Katsina State Hisbah Board Dutsin-Ma Division

Katsina State Hisbah Board Dutsin-Ma Division For The Protection & Upliftment Shari'a In Katsina State

14/06/2026

Live streaming of Wa'azin Goron Sallah

HUKUMAR HISBAH RESHEN KARAMAR HUKUMAR DUTSIN-MA TA SAMU NASARAR K**A WASU MATASA BIYU DA AKE ZARGIN SUNA AIKATA BADALAHu...
14/06/2026

HUKUMAR HISBAH RESHEN KARAMAR HUKUMAR DUTSIN-MA TA SAMU NASARAR K**A WASU MATASA BIYU DA AKE ZARGIN SUNA AIKATA BADALA

Hukumar Hisbah Reshen Karamar Hukumar Dutsin-ma, ƙarƙashin jagorancin Kwamanda Shafi'u Ibrahim, ta samu nasarar k**a wani saurayi tare da wata budurwa a wani gida da ke bayan Motel Dutsin-ma, inda ake zargin suna aikata badala.

Wannan nasara ta samu ne bayan da Hukumar ta karɓi ƙorafe-ƙorafe daga wasu mazauna yankin masu kishin tarbiyya da zaman lafiya, waɗanda s**a bayyana damuwarsu kan yadda ake gudanar da wasu ayyuka da s**a saɓa wa ɗabi'a a cikin gidan.

Bayan samun bayanan sirri da kuma gudanar da bincike, Hukumar ta tura jami'anta domin tabbatar da sahihancin rahoton. Samamen wanda OC G&C Haruna M. ya jagoranta tare da wasu jami'an Hukumar Hisbah ya kai ga cafke waɗanda ake zargin a wurin.

Binciken farko ya nuna cewa ana amfani da wasu gidajen da ɗalibai ke haya wajen aikata ayyukan da s**a saɓa wa tarbiyya da koyarwar addini, musamman a lokutan hutun makaranta da dakunan kan kasance babu mazauna na asali.

Hukumar Hisbah ta bayyana damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da irin waɗannan wurare wajen gudanar da ayyukan da ke iya lalata tarbiyyar al'umma, tare da jawo matsaloli ga zaman lafiya da tsaron unguwanni.

A yayin da Hukumar ke ci gaba da bincike kan lamarin, ta sake kira ga iyaye, masu gidaje, shugabannin al'umma da mazauna yankunan da ke kusa da dakunan kwanan ɗalibai da su kasance masu sa ido tare da gaggauta sanar da Hukumar duk wani abu da ya yi k**a da aikata laifi ko rashin ɗa'a.

Hukumar ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaƙi da duk wani nau'in miyagun ɗabi'u da ke barazana ga tarbiyya da kyawawan halaye a cikin al'umma, tare da tabbatar da bin doka da oda a faɗin Karamar Hukumar Dutsin-ma.

BYAREEMA
KTSHB DUTSIN-MA DIVISION

11/06/2026
Hukumar Hisbah Reshen Karamar Hukumar Dutsin-ma, ƙarƙashin jagorancin Kwamanda Shafi'u Ibrahim, ta samu nasarar k**a wan...
03/06/2026

Hukumar Hisbah Reshen Karamar Hukumar Dutsin-ma, ƙarƙashin jagorancin Kwamanda Shafi'u Ibrahim, ta samu nasarar k**a wani matashi mai shekaru 14 da ake zargi da yi wa wata yarinya mai shekaru 3 fyade.

BYAREEMA tare da Jami'an Hukumar Sun Samu Nasarar K**a Wanda ake zargin, Mahi Yahaya, ya amsa zargin yayin tambayoyin farko, inda ya bayyana cewa ya kira yarinyar, ya saya mata gyada, sannan ya kai ta wani ɗaki da ke gidan mahaifinsa.

Bayan samun wannan rahoto da kuma gudanar da binciken farko, Hukumar Hisbah ta miƙa wanda ake zargin tare da yarinyar ga hedikwatar 'Yan Sanda ta Karamar Hukumar Dutsin-ma domin ci gaba da gudanar da cikakken bincike da kuma ɗaukar matakan doka da s**a dace.

Hukumar Hisbah tana kira ga iyaye da masu kula da yara da su ƙara sanya ido tare da kula da 'ya'yansu domin kare su daga duk wani nau'in cin zarafi da barazana ga lafiyarsu da makomarsu.

Allah Ya Kara Kare Mana Zuri'armu Ya Shirya Masu Aikata Wa Ya Kare Mu Daga Aikata Aikin Da Na Sani.
Amin

BYAREEMA
O.C ICT
KTSHB DUTSIN-MA DIVISION

Hukumar Hisbah Reshen Karamar Hukumar Dutsin-ma, ƙarƙashin jagorancin Kwamanda Shafi'u Ibrahim, ta samu nasarar k**a wat...
03/06/2026

Hukumar Hisbah Reshen Karamar Hukumar Dutsin-ma, ƙarƙashin jagorancin Kwamanda Shafi'u Ibrahim, ta samu nasarar k**a wata matar aure da Wani Saurayi Suna Kokarin Aikata Badala a Darawa Dutsin-ma.

