29/04/2026
Yerima Shettima ya halarci addu'ar uku na rasuwar sirikin Yusuf Zailani
Ambasada Yerima Shettima, ɗan takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya, ya halarci addu'ar ukun sirikin Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani, ɗan majalisar jiha mai wakiltar Igabi, a yau Laraba.
An gudanar da ta’aziyyar ne a gidan marigayin da ke unguwar Rigachikun a cikin garin Kaduna, inda ‘yan’uwa, abokai da masu ruwa da tsaki a harkar siyasa s**a taru domin jajanta wa iyalan mamacin da kuma Honarabul Zailani kan wannan babban rashi.
Ambasada Yerima Shettima ya isa wajen ta’aziyyar tare da tawagarsa, inda s**a miƙa ta’aziyyarsu cikin girmamawa da nuna alhini. A yayin ziyarar, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar, yana mai cewa rashin matashi irin marigayin babban gibi ne ga iyali da al’umma baki ɗaya. Ya kuma yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya jiƙan sa da rahama, tare da ba iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.
Bayan kammala zaman ta’aziyyar, Ambasada Yerima Shettima da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani sun ɗan tattauna wasu muhimman batutuwa da s**a shafi al’umma da harkokin siyasa, kafin daga bisani su yi sallama cikin girmamawa.
Shi ma Honarabul Zailani ya nuna godiyarsa ga Yerima Shettima bisa wannan ziyara ta ta’aziyya, yana mai cewa hakan ya nuna ƙauna, zumunci da mutunta juna da ke tsakanin su.
Ziyarar ta gudana cikin yanayi na natsuwa da addu’o’i, inda malamai s**a jagoranci karatun Alƙur’ani da addu’ar neman gafara ga mamacin.