Gadaka APC Youth Dev. forum

Gadaka APC Youth Dev. forum Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gadaka APC Youth Dev. forum, Political organisation, Gadaka Fika Local Government, Gadaka.

GWAMNA BUNI YA GINA CIBIYOYIN KIWON LAFIYA 148 DA HANYOYI SAMA DA KILOMITA 500 CIKIN SHEKARU BAKWAI – MUKADDASHIN SAKATA...
29/05/2026

GWAMNA BUNI YA GINA CIBIYOYIN KIWON LAFIYA 148 DA HANYOYI SAMA DA KILOMITA 500 CIKIN SHEKARU BAKWAI – MUKADDASHIN SAKATAREN GWAMNATIN JIHAR YOBE

Gwamnatin Jihar Yobe ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta samu gagarumar nasara a bangarorin kiwon lafiya, gine-ginen hanyoyi, tsaro, ilimi da bunkasa tattalin arziki cikin shekaru bakwai da s**a gabata, inda ta gina cibiyoyin kiwon lafiya guda 148 tare da hanyoyi sama da kilomita 500 a sassan jihar.

Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Dakta Mohammed Goje (FRSPH), ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin taron manema labarai da aka gudanar a ofishin SSG da ke Damaturu domin bikin cika shekaru bakwai na gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni.

Dakta Goje ya bayyana wadannan nasarori a matsayin hujja karara da ke nuna kudurin gwamnatin wajen inganta rayuwar al’umma ta hanyar zuba jari a muhimman bangarori da kuma aiwatar da manufofin da s**a shafi jama’a kai tsaye.

A cewarsa, tun bayan hawan gwamnatin a shekarar 2019, gwamnatin Gwamna Buni ta mayar da hankali wajen samar da zaman lafiya, karfafa cibiyoyin gwamnati, bunkasa ilimin jama’a, fadada ayyukan more rayuwa da kuma farfado da tattalin arziki.

Ya kara da cewa gwamnatin ta kammala cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda 143 daga cikin cibiyoyi 178 da aka tsara a dukkan mazabun siyasar jihar. Haka kuma ta inganta manyan asibitoci guda biyar zuwa matakin kwararrun asibitoci (Specialist Hospitals), tare da kafa cibiyoyin kula da uwa da jariri na zamani domin kara inganta harkokin lafiya.

Mukaddashin SSG ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta gina tare da gyara hanyoyi sama da kilomita 500 a fadin jihar Yobe, ciki har da hanyoyin cikin birane da na hada al’ummomi, domin saukaka zirga-zirga, kasuwanci, harkokin noma da kuma inganta alakar yankunan karkara.

Daga cikin manyan ayyukan da ya lissafo akwai aikin gada ta sama da ta karkashin kasa da ake ginawa a Damaturu, hanyar Damaturu zuwa Kalallawa, hanyar Damaturu zuwa Gambir, hanyar Waziri Ibrahim Bypass da sauran muhimman hanyoyi da ake aiwatarwa a yankunan sanatoci uku na jihar.

Dakta Goje ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a bangarorin tsaro, ilimi, noma, gidaje, samar da ruwa da wutar lantarki a karkara, yana mai cewa gwamnatin ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya tare da hanzarta ayyukan ci gaba a fadin jihar.

Ya kara da cewa sama da dalibai 48,000 ne ke cin gajiyar shirye-shiryen tallafin karatu na gwamnatin jihar, yayin da dubban matasa da mata s**a amfana da shirye-shiryen tallafawa da karfafa tattalin arzikinsu.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Dakta Goje ya tabbatar da cewa gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni za ta ci gaba da kare nasarorin da aka samu cikin shekaru bakwai da s**a gabata tare da kara gina Jihar Yobe mai ci gaba, wadata da dorewar zaman lafiya.

– Umaru Sale Bebeji

SAKON BARKA DA SALLAH EID KABEER Hon. Yunusa Abare Osa ( Secretary APC Fika L.G )Yana Mika Sakon Barka da Sallar Layya (...
27/05/2026

SAKON BARKA DA SALLAH EID KABEER

Hon. Yunusa Abare Osa ( Secretary APC Fika L.G )

Yana Mika Sakon Barka da Sallar Layya (Eid Kabeer) ga daukacin Al’ummar Musulman duniya baki daya.

Barka da Sallah, Allah ya maimata mana da Alkhairi da nisan kwana

Ubangijin Allah Ya Karɓi Ibadunmu, Ya sanya mana albarka, zaman lafiya da ci gaban ƙasa. Ameen Yaa Rabbil Alamin.

GADAKA APC MEDIA TEAM
Umaru Sale Bebeji
27/05/2026

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara gudanar da tantancewar ‘yan takarar da ke neman tikitin shiga Majalisa...
09/05/2026

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara gudanar da tantancewar ‘yan takarar da ke neman tikitin shiga Majalisar Tarayya gabanin zabukan fidda gwani na jam’iyyar.

Za a gudanar da tantancewar masu neman kujerar Sanata a Abuja Continental Hotel, yayin da masu neman kujerar Majalisar Wakilai za a tantance su a Treasures Suites & Conferences.

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa wannan tsari na daga cikin shirye-shiryen tabbatar da gaskiya, adalci da ingancin ‘yan takarar da za su shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar.

GADAKA APC MEDIA TEAM CREW

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. (Dr) Mai Mala Buni, ya yi ta’aziyya ga Sarkin Fune kan hatsarin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka...
04/05/2026

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. (Dr) Mai Mala Buni, ya yi ta’aziyya ga Sarkin Fune kan hatsarin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka yayin sallar Juma’a.

