15/07/2015
"
"
'YAN-UWA-
Ina mai Matuqar Farincikin Gabatar muku
da Wannan Lakcar, Mai Suna Kamar
haka.......
"
"
ZAN GABATAR DA WANNAN LAKCAR/ BA
DON KOMAIBA......
"
"
SAI DAN-
yadda naga Sallar tana Qara Fuskantaru a
'yan-wasu Kwanaki da zasu zo Nan bada
Dadewa ba..
"
"
DAN HAKA-
Muyi haquri mu Karanta Wannan Saqon,
Domin amfanin kanmu da Iyalinmu...
"
"
'YAN-UWA,
KAMAR YADDA NACE-
"
* MECE CE SALLAR-IDI ???
"
"
AMSA-
sallar-idi, / Sallace da ake gabatarda ita a
wani Lokaci Ke6antacce, a wata Siffa
Ke6antacciya, Sau biyu (2) a Shekara....
"
"
'YAN-UWA-
Kafin in kaiga fashin Baqin Wannan Ta'arifi
na Sallar-idi, / bari in gabatar muku da
Tabbatuwan Sallar-idin Tukun.....
"
"
TABBATUWAR SALLAR-IDI,
'YAN-UWA-
Sallolin idi, guda biyu (2) da musulunci
yake da su Sune kamar haka.....
* BABBAR-SALLAH
* QARAMAR- SALLAH
Dukkansu sun Tabbata a Sharia..
"
"
QARAMAR-SALLAH
Qaramar sallah, itace Sallar da ake
gabatarwa, a Ranar daya (1) ga watan-
(( Shawwal )) don Nuna Godiya ga Allah
(s.w.t) akan Baiwar da yayi mana na
Kammala Azumin Watan- (( Ramadan ))...
"
"
'YAN-UWA-
Wannan Sallar ta Tabbata A Cikin Alqur'ani
mai Girma....
Suratul- ( A'ala ) aya ta 14-15 ....
"
"
SANNAN
* imam Bukhariy da-
* imam Muslim bin hajjaj da-
* imam abu Dauda da-
* imam Nasa'i
Sun Rawaito daga ( Jabir ) (r.a) yace: .....
NA HALARCI SALLAR-IDI, TARE DA
MA'AIKIN ALLAH (s.a.w)..
"
"
HAKA SHIMA-
( Bara'u Dan Azib ) (r.a) yace: ...
MANZON ALLAH (s.a.w) yayi mana
huduba a Babban Sallar-idi, / bayan idar
da sallar idin...
"
"
DAN-HAKA-
Ataqaicen-Taqaitawa, Sallar idi, Sunnah ce
mai Qarfi...
"
"
SA'ANNA-
maza, da mata, / yaro, da Babba,
Harta mata masu yin ( Al'ada ) suma
Anbasu Izinin Zuwa Masallacin idi, Domin
Nuna Farinciki da Godiya Ga Allah (s.w.t)
"
"
TAMBAYA
MENE NE LADUBBAN ZUWA SALLAR-
IDI, ???
"
"
AMSA-
YANA DAGA CIKIN LADUBBAN ZUWA
MASALLACIN IDI, KAMAR HAKA....
* Ana so kaci abinci kafin ka tafi
masallacin-idi,/ amma a Qaramar-sallah
* Ana so ka Sanya Sabon kaya, idan kana
da iko,
* Ana so kafito Tsaf-tsaf, ka sanya Turare
* Ana so ka dinga yin wannan zikirin a
hanyarka ta Zuwa masallacin Idi, GASU
KAMR HAKA..
ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR
LA,ILAHA ILLALLAH
ALLAHU AKBAR
ALLAHU AKBAR
WALILLAHIL-HAMDU
anso kadiga maimaitawa har sai kaje
masallacin idin
* sallar-ida, / Ba'a yi mata Nafila, saidai
Tahiyyatul-masjid, shima sai in ka samu
Wuri a Cikin masallaci
AMMA'
Idan baka sami wuri a cikin masallaci ba,/
to Babu wata Nafila da Zaka yi, zaka zauna
ne kawai a harabar Masallaci ba tare da
yin Nafilaba
* Ana so ka Tsaya bayan an kammala
Sallar idi,/ Domin sauraren
(( Kudubah )) .....
"
"
'YAN-UWA-
WANNAN SHINE SAQON DA NIKE SO IN
KAWO MUKU