22/05/2026
"Allah SWT yana cewa:- Lalle Allah yana umurni da adalci da kyautatawa..."
Suratun Nahl 16:90
A wannan ranar Juma’a mai albarka, mu tuna cewa siyasa ba faɗa ba ce, hidima ce ga al’umma. Shugabanci na gaskiya yana buƙatar haƙuri, amana, da tausayi ga jama’a.
Al’ummar Gombe Ta Arewa na buƙatar shugabanni masu tsoron Allah, masu gaskiya, da masu aiki domin cigaban matasa, mata, da ƙasa baki ɗaya.
Kada mu bari bambancin siyasa ya raba kanmu. Mu yi siyasa cikin mutunci, zaman lafiya, da girmama juna domin cigaban Gombe Ta Arewa.
Allah Ya zaɓa mana shugabanni nagari, Ya haɗa kan al’ummar mu, Ya ba mu zaman lafiya da ci gaba.
JUMMU’AT MUBARAK 🤲
,✍️