28/03/2026
Hukumar Hisbah Reshen Karamar Hukumar Dutsin-ma Karkashin Jagorancin Kwamanda Shafi'u Ibrahim ta Samu Nasarar K**a Wani Mutum Mai Shekara 45 Da Yayi Yunkurin Yi Ma Wata Yarinya Mai Shekara 10 Fyade.
Jami'an Hukumar Hisbah Na Yanki Dake Faguwa Tare Da Hadin Guiwa da Vigilante Na Faguwa Sune Wanda S**a K**a tare da Hannanta Wannan Mutunen Hannun Hukumar Hisbah a Karamar Hukumar Dutsin-ma.
Asirinshi Ya Tonu Sakamakon Kururuwa da Yarinyar Tayi.
Bayan Dogon Bincike Hukumar Hisbah ta Gano Cewa Wannan Ba Shine Karo Na Farko ba, Akwai lokacin Da Ya Sameta Da Tsakiyar Dare Yayi Mata Fyade, Kuma Yayi Mata Barazana Cewa Idan Ta Sanar Ma Wani Sai Ya Illata ta.
Wanda Ya Aikata Fyaden Ya Kasance Abokin Mahaifin Yarinyar ne,
Bayan Zantawa Da Mahaifin Yarinyar Yace Bai Taba Zaton Zaici Amanarsa Haka Ba.
Allah Ya Sa Mufi Karfin Zukatanmu, Ya Kare Mu Daga Fadawa Mummunar Kaddara, Ya Kara Kare Mu Daga Aikata Dana Sani, Allah Ya Kara Shirya Mu Baki Daya Zuri'ar Manzon Allah (S.A.W)
Amin
Dr. Aminu Usman Abu Ammar Ph.D katsina
Dr. Dikko Umaru Radda
Arewa Updates
Katsina Post
โ๏ธ๐๐ฌ๐๐ฅ๐๐๐ ๐
๐ข.๐ ๐๐๐ง
๐๐ง๐ฆ๐๐ ๐๐จ๐ง๐ฆ๐๐ก-๐ ๐ ๐๐๐ฉ๐๐ฆ๐๐ข๐ก