30/10/2025
30TH OCTOBER, 2025.
*ANBA SHUGABA ƘARAMAR HUKUMA'R BIRNIN GWARI GRAND PATRON*
kungiyar cigaban RANDAGI, wato *Randagi Development Association (RADA)* yau Alhamis ta tabbatar ma shugabancin ƙaramar hukuma takardar zama Grand Patron, wand Hon. Salisu Isa ke jagorantar ƙarama'r hukumar a yanzu a yanzu.
Shugabancin kungiyar sun tattauna da shugaba'n na ƙaramar hukumar, Hon. Salisu Isah na tsawon awa 2, inda s**a masa cikakken jawabi akan kungiyar haɗi da manufofin su,inda s**a fito, inda suke da kuma inda sukeso suje.
Hon. Salisu Isah yayi godiya ya kuma ja hankalinsu akan abubuwa da s**a shafi rayuwa da kuma shugabanci, ya kuma basu shawarwari inda yake ganin ya kamata a gyara best on experience da yake da shi na shugabanci, haka zalika shugaban ya amshi wannan matsayi da aka bashi daga wannan ƙungiya ya kuma tabbatar masu da zai taimaka aduk sanda buƙatar hakan ta taso.
Shugabcin kungiyar na *RADA* ya naimi taimakon kula da wata yarinya mara lafiya da take cikin wani hali, Inda nan take Hon. Salisu Isah yayi alƙawarin taimakawa dan ganin an sama mata lafiya.