29/05/2026
Cika shekara uku a mulki: Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki sun fara haifar da ɗa mai ido
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa Nijeriya ta fara fita daga mawuyacin halin rashin tabbas a fannin tattalin arziki, ya ce ƙasar tana kan turbar farfaɗowa da bunƙasa yayin da gwamnatin sa ta cika shekara uku a mulki.
A jawabin da ya yi ga al’ummar ƙasa domin bikin cika shekaru uku na mulkin sa a ranar wannan Juma'ar, Shugaba Tinubu ya amince cewa ‘yan Nijeriya sun sha wahalhalu sakamakon manyan sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin sa ta aiwatar, ciki har da cire tallafin man fetur da kuma haɗa tsarin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje. Sai dai ya jaddada cewa waɗannan matakai sun zama dole domin kauce wa faɗuwar tattalin arziki da kuma shimfiɗa tubalin cigaba mai ɗorewa.
Shugaban ya ce lokacin da gwamnatin sa ta hau mulki a shekarar 2023, ƙasar nan tana fama da matsaloli masu yawa da s**a haɗa da matsin tattalin arziki, raguwar kuɗaɗen shiga, matsalolin tsarin canjin kuɗaɗen waje, hauhawar kuɗin biyan basuss**a, rashin tsaro da kuma raguwar amincewar jama’a da hukumomin gwamnati.
A cewar sa, Nijeriya na kashe kusan Naira biliyan 18.4 a kowace rana wajen tallafin man fetur, lamarin da ya kai sama da Naira tiriliyan 4 a shekarar 2022 kaɗai. Ya kuma ce tsarin canjin kuɗaɗen waje da yawa ya haifar da asarar sama da Naira tiriliyan 8 cikin shekaru uku sakamakon amfani da guraben da tsarin ya samar domin cin riba ba tare da samar da wata ƙima ga tattalin arziki ba.
“Zaɓi mafi sauƙi zai kasance mai amfani a siyasance, to amma shugabanci yana buƙatar jajircewa da ɗaukar matakan da s**a dace ko da kuwa suna da wahala,” inji Tinubu, yana mai cewa rashin ɗaukar waɗannan matakai zai iya jefa ƙasar nan cikin matsananciyar matsalar tattalin arziki da ƙarin talauci.
Da yake zayyana nasarorin da gwamnatin sa ta samu cikin shekaru uku, Shugaban ya ce tattalin arzikin Nijeriya ya zama mafi ƙarfi kuma ya fi dacewa da cigaba mai ɗorewa. Ya ce an samu ƙaruwar amincewar masu zuba jari, inganta kuɗaɗen gwamnati da kuma bunƙasar kasuwar hannayen jari, inda darajar kasuwar ta tashi daga Naira tiriliyan 30 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 160 a shekarar 2026.
Tinubu ya kuma bayyana cewa ana gudanar da manyan ayyukan more rayuwa a faɗin ƙasar nan, inda ya ce fiye da kilomita 2,700 na manyan hanyoyi ake cikin ginawa, gyarawa ko faɗaɗawa. Ya ambaci Babban Titin Bakin Teku na Legas zuwa Kalaba, Babban Titin Sakkwato zuwa Badagiri, hanyar Abuja-Kaduna-Zariya-Kano da kuma titin Gabas zuwa Yamma a matsayin wasu daga cikin manyan ayyukan da ake aiwatarwa.
Ya ƙara da nuni da cewa ana ci gaba da aikin sabunta hanyoyin jirgin ƙasa domin inganta sufuri da haɗa yankunan ƙasar nan ta fuskar tattalin arziki.
A fannin mai da iskar gas, Shugaban ya ce sauye-sauyen da gwamnatin sa ta aiwatar sun jawo sababbin jarin biliyoyin daloli daga kamfanonin ƙasa da ƙasa. Ya kuma ce ƙarfin tace mai a cikin gida ya ƙaru, abin da ke rage dogaro da shigo da man fetur daga ƙasashen waje tare da adana kuɗaɗen musayar waje.
Game da wutar lantarki, Tinubu ya ce gwamnatin sa tana saka hannun jari wajen faɗaɗa hanyoyin isar da wuta, inganta tsarin sadarwa da kuma amfani da makamashi mai sabuntawa domin tabbatar da cewa tattalin arzikin ƙasar nan ya samu ingantaccen tushen cigaba.
Shugaban ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a fannoni daban-daban kamar noma, ilimi, gidaje, lafiya, sadarwa da fasahar zamani. Ya ce shirye-shiryen tallafa wa manoma sun amfani miliyoyin manoma a faɗin ƙasar nan, yayin da Asusun Lamunin Ilimi na Nijeriya ya taimaka wa sama da ɗalibai miliyan 1.5 samun damar cigaba da karatu ta hanyar bayar da sama da Naira biliyan 282.
A ɓangaren gidaje kuwa, ya ce sama da gidaje 10,000 ne ake ginawa a jihohi 14 da Babban Birnin Tarayya ƙarƙashin Shirin 'Gidajen Renewed Hope' da na Hukumar Gidaje ta Tarayya, lamarin da ya samar da fiye da ayyukan yi 300,000.
Dangane da tsaro, Shugaban ya ce jami’an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, ɓarayin man fetur da sauran masu aikata laifuffuka. Duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale, ya ce yankuna da dama da hanyoyi sun fi samun zaman lafiya fiye da da.
“Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba har sai kowane ɗan Nijeriya ya samu damar rayuwa, aiki, tafiye-tafiye da cimma burin sa cikin tsaro,” inji shi.
Tinubu ya yi kira ga jama'ar ƙasa da su ci gaba da haɗin kai tare da kauce wa rarrabuwar kawuna, yana mai jaddada cewa cigaban Nijeriya yana buƙatar haɗin gwiwar kowa ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini, yanki ko ƙabila ba.
“Dole ne mu zaɓi fata maimakon yanke ƙauna, haɗin kai maimakon rarrabuwar kawuna, da gina ƙasa maimakon son rai,” inji Shugaban.
Da yake duban gaba, Tinubu ya yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin rage farashin abinci da sufuri, samar da ƙarin ayyukan yi da kuma tabbatar da cewa amfanin sauye-sauyen tattalin arziki ya kai ga talakawan Nijeriya.
Ya sha alwashin cewa Nijeriya za ta fito daga ƙalubalen da take fuskanta cikin ƙarfi da wadata, yana mai cewa ƙasar tana fuskantar wani gwaji ne na tarihi wanda daga ƙarshe zai haifar da zaman lafiya, cigaba da haɗin kai.
“A yau duniya na sake kallon ƙasar mu, ba a matsayin ƙasar da matsaloli s**a bayyana ba, amma a matsayin ƙasar da ta ƙudiri aniyar tashi tsaye da cimma nasara,” inji shi.