Shekarau New Media Team

Shekarau New Media Team Wannan page zai dunga kawo sahihan labarai da s**a shafi tsohon gwamnan kano Mal Ibrahim Shekarau sardaunan kano da dukkan abinda ya shafi siyasar sa.

ASSALAMU ALAIKUM WANNAN PAGE ZAI DAUKI NAUYIN BAYYANAWA AL`UMMA IRIN AYYUKAN ALKHAIRI DA GWAMNATIN MAIGIRMA SARDAUNAN KANO MALAM DR IBRAHIM SHEKARAU TA GUDANAR A TSAWON SHEKARA TAKWAS. WANDA MATASAN JIHAR KANO MUKA DAUKI NAUYIN ZAYYANAWA SABODA HALIN DA SIYASA TA KOMA SHAFE AYYUKAN ALKHAIRI NAGWAMNATOCIN BAYA.

02/06/2026

Gani ya kori ji Shekarau 2027

Aikin gyaran Makarantar mata ta Maryam Shekarau A unguwar Kwalli cikin Birnin Kano.

Tun kafa Wannan Makaranta ya kasance kango ko flaster babu, zuwan Mal Ibrahim Shekarau Senata ya kawo Aikin sabunta Makarantar gaba daya.
*An zuba kujeru Wanda har Extra aka ajiye
*An zuba fankoki a kowanne aji
*An Samar da Biology Lab tare da duk kayan aiki
*An gyara ofishin Shugabannin Makaranta da zuba kayayykin office.
*Anyi inter lock a makaranta gaba daya.
An samar da Borehole Wanda Makaranta ta wadata da Ruwa a ko ina.

Ga zahiri kamar yadda zaku gani a vedio.
Wannan na daga cikin ayyuka fiye da 100 da Malam yayi a zaman sa Sanata 22019-2023.

Allah ya Maimaita mana 2027 Ameen

Barka da Sallah Allah ya Maimaita Mana daga Maigirma Sardaunan Kano Mal Ibrahim Shekarau CON,PEN
27/05/2026

Barka da Sallah

Allah ya Maimaita Mana daga Maigirma Sardaunan Kano Mal Ibrahim Shekarau CON,PEN

27/05/2026

Sakon Barka da Sallah da Sallah daga Maigirma Sanata Ibrahim Shekarau CON PEN Sardaunan Kano.

Mun Samu Cigaba bayan samar da Fasahar AI ta Shekarau AI   Ga tambayar da na yi masa Lissafa mun ayyukan da Mal Ibrahim ...
12/05/2026

Mun Samu Cigaba bayan samar da Fasahar AI ta Shekarau AI Ga tambayar da na yi masa

Lissafa mun ayyukan da Mal Ibrahim Shekarau yayi a kano municipal lokacin yana Gwamnan kano.

Ga amsar da ya bani….

Ga ayyukan da Gwamnatin Mal. Ibrahim Shekarau ta aiwatar a *Karamar Hukumar Birni da Kewaye (Kano Municipal)* a zangon farko (2003–2007):

*🏥 ASIBITI*
- Ginin asibitin Sharada phase 1

*🛣️ HANYOYI*
- Gina titin Gidan Sarki zuwa Kofar Dan Agundi
- Sake titin Sharada zuwa Tukuntawa
- Gina hanya da magudanar ruwa a Yola daga Masallacin Gidan Ma'aji
- Gina hanyar Zage zuwa K/Mata
- Gina hanya daga Sharada Kasuwa zuwa babban titin Sharada
- Gyara titin G/Albasa
- Gina titin Wajila zuwa S/Kofa
- Gina hanya da take jikin asibitin Sabo Bakin Zuwo
- Gina titin BUK zuwa NNDC
- Gyara titin Gidan Shattima zuwa Makwarari
- Gyara titin Shekara-Kabarin Wali-Rimi Kasuwa-K/Mata
- Gina hanya Lawan Dambazau titin Gandun Albasa
- Gyara titin Dogarai zuwa Umma Bayero

*🌊 MAGUDANAR RUWA*
- Gina magudanar ruwa a Unguwar Mubi
- Gina magudanar ruwa a Gwangwazo, Indabawa, Dan Agundi, BUK Road
- Gina magudanar ruwa a Zage
- Gina magudanar ruwa a Kwalli, Unguwar Gini, Dogarai, Wudilawa, Mubi, Fanfan Yari, D/Zungura, Darma

