20/05/2026
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, , ya yi kira na musamman ga tsohon shugaban ƙasar Najeriya, , da ya dakatar da duk wani yunƙuri na komawa cikin siyasar Najeriya a wannan lokaci da ƙasar ke fuskantar yanayin siyasa mai cike da ruɗani.
Lamido ya bayyana cewa Jonathan ya fahimci matsayinsa a Najeriya a matsayin jagora kuma tsohon shugaban ƙasa, wanda hakan ya sanya ya zama wata alama ta haɗin kan ƙasa. Ya ƙara da cewa Jonathan na cikin jerin manyan shugabannin duniya da ake girmamawa a matakin ƙasa da ƙasa.
A cewarsa, bai dace a jawo Jonathan cikin wannan yanayin siyasa mai cike da son kai da neman anfani na kashin kai ba, musamman ganin cewa saura kwanaki kaɗan a rufe tantancewar ‘yan takarar da za su fafata a zaɓen shekarar 2027.
Lamido ya ce jam’iyyun siyasar Najeriya sun rarrabu tare da rasa cikakkiyar manufa ta siyasa, inda mafi yawansu s**a mayar da hankali kan neman mulki kawai.
Ya bayyana cewa kiraye-kirayen da ake yi wa Jonathan ya dawo siyasa — ko da kuwa da kyakkyawar niyya ake yi — sun samo asali ne daga halin rashin tabbas da takaicin da Najeriya ke ciki.
“A halin yanzu, Jonathan ya kamata ya ci gaba da riƙe matsayinsa na mutunci da kima a matsayin wani ginshiƙi na ƙasa baki ɗaya,” in ji Lamido.
Ya ƙara da cewa duk da ana yaba irin wannan kira, amma kira ne na gaggawa da takaici wanda bai wuce bayyana damuwar jama’a ba.
Lamido ya jaddada cewa Jonathan bai kamata ya bari irin wannan kira na lallashi ya jawo shi komawa siyasa yanzu ba, yana mai cewa har yanzu akwai damar a ajiye shi domin wani lokaci na gaba.