Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa

Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa Barka da Zuwa Shafin Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa!

Gwamna Malam Umar Namadi a yau ya halarci bikin ɗaura auren ma'aurata 1,500 da Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauki nauyi ta ha...
08/08/2026

Gwamna Malam Umar Namadi a yau ya halarci bikin ɗaura auren ma'aurata 1,500 da Gwamnatin Jihar Kano ta ɗauki nauyi ta hannun Hukumar Hisbah ta Jihar Kano. An gudanar da bikin ne a harabar Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Bikin ya samu halartar manyan baƙi da s**a haɗa da Gwamnan Jihar Katsina, Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, manyan malaman addinin Musulunci (Ulama) da sauran manyan baki.

Gwamna Namadi ya samu rakiyar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin, zuwa wajen bikin.

Gwamna Malam Umar A. Namadi a ranar Juma'a ya karɓi rahoton gudanar da Aikin Hajjin shekarar 1447AH (2026AD) daga Amirul...
07/08/2026

Gwamna Malam Umar A. Namadi a ranar Juma'a ya karɓi rahoton gudanar da Aikin Hajjin shekarar 1447AH (2026AD) daga Amirul Hajj, Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Nuhu Muhammad Sanusi, a Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa da ke Dutse.

A yayin karɓar rahoton, Gwamnan ya bayyana cewa aikin Hajjin bana ya kasance ɗaya daga cikin mafi nasara a tarihin Jihar Jigawa. Ya yaba wa Amirul Hajj, Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, da sauran jami'an da s**a taka rawa wajen gudanar da aikin cikin tsari da nasara.

Gwamna Namadi ya kuma sanar da cewa gwamnatin jihar za ta fara aikin gina sansanin Alhazai na dindindin (Permanent Hajj Camp) kafin ƙarshen wannan shekara, domin ƙara inganta shirye-shiryen aikin Hajji da walwalar alhazan jihar a shekaru masu zuwa.

Gwamna Malam Umar Namadi a yau ya jagoranci bikin yaye matasa 928 'yan asalin Jihar Jigawa da s**a samu horo kan ilmin k...
06/08/2026

Gwamna Malam Umar Namadi a yau ya jagoranci bikin yaye matasa 928 'yan asalin Jihar Jigawa da s**a samu horo kan ilmin kwamputa da fasahar sadarwa ta zamani, a wani biki da aka gudanar a Babban ɗakin taro na Banquet Hall da ke Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa, a Dutse.

An horar da matasan ne a ƙarƙashin Shirin IDEAS da ya samu tallafin Bankin Duniya, wanda Ma'aikatar Ilimi ta Tarayya ke da ido akan sa, yayin da Jami'ar Baze da ke Abuja ta gudanar da horon.

Bikin ya kuma haɗa da ƙaddamar da Shafin intanet da zai bada damar Bibiyar BBC yadd gwamnatin jihar Jigawa ke Aiwatar da Ajandar ta Mai kudurori 12 ta Hanyar Fasahar Zamani (12-Point Agenda Digital Performance Portal), wanda aka ƙirƙira domin ƙarfafa gaskiya a aikin gwamnati, riƙon amana, da kuma bai wa al'umma damar bibiyar ayyukan gwamnati.

06/08/2026
A yau da rana, Gwamna Malam Umar A. Namadi ya karɓi lambar yabo ta ƙwarewa daga Ƙungiyar Ma'aikatan Shagunan Tallafin Ra...
03/08/2026

A yau da rana, Gwamna Malam Umar A. Namadi ya karɓi lambar yabo ta ƙwarewa daga Ƙungiyar Ma'aikatan Shagunan Tallafin Rage Raɗaɗin Rayuwa (Association of Palliative Shop Workers).

Ƙungiyar ta karrama Gwamnan ne bisa irin nagartaccen jagoranci da kuma shirye-shiryen ci gaba da gwamnatin sa ke aiwatarwa domin inganta walwala da rayuwar al'ummar Jihar Jigawa.

Lambar yabon ta ƙara nuna yadda ƙungiyoyi da al'umma ke ci gaba da yaba wa ƙoƙarin gwamnatin Malam Umar Namadi wajen gudanar da mulki mai mayar da hankali kan jin daɗin jama'a da ci gaban jihar.

Gwamna Malam Umar A. Namadi a yau ya karɓi Takardar Manufofin Shirin Buɗaɗɗiyar Gwamnati (Open Government Partnership – ...
03/08/2026

Gwamna Malam Umar A. Namadi a yau ya karɓi Takardar Manufofin Shirin Buɗaɗɗiyar Gwamnati (Open Government Partnership – OGP) ta Jihar Jigawa a yayin zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar.

Mataimakin Gwamnan Jihar Engr. Aminu Usman, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Jagorancin Shirin OGP na Jihar Jigawa, ne ya miƙa takardar ga Gwamna Namadi.

Takardar manufofin na da nufin ƙarfafa gaskiya, riƙon amana, buɗaɗɗen tsarin mulki, da kuma ƙara haɗin kan al'umma a harkokin gudanar da gwamnati, a wani ɓangare na ƙudurin gwamnatin Malam Umar Namadi na inganta shugabanci nagari da gudanar da mulki cikin gaskiya da adalci.

Gwamna Malam Umar A. Namadi a yau ya rantsar da sabbin Masu Ba Shi Shawara na Musamman guda shida, a wani biki da aka gu...
03/08/2026

Gwamna Malam Umar A. Namadi a yau ya rantsar da sabbin Masu Ba Shi Shawara na Musamman guda shida, a wani biki da aka gudanar a Babban Zauren Majalisar Zartarwa da ke Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa.

Sabbin jami'an da aka rantsar sun haɗa da Muftahu Sa'adu Kiri, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Ilimi Mai Zurfi; Hajiya Salma Wakili, Mai Ba da Shawara kan Kasuwanci da Dogaro da Kai; Adamu Yusuf Garkuwa, Mai Ba da Shawara kan Harkokin Hajji; Mubarak Aliyu, Mai Ba da Shawara kan Hulɗa Tsakanin Gwamnatoci; Musbahu Rabi'u Kaugama, Mai Ba da Shawara kan Bunƙasa Zuba Jari; da Bala Sule Kila, Mai Ba da Shawara kan Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu (NGOs).

Ana sa ran sabbin masu ba da shawarar za su ƙara ƙarfafa ayyukan gwamnati tare da ba da gudummawa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Malam Umar Namadi na bunƙasa Jihar Jigawa.

02/08/2026

Ziyarar Ƙungiyar Save the Children, Nigeria zuwa gidan gwamnatin jihar Jigawa.

29/07/2026

A makon da ya wuce, Gwamna Malam Umar Namadi ya kai ziyarar duba ayyuka a cikin babban birnin jiha, Dutse.

Address

Government House
Dutse
720261

Opening Hours

Monday 08:00 - 16:00
Tuesday 08:00 - 16:00
Wednesday 08:00 - 16:00
Thursday 08:00 - 16:00
Friday 08:00 - 16:00

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share