Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Program GEEP

  • Home
  • Nigeria
  • Gusau
  • Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Program GEEP
Call Website Contact the organization

Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Program GEEP Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Program GEEP, Government Organization, Gusau.

Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Programme (GEEP) is a state government initiative designed to empower citizens economically by providing skills training, financial support, and business opportunities, particularly for youths, women,

29/09/2026

Maru Local Government

29/09/2026

Tsafe local government

29/09/2026

Zurmi Local Government

Ofishin Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Program GEEP  na farin cikin sanar da al’ummar Jihar Zamfar...
25/09/2026

Ofishin Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Program GEEP na farin cikin sanar da al’ummar Jihar Zamfara cewa shirin horar da matasa 7,000 maza da mata kan sana’o’i daban-daban, wanda Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, ya yi alkawari, yana ci gaba cikin nasara.

A halin yanzu, a cikin ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara, sama da kaso mai yawa daga cikin matasan da aka zaɓa sun fara samun horo a fannoni daban-daban na sana’o’i.

SANARWA GA WAƊANDA HAR YANZU BA SU FARA BA

Muna sanar da duk waɗanda aka zaɓa kuma aka tura musu saƙon gayyata cewa horon zai ci gaba a wasu cibiyoyin horo daga Litinin mai zuwa, In Sha Allah.

Muna kira gare su da su:

- Halarta a cibiyar horo akan lokaci;
- Nuna ƙwazo da jajircewa;
- Amfana da damar da aka ba su;
- Kuma su kasance masu bin ƙa’idojin horon.

Wannan shiri ba horo kawai ba ne; hanya ce ta ƙarfafa matasa, rage zaman banza, samar da sana’o’in dogaro da kai da kuma gina makoma mai inganci.

A matsayina na State Coordinator, GEEP Zamfara, ina tabbatar wa al’ummar jihar cewa ofishin GEEP zai ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da cewa an samar da ingantaccen horo da zai ba matasanmu damar dogaro da kansu tare da bayar da gudummawa wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Muna mika godiya ta musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, bisa hangen nesansa da ƙoƙarinsa na samar da damarmaki ga matasa.

Hajiya Sadiya Bello Barade
State Coordinator, GEEP Zamfara State

23/09/2026

Maru Local Government Training Centre

Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Program GEEP

📢 MUHIMMIYAR SANARWA – GEEP ZAMFARAAna sanar da dukkan waɗanda aka tura musu saƙon gayyata (Message) cewa Screening zai ...
20/09/2026

📢 MUHIMMIYAR SANARWA – GEEP ZAMFARA

Ana sanar da dukkan waɗanda aka tura musu saƙon gayyata (Message) cewa Screening zai ci gaba gobe, Litinin.

Muna kira ga duk waɗanda s**a samu saƙon da su tabbatar sun halarci screening a lokacin da aka tsara, tare da zuwa da abubuwan da aka buƙata.

⚠️ Lura: Wannan sanarwar ta shafi waɗanda s**a karɓi saƙon gayyata ne kawai.

18/09/2026

State Coordinator GEEP Zamfara State, Hon. Sadiya Bello Barade

ZAMFARA STATE GOVERNMENT ENTERPRISES AND EMPOWERMENT PROGRAM (GEEP)SANARWAA yau Litinin, 14/09/2026, an fara gudanar da ...
14/09/2026

ZAMFARA STATE GOVERNMENT ENTERPRISES AND EMPOWERMENT PROGRAM (GEEP)

SANARWA

A yau Litinin, 14/09/2026, an fara gudanar da horon sana’o’i a ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara.

Ana sanar da dukkan waɗanda aka tantance a kowace ƙaramar hukuma da su halarci cibiyar horon (Training Centre) da aka sanya musu, domin fara karɓar horon sana’o’i.

Wannan horo zai ba mahalarta damar samun ƙwarewa da ilimin sana’o’i, domin su samu damar dogaro da kansu da kuma inganta rayuwarsu.

Ana ƙara kira ga dukkan mahalarta da su kasance masu bin umarni, halartar horo a kan lokaci, tare da mai da hankali domin su amfana sosai da wannan dama.

Signed by:
Mustapha Lawal
Head of Media
Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Program GEEP

A ranar Laraba, 09 ga Satumba, 2026, State Coordinator na Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Programme...
11/09/2026

A ranar Laraba, 09 ga Satumba, 2026, State Coordinator na Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Programme (GEEP), Hajiya Sadiya Bello, ta gudanar da muhimmiyar ganawa da Training Managers (T.M) na ƙananan hukumomi 14 a ofishinta.

Ganawar ta mayar da hankali ne kan hanyoyin da za a ƙara inganta tafiyar da shirin GEEP, musamman wajen tabbatar da ingantaccen horo ga matasa maza da mata da ke cin gajiyar shirin.

A yayin ganawar, Hajiya Sadiya Bello ta jaddada wa Training Managers muhimmancin ƙara jajircewa wajen kulawa da kuma sa ido sosai kan malaman da ke koyar da matasan sana’o’in da aka tanadar musu.

Ta bayyana cewa manufar shirin ita ce tabbatar da cewa kowane matashi da ke cikin shirin ya samu ingantaccen horo, ƙwarewa da ilimin sana’ar da yake koya, domin bayan kammala horon ya samu damar dogaro da kansa, iyalansa da kuma al’ummarsa.

Ta ƙara da cewa, shirin GEEP ba horo ne kawai na koyon sana’a ba, illa wani muhimmin mataki ne na samar da makoma mai kyau ga matasan Zamfara, da kuma taimakawa wajen rage zaman banza da rashin aikin yi a jihar.

Hajiya Sadiya Bello ta kuma bayyana matuƙar godiyarta ga Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, bisa irin goyon baya da kulawar da yake bai wa shirin GEEP, da kuma ƙoƙarinsa na samar da damammaki ga matasa da mata a faɗin jihar.

A matsayinta na State Coordinator, Hajiya Sadiya Bello ta tabbatar wa al’ummar Jihar Zamfara cewa za ta ci gaba da yin aiki tukuru tare da tabbatar da gaskiya, tsari da inganci, domin cimma manufofin shirin.

Ta bayyana yakinin cewa idan aka bai wa matasan jihar dama tare da ingantaccen horo, za su iya dogaro da kansu tare da taka muhimmiyar rawa wajen gina Zamfara mai ƙarfi da wadata.

Allah Ya taimaki Jihar Zamfara, Ya kuma ci gaba da yi wa Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara jagora wajen tafiyar da jihar.

— OFFICE OF THE MEDIA
Zamfara State GEEP

We were pleased to receive the visiting Chairman of the Presidential CNG Initiative (Pi-CNG), His Excellency Ismail Ahma...
11/09/2026

We were pleased to receive the visiting Chairman of the Presidential CNG Initiative (Pi-CNG), His Excellency Ismail Ahmad, during his visit to Zamfara State.

The visit was aimed at assessing and witnessing Zamfara State’s commitment to the Pi-CNG initiative under the visionary leadership of His Excellency, Dr. Dauda Lawal, Executive Governor of Zamfara State.

Zamfara remains committed to supporting initiatives that promote economic empowerment, reduce the cost of living, and improve the welfare of our people.

We appreciate the Chairman and his team for the visit and look forward to greater collaboration for the benefit of the people of Zamfara State.

Address

Gusau

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Program GEEP posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Zamfara State Government Enterprises and Empowerment Program GEEP:

Shortcuts

Share