Hon.Abubakar Na'amare Jega

Hon.Abubakar Na'amare Jega Youth Leader and Politician

Ɗan Najeriya, idan ka ga dama ka sake zaɓensa, amma ka tuna: zaɓenka ne ke ƙayyade makomarka ta gobe.Allah Ya zaɓa mana ...
15/09/2026

Ɗan Najeriya, idan ka ga dama ka sake zaɓensa, amma ka tuna: zaɓenka ne ke ƙayyade makomarka ta gobe.

Allah Ya zaɓa mana shugabanni masu tausayin talaka, masu adalci da kishin ƙasa. Amin Ya Allah.

15/09/2026

DUK WANDA YA ƘARA CEWA TINUBU BAYA AIKIN KOMAI A ƘASAR NAN, KA NUNA MASA WAƊANNAN ABUBUWAN DA TINUBU YA YI...

A duk tarihin Najeriya, babu wani shugaban da ya yi aikin da Tinubu ya yi kuma yake kan yi. Mutane suna yawan ƙorafi, amma ba su lura da irin gagarumin ci gaban da aka samu ba.

Ga wasu daga cikin ainihin Ayyukan da Tinubu ya yi mana a cikin shekaru uku na mulkinsa:

1. Man Fetur (Lita ɗaya):
A baya ₦185 ne, amma yanzu an inganta shi ya koma ₦1,400.

2. Darajar Dala ($):
A baya Dala ₦460 ce, yanzu an yi aiki ta koma ₦1,550.

3. Shinkafa (Buhu 50kg):
A baya tana ₦28,000 kacal, yanzu an taimaka ta tashi zuwa ₦95,000.

4. Gas ɗin Girki (12.5kg):
A baya ₦7,000 ne, yanzu ya koma ₦24,000.

5. Hauhawar Farashi (Inflation):
A baya yana 21.4%, yanzu ya cilla sama zuwa 33%+.

6. Biredi (Lof ɗaya):
A baya ₦800 ne, yanzu ya koma ₦2,000 zuwa sama.

7. Siminti (Buhu 50kg):
A baya ₦4,000 ne, yanzu an yi aiki ya koma ₦11,000 zuwa sama.

8. Wutar Lantarki (Band A):
A baya farashin yana da sauƙi, yanzu ya koma ₦209.50 a kowane kWh guda.
Kuma naji zai cire tallafin wutar lantarki soon.

9. Kuɗin Mota (A Gari):
A baya ana shiga N500 zuwa N700, yanzu ya koma N1,500 zuwa N2,500.

10. Data na Waya (1GB):
A baya ₦200 zuwa ₦250 ce, yanzu ta tashi zuwa ₦1,000 zuwa ₦1,200+.

11. Kuɗin Makaranta na Jami'a (Federal):
A baya ₦100,000 zuwa ₦150,000 ne, yanzu an ninka shi zuwa ₦300,000 zuwa ₦500,000+.

12. Kayan Abinci na Yau da Kullum:
A baya da ₦72,000 za ka yi sayayya mai tsoka, yanzu sai da ₦220,000 zuwa sama.

13. Mafi Ƙarancin Albashi:
An samu ci gaba daga ₦30,000 zuwa ₦70,000 (Duk da cewa darajar kuɗin ta riga ta zube a kasuwa).

14. Darajar Kuɗin Shiga:
A baya ana ɗan morar albashi, amma yanzu albashin baya isar mutum na kwanaki 10 da fara aikin wata.

15. Harkar Tsaro:
A baya satar mutane ba ta yi kamari sosai ba, amma yanzu mun ci gaba da yawaitar satar mutane da ɗalibai kusan kowane lokaci.

Wannan shi ne ainihin Renewed hope da akayimaku Alkawali

Babu zagi Babu cin mutunci,

A TAUSAYA WA TALAKAAbin takaici ne matuƙa ganin yadda hauhawar farashin man fetur ke ƙara jefa rayuwar talakawan Najeriy...
13/09/2026

A TAUSAYA WA TALAKA

Abin takaici ne matuƙa ganin yadda hauhawar farashin man fetur ke ƙara jefa rayuwar talakawan Najeriya cikin matsi, tashin hankali da tsadar rayuwa. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zo ya tarar da farashin litar man fetur kusan ₦250, amma yau hoton da ke yawo ya nuna farashin lita ya kai ₦1,562.50.

