04/09/2026
A YAU CITY BOY MOVEMENT RESHEN JAHAR KEBBI TA TARBI GRAND PATRON DINTA.
A yau ne City Boy Movement reshen jahar kebbi ta tarbi Patron dinta dan gwaman jahar kebbi Hon. Anas Nasir Idris , Magayakim Zogirma.
Cikin tawagar akwai darakta na City Boy Movement reshen jahar kebbi Hon. Munir Umar tare da Shugabar mata ta City Boy Movement reshen jahar kebbi Hon. Aysha Ibrahim Mgwt ,
An tarbi babban bakonne tun daga filin jirgi na Ahmadu Bello har zuwa Ofishin City Boy Movement da yake anan cikin jaha, inda aka gudanar jawabai wanda yake kara nuna amfanin wan nan tafiya da kuma kara kira dan sake zaben Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tare da maigirma gwamna Dr Nasir Idris Kauran Gwandu.
An kuma gudanar da wasanni na gargajiya da al'adu domin kara nuna inganci Al'adda a wan nan jaha tamu mai albarka.
Hon. Aysha Magawata tayi jawabi inda take nuna farin cikinta da godiya na yadda mata s**a fito domin tarbon babban bako na musamman a wan nan tafiyar ta City Boy Movement.
City Boy Movement Women Wing Kebbi State.