Arewa Computer Library

Arewa Computer Library Koyon ilimin na'ura da harshen hausa..

Alhamdulillah!Yan'uwa kusa mana Albarka.Na kammala kusan kashi 80% na wannan littafi mai taken: "Pantami: The Digital Ar...
31/07/2025

Alhamdulillah!

Yan'uwa kusa mana Albarka.

Na kammala kusan kashi 80% na wannan littafi mai taken: "Pantami: The Digital Architect of a New Nigeria"
(a cikin harshen Hausa da kuma Turanci).

Wannan littafi ya samu sanyawar albarka da kuma sahalewar Professor Isa Ali Pantami CON, da kansa. Kuma Muna fatan kaddamar da shi (Launching) a cikin birnin Gombe, in sha Allah, bayan kammala aikin gyara da bugawa, muna sa ran Professor da kansa zai kasance babban bako na musamman a taron.

Abubuwan da littafin ya ƙunsa sun haɗa da:

1. Gudunmawar Professor Pantami ga ci gaban Nigeria, tun daga lokacin da yake DG na NITDA har zuwa lokacin da ya zama Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki.

2. Cigaban da aka samu a NITDA a lokacin jagorancinsa, da kuma rawar da hukumar ta taka wajen sauya tsarin digital a Najeriya.

3. Nasarar da Ma'aikatar Sadarwa da Tattalin Arzikin ta samu a karkashin jagorancinsa, da wasu muhimman ayyuka da aka aiwatar a wannan lokaci.

4. Gudunmawar Professor Pantami a fannonin:

A. Noma
B. Lafiya
C. Ilimi
D. Sana’o’i
E. Tsaro
F. Tattalin Arziki

5. Ayyukan talafawa matasa da ya jagoranta daga matakin jaha har zuwa matakin tarayya da adadi da misalan wasu daga cikin matasan da s**a amfana.

6. Ayyukan da ya aiwatar a dukkan jahohi 19 na Arewacin Najeriya, da tasirinsu ga al’umma.

7. Gudunmawar sa ta musamman ga Jahar Gombe, musamman a fannoni kamar:

A. Noma
B. Ilimi
C. Lafiya
D. Sana’o’i

8. Ci gaba da bayar da gudunmawarsa bayan barin kujerar Minista, inda har yanzu yake ba da tallafi da tsari ga al’umma da matasa.

9. Yabon da ya samu daga shugabanni, malamai da dattawan kasa, wanda ke nuna irin girmamawa da martabar da ya samu a idon al’umma.

Allah yasa albarka, Allah kuma ya bamu ikon kammala aikin lafiya. Amin

17/07/2025

ACL💖

16/02/2025

Big shout-out to our newest top fans! Kamal Ladan Inusa, Aliyu Tijjani, Mübãräk Ïsãh Mübxëy, Auwal Umar Faruk, Muhammad Barau

10/01/2025

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.

Haƙiƙa ga Allah muke kuma gare Shi zamu koma. Cikin daren nan Ubangiji ya karɓi rayuwar mahaifin coordinator namu na jahar kano Ubale Sumaila, zuwa safiyar wannan rana ta Jumu'a akayi janaizar sa kamar yanda addinin Musulunci ya tanadar.
Rayuwa mara tabbas zuwa rayuwa madauwamiya.

Allah Ya gafarta masa, Ya jikan sa, Ya sanya aljannah ta zamo makoma gare shi.

Signed: ACL National Office.

Arewa Computer Library Gombe State Chapter ta karrama Professor Isa Ali Pantami CON (Majidadin Daular Usmaniyya) da awar...
30/12/2024

Arewa Computer Library Gombe State Chapter ta karrama Professor Isa Ali Pantami CON (Majidadin Daular Usmaniyya) da award ta girmamawa, a yau 30th ga watan December a wurin yayen dalibai 100 da Professor ya dauki nauyin horarwa.

You're all invitedArewa Computer Library Gombe State Chapter
27/12/2024

You're all invited
Arewa Computer Library Gombe State Chapter

18/12/2024

Duk jahar da take bukatar mu, domin horar da matasa ilimin computer, a shirye muke domin babu jahar da bamu da kwararru.

Dakin karatu ake bukata kawai

Ku nemi sponsors kawai!

A karkashin Sponsorship na Professor Isa Ali Pantami Kungiyar Arewa Computer Library (ACL) zatayi graduating dalibai 100...
18/12/2024

A karkashin Sponsorship na Professor Isa Ali Pantami Kungiyar Arewa Computer Library (ACL) zatayi graduating dalibai 100 da s**a koyi ilimin computer a jahar gombe.

Haka zalika a karkashin Sponsorship dinsa ACL zata ci gaba da horar da matasa ilimin computer a jahar gombe har sai an horar da dalibai 1,000.

17/12/2024

Babu jahar da bamu da Members kuma babu jahar da bamu da coordinator, haka zalika babu jahar da bamu da kwararrun malamai a Arewa.

16/12/2024

A ko wace jaha a cikin Arewacin Nigeria Arewa Computer Library Zata iya shiga ta horar da matasa ilimin Na'ura domin dogaro dakai.

01/09/2024

Me zaka iya cewa akan Arewa Computer Library?

Address

Kawo Capital Plaza Room 033
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Computer Library posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Arewa Computer Library:

Share

Category