Birnin Kebbi Youth - Initiative & Cooperative

Birnin Kebbi Youth - Initiative & Cooperative Empowering the next generation in Birnin kebbi through leadership skills development and cooperative

A heart that gives is a heart that inspires. Wishing Kaura continued strength and wisdom.Kaura 2x Insha Allah ✌️💯
30/07/2026

A heart that gives is a heart that inspires. Wishing Kaura continued strength and wisdom.

Kaura 2x Insha Allah ✌️💯

04/07/2026

Bismillahir Rahmanir Rahim

“Idan aka gina matashi da ilimi, an gina al’umma. Idan aka bar shi babu ilimi, an bar makomar gobe cikin haɗari.”

Mu a BIRNIN KEBBI YOUTH SUPPORTERS DEVELOPMENT INITIATIVE AND COOPERATIVE ASSOCIATION mun ɗauki wannan mataki ne domin samar da Project na Littattafai wanda zai zama gudunmawa wajen bunƙasa ilimi, ƙarfafa matasa, da raya al’ummar Jihar Kebbi.

Wannan ba aikin mutum ɗaya ba ne, aiki ne na ci gaban al’umma baki ɗaya. Saboda haka muna roƙon dukkan masu ruwa da tsaki, ’yan siyasa, ’yan kasuwa, masu hannu da shuni, da duk masu kishin ci gaban ilimi da matasa, da su mara mana baya domin ganin wannan buri ya zama gaskiya.

Muna kuma miƙa wannan kira cikin girmamawa ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu, da kuma Mai Girma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Yakubu Ahmad (Mai Bindiga), da sauran shugabannin gwamnati. Muna fatan za ku dubi wannan aiki na alheri, ku tallafa masa domin amfanin matasa, ɗalibai, da al’ummar Jihar Kebbi gaba ɗaya.

Tarihi yana tuna waɗanda s**a gina mutane, ba waɗanda s**a tara dukiya kaɗai ba. Taimakon da za a bayar yau zai zama haske ga dubban matasa gobe, kuma zai kasance sadaka mai ɗorewa idan Allah Ya so.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka wa duk wanda ya tallafa da alheri, Ya ƙara wa shugabanninmu hikima, lafiya, da ikon ci gaba da yi wa al’umma hidima.

A taimaka a yaɗa wannan saƙo. Wataƙila wanda zai ga wannan bidiyo shi ne zai zama sanadin cikar wannan babban buri.

🤝 BIRNIN KEBBI YOUTH SUPPORTERS DEVELOPMENT INITIATIVE AND COOPERATIVE ASSOCIATION





Address

Birnin Kebbi
Birnin-Kebbi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Birnin Kebbi Youth - Initiative & Cooperative posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share