DL Media Connect

DL Media Connect Connecting Vision, Inspiring Progress

DL MEDIA CONNECT ✅️ Kyautar kudi Naira 500,000 daga HON. KABIRU LAWAL (jagaba) ga wasu membobi na kungiyar DL MEDIA CONN...
14/07/2026

DL MEDIA CONNECT ✅️

Kyautar kudi Naira 500,000 daga HON. KABIRU LAWAL (jagaba) ga wasu membobi na kungiyar DL MEDIA CONNECT dan dogaro da kansu.

Yayin kaddamar da wannan tallafi Hon.Kabiru Lawal jagaba wanda shine Uban wannan kungiya ya jaddada cewa kamar yanda wa yan nan s**a amfana akwai zai kara zakulo wasu daga cikin membobi har sai kowa ya Amfana insha Allah.

Ga rukuni na farkon wa yanda s**a amfana

1. Attahiru Musa
2. Sa'ad A Liman
3. Nafisat Autar Lugga
4. Hiskilu Musa Danjuma Boss
5. Abbakar Sahabi Gurusu

Allah ya sakamai da Alkhairi ya biya dukkan bukatu 🙏

14/07/2026

Allah ya bamu aron lokaci.
Mulki daidai da zamani
JAGABAN ZAMFARA

DL MEDIA CONNECT ✅️ Hon. Babangida bello kwatarkwashi, da Bello Hussaini finance sun amfana da kyautar motoci biyu daga ...
12/07/2026

DL MEDIA CONNECT ✅️

Hon. Babangida bello kwatarkwashi, da Bello Hussaini finance sun amfana da kyautar motoci biyu daga k***n Gwamna Hon. Kabir Lawal Jagaban Zamfara na farko, ta hannun Abdul Sidi.

Allah yasaka da mafificin alkhairinsa, Amin 🙏

DL MEDIA CONNECT ✅️ A yau Gwamnan Jihar ZAMFARA, Dauda Lawal, ya jagoranci bikin ƙaddamar da buɗe wurin haƙar ma’adanai ...
11/07/2026

DL MEDIA CONNECT ✅️

A yau Gwamnan Jihar ZAMFARA, Dauda Lawal, ya jagoranci bikin ƙaddamar da buɗe wurin haƙar ma’adanai a garin Boko, da ke Ƙaramar Hukumar Mulkin Zurmi.

Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunƙasa harkar ma’adanai tare da tabbatar da cewa ana gudanar da ita bisa doka da kuma amfanar al’ummar jihar.

Hon Jagaba 💥
11/07/2026

Hon Jagaba 💥

23/05/2026

KLM 📌

17/05/2026

Kabiru Lawal Jagaba 📌

DL MEDIA CONNECT ✅️ GWAMNA DAUDA LAWAL YA KAFa TARIHI YAYIN DA AKA YI JIRGIN HAJJI NA FARKO DAGA FILIN JIRGIN SAMA NA GU...
16/05/2026

DL MEDIA CONNECT ✅️

GWAMNA DAUDA LAWAL YA KAFa TARIHI YAYIN DA AKA YI JIRGIN HAJJI NA FARKO DAGA FILIN JIRGIN SAMA NA GUSAU

Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, ya kafa tarihi bayan tashin jirgin Hajji na farko daga Filin Jirgin Sama na Gusau zuwa ƙasar Saudiyya.

Jirgin farko na aikin Hajjin bana ya tashi ne a ranar Juma’a daga Filin Jirgin Sama na Gusau ɗauke da mahajjatan Zamfara guda 415 cikin jirgin Max Air mai lamba NGL270.
Adadin mahajjatan ya ƙunshi maza 288 da mata 127.

Yayin bikin ƙaddamar da tashin jirgin, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana farin cikinsa da godiyarsa ga Allah bisa ganin wannan gagarumin tarihi ya tabbata a jihar Zamfara.

Gwamnan ya bayyana aikin gina Filin Jirgin Sama na Gusau a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan tarihi da gwamnatinsa ta sa gaba.
“Ina matuƙar farin ciki a yau ganin mahajjatanmu suna tashi kai tsaye daga Filin Jirgin Sama na Gusau zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji na bana.

“Mutane da dama sun yi shakku kan cewa wannan aiki zai zama gaskiya, amma yau ga shi ya tabbata. Mun fara aikin gina wannan filin jirgin sama ne a ranar 18 ga Yuni, 2024.

15/05/2026

Thank you GDL

DL MEDIA CONNECT ✅️ Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da ƙarin albashin fansho ga masu ritaya na jiha da na ƙananan huku...
12/05/2026

DL MEDIA CONNECT ✅️

Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da ƙarin albashin fansho ga masu ritaya na jiha da na ƙananan hukumomi, domin inganta rayuwarsu da rage musu wahalhalun tsadar rayuwa.

Haka kuma, gwamnati za ta aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na ₦32,000 ga ‘yan fansho. Matakin na nufin aiwatar da cikakken ƙarin ₦32,000 bisa sabon tsarin mafi ƙarancin albashi

Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin wajen kula da walwalar ma’aikata da kuma masu ritaya a faɗin jihar.

Address

Zamfara
Gusau
880001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DL Media Connect posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share