Wannan ba ƙaramin sauyi ba ne. Ƙarin farashin man fetur yana da tasiri kai tsaye kan sufuri, farashin kayan abinci, haya, noma, kasuwanci, samar da kayayyaki da sauran bukatun yau da kullum.

Idan farashin man fetur ya ƙaru, kusan komai yana bin sa ne. Kudin mota yana ƙaruwa, farashin kayan abinci yana tashi, ’yan kasuwa suna fuskantar ƙarin kuɗin jigilar kaya, manoma suna ƙara kashe kuɗi wajen samar da amfanin gona, sannan iyalai suna ƙara fuskantar wahalar tafiyar da rayuwarsu.

Abin da ya fi ciwo shi ne yadda talaka yake ƙoƙarin rayuwa cikin wannan matsin tattalin arziki, yayin da kudin shiga bai ƙaru daidai da hauhawar farashin kayayyaki ba. Mutane suna aiki tuƙuru suna neman abin da za su ci, amma abin da suke samu yana ƙara rasa ƙima a kullum.

Talaka ba ya neman alfarma; yana neman damar rayuwa cikin mutunci. Yana son samun abinci mai araha, sufuri mai sauƙi, ingantaccen kiwon lafiya, ilimi mai kyau, tsaro da damar gudanar da kasuwanci ba tare da tsananin matsin tattalin arziki ba.

Wannan ya kamata ya zama babban darasi ga shugabanni da ’yan ƙasa baki ɗaya. Duk wata manufar tattalin arziki ya kamata a auna ta da irin tasirin da take yi ga rayuwar talaka. Ba wai kawai a duba lambobin tattalin arziki ba, har ma a duba rayuwar iyalai da halin da talakawa ke ciki a zahiri.

A matsayinmu na ’yan ƙasa, muna da hakkin tambayar gwamnati tambayoyi masu muhimmanci, neman gaskiya, bayyana damuwarmu cikin lumana, sannan mu yi amfani da ’yancinmu na dimokuraɗiyya wajen tantance ayyukan kowace gwamnati da irin tasirin manufofinta ga rayuwar jama’a.

Ya Allah Ka tausaya wa al’ummar Najeriya. Ka sauƙaƙa mana wannan tsadar rayuwa, Ka kawo sauƙin tattalin arziki, Ka albarkaci arzikin ƙasarmu, Ka ba shugabanninmu hikima, adalci, tausayi da tsoron Allah wajen gudanar da amanar da aka ɗora musu.

Ya Allah Ka taimaki talakawa da marasa ƙarfi, Ka buɗe ƙofofin arziki ga iyalai, Ka rage mana wahala da tsadar rayuwa, Ka dawo da albarka cikin abincinmu da dukiyarmu.

Allah Ya kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata mai ɗorewa a Najeriya. Ya sa gobe ta fi yau alheri, Ya kare ƙasarmu daga duk wani sharri, Ya shiryar da shugabanni da ’yan ƙasa baki ɗaya zuwa ga abin da ya fi alheri.

Amin Ya Rabbal Alamin.

Abubakar Na’amare Jega
(Majikiran Jega)

1st Majikiran JegaMay Allah continue to bless our lives with abundant blessings, good health, peace, happiness, and succ...
13/09/2026

1st Majikiran Jega

May Allah continue to bless our lives with abundant blessings, good health, peace, happiness, and success. May Allah also bless our beloved country, Nigeria, with lasting peace, unity, and prosperity.

12/09/2026

BETRAYAL OF THE STRUGGLE: FROM PROTESTERS TO PROFITEERS

I hear petrol is now selling for as much as ₦1,500 per litre in some places. So, you people are no longer complaining because you’re about to own a small stake in the refining company, abi?

From fighting against high fuel prices to suddenly staying silent when the price skyrockets what changed?

Sellouts! You betrayed the struggle.

ABIN DA JAMA’A SUKE BUKATA DAGA SHUGABANNIA kowace al’umma, musamman a Najeriya, talakawa da masu karamin ƙarfi su ne ma...
10/09/2026

ABIN DA JAMA’A SUKE BUKATA DAGA SHUGABANNI

A kowace al’umma, musamman a Najeriya, talakawa da masu karamin ƙarfi su ne mafi yawan mutanen da ke jin tasirin shugabanci kai tsaye. Saboda haka, abin da ya kamata jama’a su fi duba a lokacin zaɓe ba wai kalamai da alkawuran siyasa kaɗai ba ne, illa ayyukan da shugaban ya aiwatar da kuma yadda s**a inganta rayuwar jama’a.

