08/02/2025
A Yau Asabar 08/02/2025 Shugaban Karamar Hukamar Bade Hon. Ibrahim Babagana (Yurema)Yakarbi Bakwancin tawagar Gwamnatin Jihar Yobe karkashin jagorancin Mai bawa Gwamna shawara akan kiwon lafiya da bincike, Dr. Mahmud Maina Bukar, a bisa umarnin Gwamna, sun kaddamar da shirin kawo karshen ciwon ƙoɗa a yankin karamar hukumar Bade.
Tawagar, wanda take ɗauke da kwararrun likitoci da masana daga fannonin kiwon lafiya, cibiyoyin bincike akan harkokin kiwon lafiya daga sassan Najeria daban-daban sun kaddamar da shirin gwaje-gwaje na kwanaki goma har sai an gano tushen cutar tare da maganin ta.
A madadin Gwamnatin Mai Mala Buni, CON, Dr. Mahmud Maina Bukar ya bayyana irin damuwar da mai girma Gwamna yake yi akan wannan cutar, ya jajanta wa karamar hukumar Bade, sannan yayi alwashin da yardar Allah za'a gano bakin zaren.
A cikin jawaban shugaban karamar hukumar Bade, Hon. Babagana Ibrahim, ya bayyana cewa shima wannan cutar tana tayar masa da hankali -- domin a dangin su kaɗai sun rasa rayuka har shida sanadiyyar ciwon ƙoɗa. Daga karshe, yayi alwashin karamar hukumar sa zata bada haɗin kai kamar yadda ake bukata.
Muna Addu'an Ubangiji Allah Yakawo Karshan Wannan Annobar.
Signed: SSA ON MEDIA AND PUBLICITY TO THE EXECUTIVE CHAIRMAN BADE LOCAL GOVERNMENT COUNCIL