08/09/2025
MAULIDI DA JERIN GWANO
Maulidi kalma ce da ke nufin bikin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW).
A wannan rana, ana gudanar da abubuwa kamar karanta tarihin rayuwarsa, rera waƙoƙin yabonsa, da gabatar da wa'azi domin tunatar da mutane su bi tafarkinsa na gari.
Babbar manufar Maulidi ita ce ƙara ƙauna da girmama Annabi (SAW) a cikin zukatan Musulmi.
A abinda yake a bayyane shine, kowace al'umma na da salon yadda take gudanar da bikin Maulidi. Wasu s**an yi shi ta hanyar taron karatu da wa'azi kaɗai. Wasu kuma s**an haɗa da rera baitocin yabo ga Annabi (SAW), wato rera qasidu. A wasu wuraren kuwa, ana gudanar da Maulidin ne tare da al'adu na nuna farin ciki da shagali.
Daga cikin hanyoyin da wasu ke nuna murnarsu a lokacin Maulidi har da JERIN GWANO. Wannan wani nau'i ne na tattaki ko zagayen gari da ake yi cikin nishaɗi da rera waƙoƙin yabon Annabi don bayyana farin ciki da haihuwarsa. Duk da cewa jerin gwano ba ya cikin ainihin tushen yadda ake gudanar Maulidi a baya, amma a yanzu hanya ce da wasu al'ummu s**a zaɓa don gudanar da nasu bikin.
A taƙaice, Maulidi biki ne da ya shafi tunawa da haihuwwar Annabi (SAW), amma hanyoyin gudanar da shi sun bambanta bisa ga al'ada da fahimtar kowace al'umma.
Jerin gwano kuma yana ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu ke amfani da su wajen nuna murnar wannan rana.
Allah sa mu dace!
~ Nasiru Saleh✍️