Tsaro yana daga cikin muhimman abubuwan da gwamnati ke da alhakin tabbatarwa. Idan babu tsaro, noma, kasuwanci, ilimi da sauran harkokin rayuwa ba za su samu kwanciyar hankali ba.

Hanyoyi kuma suna da matuƙar muhimmanci. Hanyoyi masu kyau suna sauƙaƙa zirga-zirga, rage kuɗin sufuri, taimaka wa manoma wajen kai amfanin gona kasuwa, tare da haɗa garuruwa da ƙauyuka.

Asibitoci da kiwon lafiya su ne ginshiƙan rayuwa. Talakawa bai kamata su rasa kulawar lafiya saboda rashin kuɗi ko rashin ingantattun cibiyoyin lafiya ba. Ya kamata gwamnati ta tabbatar da samun asibitoci masu aiki, magunguna, kayan aiki da ƙwararrun ma’aikata.

Ruwan sha mai tsafta ma ba alfarma ba ce; haƙƙi ne na jama’a. Samun tsaftataccen ruwa yana taimakawa wajen rage cututtuka da inganta lafiyar iyalai.

Ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. Ya kamata a samar da makarantu masu kyau, malamai, kayan koyarwa da damar samun ilimi ga yara daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.

Haka kuma, inganta kasuwanci da samar da ayyukan yi ga matasa suna da matuƙar muhimmanci. Matasa suna buƙatar damar koyon sana’o’i, samun horo, tallafin jari da yanayin da zai ba su damar kafa sana’o’insu. Idan aka samar da ayyukan yi, za a rage zaman banza da matsalolin da ke addabar al’umma.

Saboda haka, ya kamata ɗan Najeriya, musamman talaka, ya koyi tambayar kansa: Me wannan shugaban ya yi wa al’umma? Mene ne ya inganta? Kuma me ya canza a rayuwar talakawa?

A lokacin zaɓe, kada mu kalli jam’iyya, ƙabila, addini ko kyawawan alkawura kawai. Mu duba aiki, gaskiya, amana, shugabanci nagari da sakamakon da jama’a s**a gani.

Idan shugaban ya samu damar yin wa’adi na farko, ya kamata jama’a su tantance ayyukansa kafin su sake ba shi damar ci gaba. Zaɓe ba kyauta ba ne; amana ce da jama’a ke ba wa wanda suke ganin zai yi musu hidima.

Mu riƙa zaɓar shugabanni bisa abin da s**a aikata, ba kawai abin da s**a ce za su yi ba.

Najeriya za ta samu ci gaba ne idan jama’a s**a nemi shugabanci mai inganci, s**a riƙa tambayar shugabanni gaskiya, kuma s**a yi amfani da ƙuri’arsu cikin hikima da kishin ƙasa.

Allah Ya kawo mana shugabanni nagari, masu tsoron Allah, gaskiya da kishin al’umma.

Hon. Abubakar Na’amare Jega
(Majikiran Jega)
National
Chairman Northern Youths Coalition Forum

2027 HAJJ MEDICAL TEAM RECRUITMENTApplications are now open for the recruitment of qualified medical personnel to serve ...
10/09/2026

2027 HAJJ MEDICAL TEAM RECRUITMENT

Applications are now open for the recruitment of qualified medical personnel to serve Nigerian pilgrims during the 2027 Hajj Exercise.

Qualified medical professionals who are interested in serving Nigerian pilgrims are encouraged to apply through the official portal:

🌐 www.nahcon.gov.ng/nmt/

Please ensure you meet the required qualifications before submitting your application.

Good luck to all applicants!

Please share this information with qualified medical professionals who may be interested.

ME YA SA ƘASASHEN MASU MAN FETUR SUKE MORE ARZIKIN MAN NASU, AMMA TALAKAN NIGERIA KE FUSKANTAR TSADAR RAYUWA?Ya kamata m...
10/09/2026

ME YA SA ƘASASHEN MASU MAN FETUR SUKE MORE ARZIKIN MAN NASU, AMMA TALAKAN NIGERIA KE FUSKANTAR TSADAR RAYUWA?

Ya kamata mu tsaya mu yi tunani: shin farashin man fetur da talakan Najeriya ke fuskanta a yau ya yi daidai da kasancewar Najeriya ƙasa ce mai dimbin arzikin man fetur?

