12/09/2026
TIRKASHI: Wani magidanci a jihar Gombe ya yiwa matarshi saki uku saboda taje karbar tallafin da jam'iyyar APC ta raba.
Wani labari marar dadi ya faru jiya Laraba a jihar Gombe cikin anguwar Gabukka inda wani magidanci ya dawo gida bai samu iyalanshi ba kasancewar ta tafi wurin taron APC da aka dinga raba musu Atamfa da Naira 10k.
Ran mai gidan nata ya baci kasancewar sunyi dare a wurin taron saboda turmutsi-tsi da rikici na fada da aka yi ta samu a wurin taron har suke ta korafin an walakanta su.
Mun samu rahoton abunda ya faru a wurin 'yar uwar wacce maigidan nata ya sake ta, inda ta nemi da mu boye sunanta, ta kara mana bayani da cewa bayan dawowarta gida ta tarar da maigidan nata cikin fushi s**a kaure da cacar baki karshe yace yayi Mata saki uku.