakan ya sanya duka ma’aikatun biyu a ƙarƙashin jagorancin Gwani Haruna Makoɗa.

Me za ku ce?.

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da rushe ma'aikatar ilimi mai zurfi ta jihar, tare da haɗe ayyukan ta d...
15/03/2026

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da rushe ma'aikatar ilimi mai zurfi ta jihar, tare da haɗe ayyukan ta da Ma’aikatar Ilimi, domin ƙarfafa daidaito da hanzarta gyare-gyare a fannin ilimi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Sanarwar ta ce bayan sauyin da gwamnan yayi, sabuwar ma’aikatar za ta ci gaba da aiki da sunan Ma’aikatar Ilimi, inda za'a samar da wani sashen mai kula da ilimi mai zurfi a cikin ma’aikatar domin kula da harkokin manyan makarantu.

Sashen dai zai kasance ƙarƙashin jagorancin babban Sakatare tare da sauran ma’aikata domin tabbatar da gudanar da harkokin manyan makarantu a jihar.

Address

Kano
3002

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tinubu/Abba Youth Support Organizations Kano State posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share