Cire tallafin man fetur ya haifar da gagarumin ƙarin farashin PMS, wanda ya shafi kusan kowane fanni na rayuwar ɗan Najeriya. Tsadar man fetur na nufin tsadar sufuri, abinci, kayan masarufi, noma da samar da kayayyaki, lamarin da ke ƙara jefa iyalai da ƙananan ’yan kasuwa cikin matsin tattalin arziki.

Abin da ya dace shi ne mu duba halin da sauran ƙasashe masu arzikin man fetur suke ciki, mu tambayi kanmu: Me ya sa talakan Najeriya, wanda ƙasarsa ke da dimbin albarkatun man fetur, yake fuskantar irin wannan tsadar makamashi?

Wannan ba kira ba ne na s**ar gwamnati, sai dai kira ne na tausayi, fahimta da ɗaukar matakan da za su rage wa talaka nauyi. Muna roƙon shugabanninmu da su duba hanyoyin da za su rage farashin makamashi, musamman ta hanyar ƙarfafa matatun mai na cikin gida, inganta samar da wutar lantarki, rage farashin sufuri, tallafawa manoma da ƙananan ’yan kasuwa, tare da tabbatar da cewa amfanin albarkatun ƙasa ya isa ga talakawa.

Shugabanni, ku saurari muryar talaka. Ku tausaya masa. Ku tabbatar da cewa gyare-gyaren tattalin arziki ba su zama ƙarin nauyi ga talakawa ba, sai dai su zama hanyar samun sauƙi da kyakkyawar makoma.

Najeriya ƙasa ce mai albarkatu, kuma burinmu shi ne ganin waɗannan albarkatu sun inganta rayuwar ’yan ƙasa baki ɗaya.

’YAN NIGERIA, ZABI YA RAGE A HANNUN KU

Idan lokacin zaɓe ya zo, ku tsaya ku yi tunani, ku duba tarihin ’yan takara da ayyukansu, sannan ku zaɓi shugabanni masu adalci, gaskiya, kishin ƙasa, tausayi da jinƙai.

Kada mu zaɓi shugaba saboda son rai, ƙabila, addini ko abin da aka ba mu na ɗan lokaci. Mu zaɓi shugabannin da za su saurari talaka, su kare muradun jama’a, su yi amfani da albarkatun ƙasa domin amfanin kowa, kuma su yi mulki cikin adalci da amana.

Zaɓe shi ne damar ɗan ƙasa ta bayyana ra’ayinsa. Idan lokacin ya zo, mu yi amfani da wannan dama cikin hikima da kishin ƙasa.

“Albarkatun ƙasa na kowa ne ci gaban ƙasa ya kamata ya shafi kowa.”

Abubakar Na'amare Jega
(Majikiran Jega)

09/09/2026

BUHARI UMAR DANWARAI: THE TALENTED YOUNG ENGINEER

Engineer Buhari Umar Danwarai, from Aliero Local Government Area of Kebbi State, has demonstrated remarkable technological skills, creativity, and innovation at a young age.

On behalf of the Inna-Tafidah-Boya Foundation (ITBF), we appeal to the Kebbi State Government, Federal Government, philanthropists, corporate organisations, NGOs, foundations, and potential sponsors to come forward and support this talented young man.

We are seeking support for his education, advanced technical training, mentorship, tools and equipment, and further development of his technological innovations.

With the right support, education, mentorship, and exposure, Buhari can further develop his talent, create innovative solutions to local challenges, generate employment opportunities, and contribute meaningfully to the technological development of Kebbi State and Nigeria.

We therefore call on individuals, organisations, and sponsors who are willing to invest in this young talent to come forward and give him the opportunity to reach his full potential.

A CALL TO SPONSORS AND PARTNERS

This is a talent worth investing in. Let us discover, support, and nurture Buhari Umar Danwarai’s potential today for a more innovative and prosperous Nigeria tomorrow.

Inna-Tafidah-Boya Foundation (ITBF)
Changing Lives, Building Hope, Creating Sustainable Communities

Abubakar Na’amare Jega
(Majikiran Jega)
National Coordinator
Inna-Tafidah-Boya Foundation (ITBF)

With my friend and lawyer, Barr. Abubakar Kawuwa Jalingo. May Allah make you Attorney General of the Federation. Ameen.
03/09/2026

With my friend and lawyer, Barr. Abubakar Kawuwa Jalingo.

May Allah make you Attorney General of the Federation. Ameen.

Address

Jega

Telephone

+2347064998864

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hon.Abubakar Na'amare Jega posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Hon.Abubakar Na'amare Jega:

Shortcuts

Share