06/12/2025
Al'ummar Karamar Hukumar Jibia Assalamualaikum
Ina farin cikin sanar da kaddamar da shirin karfafa tattalin arziki da kuma gagarumin cigaban ayyukan more rayuwa domin inganta rayuwa da cigaban al’ummominmu a fadin Karamar Hukumar Jibia.
A wannan karon mun tallafawa alumma ta hanyar raba kayayyakin sana’o’i domin karfafa kananan masana’antu da bunkasa tattalin arzikin mata da matasa, wanda ya hada da:
Injin nika 100
Keken dinki 100
Injin yin taliya da fulawa 100
Injin markade 100
Kayan masu shayi 100
Kayan aski 100
Wadannan kayan zasu taimakawa mata da matasa musamman masu sana’o’in cikin gida wajen samun dogaro da kai da fadada sana’arsu.
Sauran kayan tallafin sun hada da:
Motoci 20
Kekunan guragu 50
Babura 75 ga matasa
Kayan daki ga amare marayu 10
Tallafin kuɗi ₦20,000 ga matasa maza da mata su 609
Sabbin babura 17 ga dukkan magaddai
Gwamnatina ta kuma aiwatar da muhimman ayyukan cigaba a sassa daban-daban na Jibia, ciki har da:
1. Bude Sabon Ofishin Shugaban Karamar Hukuma
Gini mai inganci da na zamani domin inganta gudanar da mulki da kusantar da jama’a da hidimomi masu inganci.
2. Kaddamar da Sabon Dakin Taron Majalisar Karamar Hukuma
Wannan gini na zamani zai inganta tattaunawa, zartar da dokoki, da kyakkyawan gudanar da mulki a matakin karamar hukuma.
3. Sabon Ginin Asibitin Hayin Gada Mai Dakuna 12
Sannan Mun kaddamar da sabon ginin amenity mai dakuna 12 a Asibitin Hayin Gada domin fadada ayyukan lafiya, karbar marasa lafiya, da inganta kula da lafiyar jama’a.
4. Da Sauran Wasu Ayyuka Daban-Daban
Yanzu haka ana cigaba da aiwatar da wasu muhimman ayyuka a fadin karamar hukumar jby domin karfafa al’umma, gina cibiyoyi, da inganta jin dadin jama’a wanda yanzu haka baa ida kammalasu ba.
Da wannan nike mika godiya t musamman ga Maigirma Gwamna Malam Dikko Umar Radda, PhD, bisa baiwa kananan hukumomi cikakken ikon gudanarwa. Wannan goyon baya ne ya bamu damar yi wa al’ummarmu hidima cikin alfahari da cikakkiyar gaskiya da amana.