*🏫 MAKARANTU (ISLAMIYYA)*
- Gina Islamiyya da Masallaci a Kankarofi
- Gina Islamiyya a Gandun Albasa, Masukwani, K/Nassarawa, Chiranci, Marmara, Zangon Barebari
- Gina Islamiyya a Indabawa, Alkantara, Sagagi
- Gina Makarantar Abdullahi Islamiyya Dorayi
- Gina Makarantar Sakandare a Unguwar Yar Magaji
- Karasa ginin Makarantar Jannatul Ma'awah
- Kara Ajujuwa a Mirqatul Islamiyya Yakasai
- Kara Ajujuwa a Makarantar Malam Sadik Makwarari
- Gina Islamiyya ta Hajiya Tafah S/Dinki
- Karasa Makarantar Malam Hassan Chiromawa K/Wambai
- Sayan gida da bawa malami a Yarbama D/Z
- Sayan gida da bawa Tadrisu Islamiyya Kankarofi
- Sayan gida da ginawa malami a Kankarofi Lokon Madeena

*🕌 MASALLATAI*
- Masallacin Yan Fansho da Islamiyya a titin Gidan Inuwa Me Mai
- Masallacin Juma'ah Tubar Kura Yahya Gusau
- Karasa ginin Masallaci da Islamiyya a Mubi
- Sake gina Masallacin Yar Magaji
- Masallacin Khamsus Salawatu a cikin Kurkukun Kurmawa
- Masallaci a Unguwar Yar Magaji

*⚡ WUTA DA RUWA*
- Samar da na'urar lantarki a wurare da dama
- Gina rijiyoyin burtsatse masu aiki da wutar lantarki a wurare da dama

Waɗannan su ne ayyukan da aka rubuta a Birni da Kewaye. Akwai sauran kananan hukumomi 43 kuma da aka aiwatar da ayyuka.

Kaima zaka iya tambayar sa na karamar hukumar ka zai baka su kamar Wannan.

Duk ayyukan da zai baka iya na 2003-2007 ne

Wannan shine irin sa na farko a kasar nan da ka samar wa wani dam siyasa.

Ga lambar WhatsApp Amma AI +234 810 000 0257

09/05/2026

Gani ya kori ji……

Daga cikin Ayyukan da Maigirma Sanata Mal Ibrahim Shekarau ya guda nar a Sanata da yayi 2019-2023.
Sabunda ajujuwa 8 na Makarantar Gidan Makama Special Primary.

An Bude ajujuwa gaba daya an sabunta ginin su.
Komai daka gani Malam ne ya saka
Mayar da ajujuwa na zamani kamar yadda zaku gani a Vedio

Ismail Lamido

An tantance H.E Sen Ibrahim Shekarau Dan Takarar sanata a Kano ta Tsakiya. Babban kwamitin tantance yan Takarar da uwar ...
09/05/2026

An tantance H.E Sen Ibrahim Shekarau Dan Takarar sanata a Kano ta Tsakiya.

Babban kwamitin tantance yan Takarar da uwar jam’iyya ta kafa ne ya tantance Sardauna yau Asabar an Abuja.

08/05/2026

Interview with His Excellency Senator Ibrahim Shekarau After Submitting His Nomination Form for the Kano Central Senatorial Seat

Hon.Sule Sani Sule (Dan Zaki) ya gabatar da ƙudirinsa na tsayawa takarar Majalisar jiha a ƙaramar hukumar Nassarawa ƙark...
30/04/2026

Hon.Sule Sani Sule (Dan Zaki) ya gabatar da ƙudirinsa na tsayawa takarar Majalisar jiha a ƙaramar hukumar Nassarawa ƙarkashin jam'iyyar APC.

Wannan wata muhimmiyar ziyara ce da ke nuna aniya, da shirinsa na yi wa al’ummar Nasarawa hidima da wakilci nagari, tare hidimta musu babu ƙyashi, babu gazawa.

Al’umma na ci gaba da nuna goyon baya da fatan alkhairi ga wannan tafiya ta haziƙin matashi Babba Ɗan Babba, rugum babban motsi, Maza gumbar Dutse.

Ubangiji Allah ya bamu nasara.



25/04/2026

Zuwa karbar Katin Jam’iyyar APC na Maigirma Mal Ibrahim Shekarau CON PEN.

25/04/2026

Jawabin Maigirma Gwamnan Kano HE Abba Kabir Yusif Wajen Taron karbar katın Jam’iyyar APC na Maigirma Mal İbrahim Shekarau.

Address

Mundubawa Bompai Kano
Kano Outlying
00007

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Shekarau New Media Team posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share