03/03/2026
DA DUMI-DUMI | Ƙungiyar Izala ta ƙasa mai babbar Hedikwata a garin Jos ta dakatar da Alƙali Abubakar Salihu Zaria daga Tafsirin Azumin Ramadana na bana.
Ƙungiyar Izala mai babbar Hedikwata a garin Jos ta sanar da dakatar da Sheikh Alƙali Abubakar Salihu Zaria daga Tafsirin Azumin Ramadana na wannnan shekara, biyo bayan wasu wa'azozi da Lakcoci da ya gabatar a wurare daban-daban a Damaturun jihar Yobe wanda ƙungiyar ta ce sun saɓa da manhajin Ahlis-sunnah.
Idan ba ku manta ba, tun a farkon Ramadana ne aka hango wasu faya-fayan bidiyon malamin su na yawo a kafafen sada zumunta na zamani — inda ya riƙa ts!nuwa ga shugabanni, gwamnono da jami'an tsaro saboda matsalar tsaro da ya ce ta addabi yankin Arewacin Najeriya.
A ranar 12 ga watan Ramadan ne kuma majalisar malamai ta ƙasa a ƙungiyar Izala, ƙaraƙashin jagorancin, Sheikh Sani Yahaya Jingre, ta ce Alƙali Abubakar ya dawo gida daga garin Damaturun jihar Yobe, inda ta sanar da dakatar da shi daga cigaba da yin Tafsirin watan Ramadana na bana.