20/10/2023
Jan Hankali Ga Al'ummar Jahar Jigawa!
Ina mai farin cikin sanar da ku cewa gwamnatin jihar Jigawa za ta fara rabon naira biliyan 1.080 da aka ware domin tallafawa marasa galihu sama da 108,000 a faɗin mazabu 287 a ƙananan hukumomi 27 na jihar daga gobe Jumu'a 20 ga watan Oktoba, 2023.
Mutane 4,000 da zasu ci gajiyar tallafin daga kowace Ƙaramar Hukumar na ƙananan hukumomi 27, da s**a cike fom, aka tantance, kuma s**a cika sharuɗan da ake buƙata za su fara karɓar Naira 10,000 kowannen su a matsayin tallafi. Wannan yunƙuri an bijiro da shi rage wahalhalun da ƴan ƙasa ke fuskanta a waɗannan lokutan masu cike da ƙalubale.
A wannan tsarin, an ware Naira miliyan 40 ga kowacce Ƙaramar Hukuma dake ƙananan hukumomi 27 da ake da su, domin raba wa matasa 1,000, mata 1,000, tsofaffi 1,000, da kuma nakasassu 1,000 masu fama da matsalar rashin lafiya. Wannan shi ke tabbatar da cewa ɗimbin mutane masu rauni a cikin al'ummarmu za su ci gajiyar wannan shirin.
Ina mai farin cikin sanar da waɗanda zasu ci gajiyar tallafin daga ƙananan hukumomin Dutse da Malam Madori, cewa za su karbi tallafin kuɗi har naira miliyan 40,000,000, wanda adadin kuɗin ya kai ₦80,000,000. Zamu cigaba da shirin rabon kuɗaɗen inda zamu dinga ɗaukar Ƙananan Hukumomi biyu a duk sanda za'a yi biyan, har sai an kammala cika dukkanin ƙananan hukumomi 27, tare da tabbatar da cewa ba a bar kowa a baya ba.
Wannan shiri na nuni ne da jajircewar Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi (FCA) wajen kyautata jin daɗin al’ummarmu. Mun fahimci ƙalubalen da yawancin ƴan ƙasar mu ke fuskanta a halin yanzu, kuma mun himmatu wajen bada tallafin da ya dace don taimaka musu a cikin wannan mawuyacin yanayi.
Ina kira ga duk waɗanda s**a amfana da su yi amfani da waɗannan kuɗaɗe cikin hikima da kuma hanyar da za ta inganta rayuwarsu. Muna da yaƙinin cewa wannan taimako zai taimaka wajen rage raɗaɗin da mutane ke fuskanta da kuma samar da sauƙi a rayuwarsu ta yau da kullum.
Copied from
Auwal Auwal D. SankaraAuwal D. San