Commrd Kiran ruwa

Commrd Kiran ruwa political opponents

27/02/2026
27/02/2026

“Bincikenmu Bai Gano Shaidar Satar Kuɗi Daga El-Rufai Ba; K**a Shi Na Da Alaƙa da Siyasa” — Majiyar ICPC

Wani babban jami’i a Independent Corrupt Practices Commission (ICPC) ya bayyana a yammacin ranar Lahadi cewa binciken da hukumar ta gudanar bai gano wata shaida da ke nuna cewa Nasir Ahmad El-Rufai ya yi almundahana da kuɗaɗen jama’a ba.

Jami’in, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin magana da kafafen yaɗa labarai, ya kuma yi zargin cewa k**a tsohon gwamnan na da alaƙa da siyasa.

18/02/2026

TABDIJAN: Tinubu zai zama shugaba mafi muni idan aka bari ya sake dawowa mulki a 2027 -inji Hakeem Baba-Ahmed

Daga Ayau News

Tsohon Mai Bai Wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu Shawara kan Harkokin Siyasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, ya ce Shugaba Tinubu zai zama “mafi muni” idan ya sake komawa kan mulki a 2027.

Baba-Ahmed a hirarsa da tashar Channels Television, ya ce tun bayan barinsa mukamin mai ba shugaban shawara, bai ga wani gagarumin ci gaba ba, sai ma kara tabarbarewar al’amura. A cewarsa, matsalar tsaro ta karu, talauci da wahala sun yi tsanani, musamman a Arewacin Najeriya.

Har ila yau, ya zargi shugaban da tara ‘yan siyasa yan amshin shata a kusa da shi wadanda yake fatan za su taimaka masa wajen samun wa’adi na biyu, yana mai cewa wannan ba tsari ne mai kyau ba.

Baba-Ahmed ya kammala da cewa, yana fargabar idan Tinubu ya sake dawowa kan mulki a 2027, zai zama shugaban kasa mafi muni.

Kun yarda da hasahen Dr. Hakeem ?

LIKE // SHARE & FOLLOW Ayau News

Allah yayimana maganiniku
18/02/2026

Allah yayimana maganiniku

Rikici ya barke a majalisar wakilai kan kudirin gyaran dokar zaɓe

Wasu mambobin Majalisar Wakilai sun fice daga zauren majalisar domin nuna rashin amincewarsu da yunƙurin soke amincewar da aka bai wa kudirin gyaran Dokar Zaɓe.

Rikicin ya ɓarke ne bayan Shugaban Kwamitin Dokoki da Harkokin Kasuwanci na Majalisar, Francis Waive, ya gabatar da ƙuduri na neman a janye matsayar da majalisar ta ɗauka a kan kudirin da ta amince da shi a ranar 23 ga Disamba, 2025.

Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya sanya ƙudurin a ƙuri’ar murya. Duk da cewa muryar masu adawa ta fi ƙarfi, ya yanke hukuncin cewa masu goyon baya ne s**a yi nasara, matakin da ya tayar da kura a zauren.

Daga nan sai ya kira zaman sirri domin lalubo mafita, amma hakan bai kawo karshen takaddamar ba, yayin da zaman ya koma cikin hayaniya.

Takaddamar ta fi karkata ne kan Sashe na 60(3) na kudirin, wanda ya tanadi wajabcin tura sak**akon zaɓe ta hanyar lantarki.

’Yan majalisar da s**a nuna adawa sun miƙe tsaye tare da hana Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, ci gaba da jagorantar zaman, lamarin da ya sa zaman ya tsaya cak na ɗan lokaci.

Dan takaran da ya ciri tuta be taba Aikin Gwamnati ba .Dan kasuwane shiyasa mutane suke kira yafito takaran GWAMNAN JIHA...
08/02/2026

Dan takaran da ya ciri tuta be taba Aikin Gwamnati ba .

Dan kasuwane shiyasa mutane suke kira yafito takaran GWAMNAN JIHAR KADUNA

Alhaji Shuaibu Idiris (MIQATI) Allah yasa ya Amsa kiran da Al'ummar jihar kaduna sukeyimas.

08/02/2026
04/02/2026

Iyalan Hausawa 16 da aka kashe a Edo suna cikin kunci har yanzu, suna korafi kan rashin taimako daga gwamnatin, yayin da aka shirya zanga-zanga a Abuja.

29/01/2026

Sanata Ali Ndume ya yi ikirarin cewa mutanen da ke kewaye da Bola Tinubu ba su san siyasa ba, kuma ba su fada masa halin da talakawa ke ciki - Duba a sashen sharhi.

Hoto: Muhammad Ali Ndume/Facebook, /X

Address

Birnin Gwari

Telephone

+2349150913066

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Commrd Kiran ruwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Commrd Kiran ruwa:

Share