Mubarak Barade

Mubarak Barade An kirkiri wannan shafin don wayar da kan al-umma akan shaanin addini da alamuran yau da kullum.

*Daga Cikin Ababen da ke Fito da Cikar Kamala, da Nagartar mace da Tarbiyar ta. itace Tsarin Shigar ta. kada kiyi Wasa d...
21/11/2025

*Daga Cikin Ababen da ke Fito da Cikar Kamala, da Nagartar mace da Tarbiyar ta. itace Tsarin Shigar ta. kada kiyi Wasa da Hakan*

✍🏼Abu itbaan

Da kaga wani dan bidi'a yana hayaniya kasa mai wannan hoton a comment section kayi shiru.
21/10/2025

Da kaga wani dan bidi'a yana hayaniya kasa mai wannan hoton a comment section kayi shiru.

14/10/2025
Daga ƙarshe dai “Sheikh Lawan Triumph” yazamo buldozar rosa bidi’a na afrika 🤔Babban abun mamaki shine; bayan ya babbaje...
13/10/2025

Daga ƙarshe dai “Sheikh Lawan Triumph” yazamo buldozar rosa bidi’a na afrika 🤔

Babban abun mamaki shine; bayan ya babbajesu da hujjoji, kuma sai ya nunamusu dattako tare da girmamasu amatsayinsu na dattawa

Yana cewa: Ni ɗanku ne idan nayi kuskure zaku iya sanar dani domin na gyara 😂

Karon farko a tarihin africa.

11/10/2025

Ka rinƙa tantance mutanen da zaka yi mu'amala da su a rayuwa musamman a irin wannan zamanin da muke ciki.

11/10/2025

Idan ka tara dukiya irin ta karuna ubanka ya canye yaci banza🤌
Inka kara tara wata ya canye ya kara cin wata banzar📌
Ko tashen batu babu.

10/10/2025

*Miƙa dukkan al’amurranka ga Allah, tare da samun natsuwa a kan hakan,*
*shi ne mataki mafi daɗi da mutum zai kai a rayuwa.♥️*

10/10/2025

Sheikh Bala Lau ya goyi bayan Sheikh Triumph, ya yi gargaɗi kan tsoma siyasa a lamarin addini.

Daga Jibwis Nigeria

Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iƙamatissunnah (JIBWIS) ta Tarayyar Najeriya, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cewa babu wata ƙungiya da ke tsayawa tsayin daka wajen kare martabar Manzon Allah (S.A.W) k**ar Ahlussunnah.

Babban shafin 'Jibwis Nigeria' ya ruwaito Shehin Malamin Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da Khudba a ranar Juma’a, 10 ga watan Oktoba 2025, a masallacin JIBWIS na ƙasa dake unguwar utako a birnin Abuja, inda ya ce tirka-tirkar da ke faruwa tsakanin Sheikh Lawal Abubakar Shu’aib Triumph da wasu Malaman Bid’ah a Kano darasi ne ga al’umma.

Sheikh Bala Lau ya jaddada cewa Ahlussunnah su ne masu kare gaskiya da bayyana ƙarya da ƴan Bid’ah ke jingina wa Manzon Allah (S.A.W). Yana mai cewa Da’awar Ahlussunnah tana gudana ne bisa tafarkin Musulunci, ƙarƙashin koyarwar Alƙur’ani da ingantattun Hadisan Annabi Muhammad (S.A.W). “Ahlussunnah su ne suke ƙalubalantar waɗanda ke alaƙanta wa Annabi abubuwan da addini bai zo da su ba, kuma wannan ne ke tabbatar da gaskiyarsu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa soyayya ga Manzon Allah ba ta tabbata cikin jahilci. Allah da Sahabbai ne s**a fi kowa son Annabi, kuma duk lokacin da Sahabbai s**a yi waƙa wadda ta zarce ƙa’ida, Annabi (S.A.W) da kansa yake hana su. “Dole ne mu nuna soyayya ga Manzon Allah ta hanyar bin shari’a, ba ta hanyar ɓatanci ko Bid'ah ba. Allah da Sahabbai ne s**a fi mu sanin matsayin Annabi, kuma sun fi kowa sanin yadda ake girmama shi,” in ji Sheikh Bala Lau.

Da yake tsokaci kan muhawarar da Sheikh Lawal Abubakar Shu’aib Triumph ke yi da Malaman Bid’ah a Kano, Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa Sheikh Triumph yana ƙoƙarin faɗakar da al’ummar Musulmi kan yadda wasu Malaman Bid’ah ke jingina karamomi ga shehunnan su, ta hanyar danganta su da Annabi (S.A.W). Ya ƙara da cewa: “Triumph yana son mutane su gane cewa Sahabbai ba su nuna soyayya ga Annabi da jahilci ba, sai dai bisa karantarwar Alƙur’ani da Hadisai.”

Shugaban JIBWIS ɗin ya kuma yi kira ga kwamiti na musamman da gwamnatin jihar Kano ta kafa da su yi adalci a binciken da suke gudanarwa kan Da’awar Sheikh Triumph da ta ƴan Bid’ah. “Idan an kira Sheikh Triumph, a tambaye shi hujjoji daga Alƙur’ani da Hadisai; idan an same su, to babu sauran jayayya. Kada gwamnati ta tsoma siyasa cikin lamuran da s**a shafi addini, domin k**a malamin Ahlussunnah saboda Da’awar Musulunci ba zai haifar da da mai ido ba,” in ji shi.

A ƙarshe, Sheikh Bala Lau ya ƙaryata furucin mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya ce k**a Abduljabbar Nasiru Kabara ra’ayin siyasa ne. Ya bayyana cewa k**a Abduljabbar haɗin kai ne tsakanin Malaman Izala, Dariƙar Tijjaniya da sauran ɓangarorin Sufaye, bisa hujjar cewa Da'awar shi ta saba da koyarwar Alƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (S.A.W). A ƙarshen Khudbar, Sheikh Bala Lau ya yi addu’ar samun haɗin kan al’ummar Musulmi da samun zaman lafiya a Najeriya da duniya baki ɗaya.

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=1263658785808316&id=100064926180538&mibextid=ZbWKwL

✍️ Ibrahim Baba Suleiman
DG Social Media
Jibwis Nigeria

10/10/2025

Saurara kaji kissar sarkin kano da mahaifin shehin malamin mu Imam Dr. Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa
Allah ya masa rahama

"kasan me Nakeso dakai Sharu Garzali, Tunda Committeen Shura Sunce Babu makawa Dole se anyi zaman nan da lawan kuyi haku...
10/10/2025

"kasan me Nakeso dakai Sharu Garzali, Tunda Committeen Shura Sunce Babu makawa Dole se anyi zaman nan da lawan kuyi hakuri Kuje a zauna din karku damu, Mu kuma munyi muku alkawari muna ganin alamun ze cinyeku Zamu tayarda rigima muce mudai koma meza ayi Lawan ya zagi annabi bazamu yarda ba kawai adau mataki"
Inji Shugaban Zawiyyar "Bahrun nada"
Lokacinda yake radawa Sharu garzali
Yanda Zasuyi nasara akan lawan Triumph🤣😂😂
Wuta 🔥

Fatima Haruna✍️

09/10/2025

Da'awar annabawa

Address

Gusau Zamfara State Of Nigeria
Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mubarak Barade posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category