Binciken da Hukumar ta gudanar ya biyo bayan bayanan sirri da ta samu kan yadda wasu matasa ke amfani da wasu dakunan Dalibai Dake Darawa wajen aikata abubuwan da s**a saɓa wa koyarwar addinin Musulunci da kyawawan ɗabi'u.

Bayan gudanar da bincike, an gano cewa matar ta daɗe tana aikata wannan ɗabi'a ta cin amanar aurenta ba tare da mijinta ya sani ba.
Abin takaici, duk da cewa ba ta rasa abin ci da sha ba, ba ta rasa sutura ba, kuma ba ta rasa kulawa ba, saida ta faɗa cikin wannan babban kuskure wanda zai iya jawo fushin Allah Madaukakin Sarki.

Ya ku 'yan uwa Musulmi!
Mu ji tsoron Allah a cikin sirri da bayyane. Mu tuna cewa rayuwar duniya mai wucewa ce, kuma kowannenmu zai tsaya gaban Mahaliccinsa domin hisabi.

Allah Ya tsare mu daga faɗawa cikin fitintinu, Ya shiryar da masu kuskure, Ya sa mu kasance cikin bayinsa na gari.

"Kada ku kusanci zina; lalle ita alfasha ce kuma mummunar hanya ce."
— Suratul Isra'i, Aya ta 32.

BYAREEMA
KTSHB DUTSIN-MA DIVISION

𝗛𝗨𝗞𝗨𝗠𝗔𝗥 𝗛𝗜𝗦𝗕𝗔𝗛 𝗧𝗔 𝗗𝗨𝗧𝗦𝗜𝗡-𝗠𝗔 𝗧𝗔 𝗞𝗔𝗠𝗔 𝗪𝗔𝗡𝗜 𝗠𝗨𝗧𝗨𝗠 𝗗𝗔 𝗔𝗞𝗘 𝗭𝗔𝗥𝗚𝗜𝗡 𝗔𝗜𝗞𝗔𝗧𝗔 𝗙𝗬𝗔𝗗𝗘A ranar Laraba 28/05/2026, Hukumar Hisbah Reshe...
29/05/2026

𝗛𝗨𝗞𝗨𝗠𝗔𝗥 𝗛𝗜𝗦𝗕𝗔𝗛 𝗧𝗔 𝗗𝗨𝗧𝗦𝗜𝗡-𝗠𝗔 𝗧𝗔 𝗞𝗔𝗠𝗔 𝗪𝗔𝗡𝗜 𝗠𝗨𝗧𝗨𝗠 𝗗𝗔 𝗔𝗞𝗘 𝗭𝗔𝗥𝗚𝗜𝗡 𝗔𝗜𝗞𝗔𝗧𝗔 𝗙𝗬𝗔𝗗𝗘

A ranar Laraba 28/05/2026, Hukumar Hisbah Reshen Karamar Hukumar Dutsin-ma karkashin jagorancin Kwamanda Shafi’u Ibrahim ta samu nasarar k**a wani mutum da ake zargi da aikata fyade ga wata yarinya mai shekara 11, bayan rahotannin da mazauna unguwar Bakin Sabuwar Kasuwa s**a bayar.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen unguwar sun k**a wanda ake zargin tare da tsare shi kafin jami’an Hisbah s**a isa wurin domin karɓarsa da gudanar da bincike.

Hukumar Hisbah ta Samu Mutumen Cikin Maye Giya, Tare da Wandonsa Hannu.

Hukumar Hisbah ta yaba da hadin kan al’umma wajen taimakawa jami’an tsaro, tare da kara kira ga iyaye da su sanya ido sosai kan yayansu musamman a wannan lokaci na gudanar da bukukuwan Sallah.

BYAREEMA
KTSHB DUTSIN-MA DIVISION

27/05/2026

𝘏𝘶𝘥𝘶𝘣𝘢𝘳 𝘐𝘥𝘪𝘯 𝘓𝘢𝘺𝘺𝘢 𝘔𝘢𝘪 𝘈𝘭𝘣𝘢𝘳𝘳𝘬𝘢
𝘎𝗮𝗯𝘢𝘵𝘢𝘳𝘸𝘢:-𝘚𝘩𝘦𝘪𝘬𝘩 𝘋𝘳. 𝘐𝘭𝘺𝘢𝘴 𝘐𝘮𝘢𝘮 𝘙𝘢𝘥𝘥𝘢.
𝗞𝗧𝗦𝗛𝗕 𝗕𝗢𝗔𝗥𝗗 𝗠𝗘𝗠𝗕𝗘𝗥 {𝗞𝗔𝗧𝗦𝗜𝗡𝗔 𝗭𝗢𝗡𝗘}
@ 𝗠𝗔𝗦𝗔𝗟𝗟𝗔𝗖𝗜𝗡 𝗜𝗗𝗜 𝗡𝗔 𝗚.𝗥.𝗔 𝗗𝗨𝗧𝗦𝗜𝗡-𝗠A

Address

Ibrahim Shehu Shema Way, Old Hospital, Opposite Yandaka Primary School Dutsin-Ma Close To J. N. I Office
Dutsin-Ma
821101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina State Hisbah Board Dutsin-Ma Division posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Katsina State Hisbah Board Dutsin-Ma Division:

Shortcuts

Share