Gwamna Mai Mala Buni ya mika sakon ta’aziyya ga Sarkin Fune, Alhaji Mai Saleh Idriss Ibn Usman, da al’ummar Damagum bisa wannan mummunan hatsari da ya yi sanadiyyar rasa rayuka yayin sallar Juma’a.

A madadin gwamnan, mataimakinsa Hon. Idi Barde Gubana ya tabbatar da tallafin gaggawa, ciki har da magani kyauta ga wadanda s**a jikkata da kuma taimakon kudi ga iyalan da abin ya shafa.

Ziyarar ta samu halartar manyan jami’an gwamnati da shugabannin tsaro, abin da ya nuna hadin kai da tausayi a wannan lokaci na jimami.

Gwamnatin Jihar ta kuma jaddada muhimmancin tsaro da daukar matakan rigakafi domin kaucewa irin wannan masifa a nan gaba.

DA DUMI-DUMI: Tsohon Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Yamaltu Deba Hon Shuaibu Umar Galadima, ya fice daga jam'iyyar A...
04/05/2026

DA DUMI-DUMI: Tsohon Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Yamaltu Deba Hon Shuaibu Umar Galadima, ya fice daga jam'iyyar APC.

Shugabannin mu na Jihar Yobe Cikin Fararen Kaya Allah ya dafa Muku Idan wannan Hoton ya Burgeka ka Danna min Like Kobe B...
04/05/2026

Shugabannin mu na Jihar Yobe Cikin Fararen Kaya

Allah ya dafa Muku

Idan wannan Hoton ya Burgeka ka Danna min Like
Kobe Burgekabama Inaso kamin Like
Anatare.

SIYASA 2027: Hon. Muhammed Ali Tanimu Ya Saya Fom Din Takarar Majalisar JiharHon. Muhammed Ali Tanimu, mai wakiltar Fika...
04/05/2026

SIYASA 2027: Hon. Muhammed Ali Tanimu Ya Saya Fom Din Takarar Majalisar Jihar

Hon. Muhammed Ali Tanimu, mai wakiltar Fika ta Gabas, ya shiga jerin ‘yan takarar kujerar majalisar jihar a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan ya saya fom din takara.

GADAKA APC MEDIA TEAM

Sabon SSG na Jihar Yobe ya k**a aikiA yau Litinin, Dr. Mohammed Goje ya fara gudanar da aikinsa a matsayin Mukaddashin S...
04/05/2026

Sabon SSG na Jihar Yobe ya k**a aiki

A yau Litinin, Dr. Mohammed Goje ya fara gudanar da aikinsa a matsayin Mukaddashin Secretary to the State Government (SSG) na Jihar Yobe. Ya shiga ofis dinsa tare da rakiyar ’yan uwa da abokan arziki, inda aka tarbe shi cikin farin ciki da fatan alheri.

Shigarsa ofis din ya biyo bayan nadin da aka yi masa a matsayin sabon SSG, kuma ana sa ran zai taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati a jihar.

GADAKA APC MEDIA TEAM CREW

Hon. Aliyu Mohammed SK ya sayi fom ɗin takarar majalisar tarayya  Mai neman kujerar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar F...
01/05/2026

Hon. Aliyu Mohammed SK ya sayi fom ɗin takarar majalisar tarayya

Mai neman kujerar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Fika da Fune, Hon. Aliyu Mohammed SK (Dan Majen Gudi), ya sayi fom na tsayawa takarar kujerar majalisar tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

GADAKA APC YOUTH DEV FORUM

𝗦𝗔𝗞𝗢𝗡 𝗧𝗔𝗬𝗔 𝗠𝗨𝗥𝗡𝗔!!!Mai girma 𝗛𝗼𝗻. 𝗬𝘂𝘀𝘂𝗳 𝗬𝘂𝗻𝘂𝘀𝗮 𝗕𝗮𝗯𝗮 (Zannah Dujiman Gudi) Dan takarar Dan Majalisar Jiha Mai wakiltan Ng...
01/05/2026

𝗦𝗔𝗞𝗢𝗡 𝗧𝗔𝗬𝗔 𝗠𝗨𝗥𝗡𝗔!!!

Mai girma 𝗛𝗼𝗻. 𝗬𝘂𝘀𝘂𝗳 𝗬𝘂𝗻𝘂𝘀𝗮 𝗕𝗮𝗯𝗮 (Zannah Dujiman Gudi) Dan takarar Dan Majalisar Jiha Mai wakiltan Ngoya/Ngeji Constuency.

Yana taya 𝗗𝗿. 𝗠𝗼𝗵𝗮𝗺𝗺𝗲𝗱 𝗚𝗼𝗷𝗲 Samun Sabon Mukami a matsayin Magatakarda Gobnaji na Jihar yobe State (𝗦𝗦𝗚-𝗬𝗢𝗕𝗘 𝗦𝗧𝗔𝗧𝗘)

Ubangijin Allah yasa hakan mafi Alkhairi ne a gareshi, yayi riko da 𝗵𝗮𝗻𝗻𝗮𝘆𝗲𝗻𝘀𝗮 Wajen ciyar da Jihar yobe State Wajen kawo 𝗰𝗶𝗴𝗮𝗯𝗮 Jiha Allahumma Ameen.

𝗛.𝗬.𝗬 𝗠𝗘𝗗𝗜𝗔 𝗧𝗘𝗔𝗠 𝗖𝗥𝗘𝗪
Umaru Sale Bebeji
01/05/2026

Address

Gadaka Fika Local Government
Gadaka
2007

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gadaka APC Youth Dev. forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share