19/06/2022
👉Wannan shi ne Mr. Jonathan Lee, mutumin da ya fi kowa kai ƙara a duniya. Jonathan har mahaifiyarsa ya shigar da ƙara a Kotu, inda ya faɗa ma kotu cewa mahaifiyar ta sa ba ta ba shi kulawa yadda ya kamata ba, a ƙarshe dai Mr. Jonathan ya samu nasara a kan mahaifiyarsa inda ta biya shi $20, 000.
👉Bayan wannan nasara ce Mr. Jonathan ya shigar da amininsa, da maƙocinsa, da wa su daga cikin ƴan uwansa, da budurwarsa, da ƴan sanda, sannan ya shigar da ƙarar wani alƙali, da wani kamfani, ƙarshe har tsohon shugaban Amuruka George Bush ya shigar ƙara kuma duk ya sami nasara, a taƙaice dai ya shigar da ƙara sau dubu biyu da ɗari shida (2600).
👉Daga baya aka sanya sunan Mr. Jonathan Lee, a matsayin wanda ya fi kowa shigar da ƙara a littafin tarihin nan na (World Guinness Book Record), ganin sunansa a cikin wannan tarihi Mr. Jonathan ya shigar da ƙarar (Guinness Book of Record) gaban kotu bisa rubuta rayuwar sa a cikin littafin ba tare da amincewar sa ba, kuma ya samu nasara da kuɗi har $8, 000, 000.
👉Bayan samun wannan nasara ne wani gidan talabijin ya nemi Mr. Jonathan, domin tattaunawa ta musamman, yayin tattaunar da s**a tambaye shi ko mai ya sa yake rayuwa shi kaɗai ba shi da masoyi ko ɗaya? Nan ta ke Mr. Jonathan ya fara dariya ya miƙe tsaye ya fice, ya yiwa kotu tsinke inda ya shigar da ƙarar gidan Talabijin ɗin bisa cin mutuncinsa a kan yi masa tambayoyin da s**a shafi rayuwar sa domin tozarta shi, inda kotu ta ci tarar gidan Talabijin ɗin $50, 000.
Wannan kenan.